Sarkin Musulmi ya ayyana Talata 16 ga Yuni a matsayin 1 ga watan Muharram

Asalin hoton, Getty Images
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ayyana ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2026, a matsayin 1 ga watan Muharram 1448, sabuwar shekarar Musulunci.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Majalisar Masarautar Sokoto.
Sanarwar, wadda Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin harkokin addini na majalisar masarautar ya fitar ta bayyana cewa wannan hukunci ya biyo bayan ganin jinjirin watan Muharram da kuma tabbatar da shi bisa ka’idojin addinin Musulunci.
Watan Muharram shi ne farkon sabuwar kalandar Musulunci, wanda ke nuna fara sabuwar shekarar Musulunci.
Haka kuma yana cikin watanni masu tsarki a Musulunci, kuma yana da muhimmanci wajen tunatar da al’ummar Musulmi game da hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina.
Sarkin Musulmi ya yi kira ga Musulmi a fadin Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, hadin kai da cigaban kasa, tare da karfafa imani da ayyukan alheri a sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH.
















