An rufe makarantu biyu a jihar Binuwai saboda tilastawa iyaye sayen littafan karatu
Hukumar Tabbatar da Ingancin Ilimi da Shirya Jarabawa ta Jihar Binuwai a Najeriya, ta rufe makarantu biyu, wato Orenda Schools da Opal Schools, bisa zargin cin zarafin ɗalibai da kuma karya manufofin gwamnati kan amfani da litattafan karatu.
Matakin ya biyo bayan wani rahoto da ke cewa mamallakin makarantun ya kai hari ga jami’an hukumar yayin da suke gudanar da aikinsu.
Sakataren zartarwa na Hukumar, Dr. Terna Francis, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a, yayin da yake bayanin dalilan da ya sa aka rufe makarantun.
Ya zargi mamallakiyar makarantun, Onyinye Okoye, tare da wasu ma’aikatan makarantar da cin mutuncin tawagarsa ta baki da kuma lalata wata motar hukuma bayan an miƙa musu umarnin kotu da ya ba da damar rufe harabar makarantun.
Dakta Francis ya ce matakin ya biyo bayan korafe-korafen iyaye kan makarantun suna tilasta musu sayen sabbin litattafan karatu kai tsaye daga makarantar.
Ya bayyana cewa wannan ya saɓa wa manufar gwamnatin Jihar Binuwai, wadda ta amince ɗalibai su ci gaba da amfani da tsofaffin litattafansu da kuma ba iyaye damar sayen littattafai daga shagunan sayar da littattafai na waje idan sun ga dama.
Hukumar ta ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, yayin da take jaddada aniyarta ta tabbatar da cewa dukkan makarantu a jihar suna bin dokoki da manufofin ilimi da gwamnati ta gindaya.