Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 16/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 16/11/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • INEC
  • Atiku
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Sama da mutum 5,500 sun mutu tun bayan ɓarkewar cutar Ebola a Kongo

    Ebola

    Hukumomin lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar Ebola a asibitocin killacewa da jinya ya fi waɗanda suka mutu a gidajensu cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

    Ƙididdigar da ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta fitar, wadda ta kai zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba, ta nuna cewa mutum 22 sun mutu a cibiyoyin jinya, yayin da mutum 14 suka mutu a gidajensu.

    Masana harkokin lafiyar jama'a sun ce wannan na iya nuna cewa mutane da dama na kai marasa lafiya cibiyoyin killacewa da jinya. Sai dai wasu daga cikinsu na zuwa ne a cikin mawuyacin hali, ta yadda ba sa iya amfana sosai da jinyar da ake ba su.

    Jinyar marasa lafiya a cibiyoyin musamman na kuma rage haɗarin yaɗuwar cutar ga 'yan uwansu ta hanyar taɓa su kai tsaye.

    Ma'aikatar ta tabbatar da samun sabbin mutane 60 da suka kamu da nau'in cutar Ebola mai suna Bundibugyo, galibinsu a lardunan Ituri da North Kivu da ke gabashin ƙasar.

    Tun bayan sanar da barkewar cutar a ranar 15 ga watan Mayu, sama da mutum 11,300 ne suka kamu da ita, yayin da fiye da 5,500 suka mutu. Sama da mutum 3,000 kuma sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

    Jami'an lafiya sun ce gano mutanen da suka yi mu'amala da waɗanda suka kamu da cutar na daga cikin manyan ƙalubalen da ke kawo cikas ga ƙoƙarin shawo kan barkewar cutar.

    A halin yanzu, ana ƙoƙarin gano sama da mutum 25,000 da aka tabbatar sun yi mu'amala da masu cutar Ebola. Sai dai zuwa ranar 14 ga Nuwamba, an samu nasarar kai wa kusan kashi 83 cikin 100 daga cikinsu.

  2. Akwai yiwuwar in gana da Kim Jong-un a China – Trump

    Trump

    Donald Trump ya ce akwai yiwuwar ya gana da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, yayin ziyarar da zai kai China.

    Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, lokacin da yake barin Fadar White House domin tafiya Philippines da China.

    Ya ce akwai yiwuwar ganawar ta gudana a China, amma hakan zai dogara ne da shugaban China, Xi Jinping.

    Trump ya ce: "Za mu gana da Shugaba Putin, kuma akwai yiwuwar mu gana da Kim Jong-un. Hakan zai yi kyau, kuma muna da isasshen lokaci don yin abubuwa da dama."

    A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, Trump ya taɓa ganawa da shugaban Koriya ta Arewa a lokacin mulkinsa na farko.

    A watannin baya-bayan nan ma ya yi ta magana kan yiwuwar sake ganawa da shi, amma har yanzu ba a samu damar hakan ba.

  3. India ta yi odar sabbin jiragen yaƙi kusan 2,200

    Jiragen yaki

    Shugaban rundunar sojin saman India, Air Chief Marshal Ashutosh Dikshit, ya ce ana sa ran fara shigar da jiragen yaƙin LCA Mk-1A da aka ƙera a cikin gida cikin rundunar sojin saman ƙasar a shekarar kuɗi ta 2026 zuwa 2027.

    A cewar jaridar Hindustan Times, ana kuma sa ran kafa rundunar sojin sama ta musamman da za ta yi amfani da waɗannan jiragen.

    Waɗannan jirage za su maye gurbin tsofaffin jiragen yaƙin MiG-21 da aka dakatar da amfani da su.

    Indiya ta bayar da odar jirage 180 daga kamfanin Hindustan Aeronautics Limited, a kwangilar da jimillar kuɗinta ta kai dala biliyan 11.72.

    Bayan samun tsaiko sau da dama, yanzu jiragen sun kusa shiga aikin rundunar sojin saman ƙasar. Su ne jiragen yaƙi na farko da za su shiga aikin rundunar tun bayan fara wa Ashutosh Dikshit jagorancinta.

    Kwamandan ya ce ƙirƙira, kera da gwada jirgin yaƙi a cikin gida aiki ne mai matuƙar wahala, kuma ƙasashe kaɗan ne a duniya suka yi nasarar cim ma hakan.

  4. Imran Khan ya nemi kotun ƙolin Pakistan ta ba shi damar neman lafiya

    Tsohon firaministan Pakistan da ke tsare, Imran Khan, ya roƙi Kotun Koli ta ƙasar ta ba shi agajin gaggawa na lafiya.

    Khan, wanda ya kwashe fiye da shekara uku a gidan yari bisa zargin cin hanci da rashawa, ya ce likitoci sun gaya masa cewa yana cikin haɗarin kamuwa da zubar jini a ƙwaƙwalwa da kuma bugun zuciya.

    A cikin wata wasiƙa da ya aike, ya ce ba a aiwatar da umarnin kotu da suka ba shi damar karɓar baƙuncin iyalansa da kuma samun kulawa a wani asibiti mai zaman kansa ba.

    Sai dai wani minista a gwamnatin Pakistan ya ce tsohon firaministan ya samu an duba lafiyarsa daga likitoci.

    Imran Khan ya ci gaba da cewa shari'o'in cin hanci da rashawar da ake masa suna da alaƙa da siyasa, yana mai zargin cewa an shirya su ne domin hana shi ci gaba da taka rawa a harkokin siyasar ƙasar.

    Khan, wanda ya jagoranci Pakistan daga shekarar 2018 zuwa 2022, ya sha musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yana mai cewa ana amfani da su ne a matsayin makamin siyasa a kansa.

  5. An kama mutum 8 kan zargin arangamar APC da NDC a Kano

    Abba da Gwarzo

    Rundunar ƴansandan jihar Kano ta tabbatar da kama mutum takwas kan zargin hannu a arangamar da ta auku tsaknain magoya bayan jam'iyyun APC da NDC a jihar.

    Cikin wata sanarwa da da kakakin rundunar ƴansanda na jihar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya ce an ɓarkewar rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da NDC a cikin garin Bichi ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamban da muke ciki.

    Sanarwar ta ce rikicin ya haddasa lalata wasu motoci da allunan tallan ƴantakara da kuma jikkata mutane.

    Rundunar ƴansandan jihar ta ce bayan da suka samu labarin arangamar ta tura jami'nta domin kwantar da tarzomar, inda kuma suka samu nasarar ƙwato makamai daban-daban.

    Rundunar ta ce motoci 13 ne aka lalata yayin rikicin, yayin da mutum biyar da suka samu raunuka aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

    Sanarwar ta kuma ce an tura waɗanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID), Bompai, domin ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

    Rundunar ta kuma yi kira ga shugabannin siyasa, magoya bayan jam'iyyu da sauran jama'a su kiyaye doka da oda, su guji tashin hankali, tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da ke tayar da zargi ga ofishin 'yan sanda mafi kusa.

  6. Matakai 5 da Tinubu zai ƙarshen rashin tsaro a shekara biyar

    Tinubu

    Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da ɗaukar ƙarin sojoji 28,000 da jami'an 'yan sanda 50,000 a wani bangare na sabon shirin da take yi na yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya.

    Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na jam'iyyar APCn, Dele Alake, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2026.

    Ya ce matakan na cikin wani shirin samar da tsaro na shekaru biyar da Shugaba Tinubu ya amince da shi, domin ƙarfafa rundunonin tsaron kasar da inganta yadda suke tunkarar matsalolin ta'addanci, da fashi da makami, da garkuwa da mutane da sauran laifuka.

  7. Jordan da Iraƙi sun haramta amfani da manhajar Telegram

    Telegram

    Kasashen Jordan da Iraq sun sanar da haramta amfani da manhajar sada zumunta ta Telegram, saboda dalilan tsaron ƙasashen.

    Jordan ta ɗauki wannan mataki ne bayan wani hari da aka kai wa wata coci a watan da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara.

    Mahukuntan Jordan sun ce mutanen uku da aka yanke wa hukuncin kisa kan harin mabiyan aƙidar tsattsauran ra'ayin addinin Islama ne.

    Kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, ciki har da ƙungiyar Islamic State (IS), sun daɗe suna amfani da Telegram wajen yaɗa bidiyoyi da sanarwarsu.

    Sai dai wanda ya kafa Telegram a baya ya ce manhajar ta yi fiye da abin da ake bukata a kanta wajen sa ido da kuma takaita wallafa abubuwan da suka saɓa ƙa'ida.

  8. An yanke wa gomman ƴan Shi'a hukuncin ɗaurin rai da rai a Bahrain

    Shi'a

    Rahotanni daga ƙasar Bahrain sun ce an yanke wa Musulmai ‘yan Shi’a sama da 60 hukuncin ɗaurin rai da rai bisa zargin aikata laifukan ta’addanci da ake alaƙanta su da Iran.

    Yawancin waɗanda aka yanke wa hukuncin malaman addini ne.

    Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Bahrain mai hedikwata a Birtaniya ta ce daga cikin waɗanda abin ya shafa har da fitaccen malamin Shi’a na ƙasar Ayatollah Isa Qassim.

    Ofishin masu gabatar da ƙara na Bahrain ya ce an samu wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma da laifin kafa da kuma gudanar da wata ƙungiyar ta’addanci da ake dangantawa da rundunar juyin juha halin Iran, sai dai bai bayyana ƙarin bayani kan lamarin ba.

    Bahrain ƙasa ce mai rinjayen Musulman Sunna a shugabanci, amma tana da yawan al’ummar Shi’a, waɗanda ke yawan ƙorafin cewa ana nuna musu wariya da kuma ware su a wasu fannoni.

  9. EFCC na shirin kamani kafin zaɓen 2027 - Amaechi

    Rt Hon Chibuike R Amaechi

    Ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya na jam’iyyar ADC a zaɓen, Rotimi Amaechi, ya zargi hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da shirin kama shi kafin babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027.

    A wata tattaunawa ta musamman da sashen Pidgin na BBC, tsohon minista kuma tsohon gwamnan jihar Ribas ya yi iƙirarin cewa manufar wannan shiri ita ce haifar da ruɗani da kuma hana jam’iyyarsu samun damar fafatawa a zaɓen.

    BBC ta nemi jin ta bakin EFCC kan zargin, amma har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto hukumar ba ta mayar da martani ba.

    Da aka matsa masa ya yi ƙarin bayani kan zargin, Amaechi ya ce baya fargaba ko shakka game da hakan ba.

    "Su zo mana, ina nan ina jiransu. Ai ba wai za su ɗauke ni su tafi da ni ba ne? Manufarsu kawai ita ce su tabbatar ba mu kayar da su ba."

    Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar ƙalubalen shari’a da ka iya hana ta shiga zaɓen na 2027.

    A ranar 5 ga Nuwamban 2026, babbar kotun tarayya da Abuja, ta soke shugabancin jam’iyyar ADC tsagin David Mark, tare da rushe dukkan matakan da kwamitin riƙon ƙwaryar jam’iyyar na ɓangarensa suka ɗauka.

    Hakan ya haɗa da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da ya tsayar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen shekarar 2027, wanda shi kuma ya ɗauki a Amechi a matsayin ɗantakar mataimaki..

  10. Ba za mu bar jami'an IAEA sun ziyarci cibiyoyin nukiliyarmu ba - Iran

    Isfahan

    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin shari'a, Kazem Gharibabadi, ya ce manufar da ke bayan buƙatar da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta yi na ziyarar wuraren nukiliyarta da suka lalace ita ce auna “tasirin ɓarnar da Amurka ta yi musu”.

    A wata hira da ya yi da wani shirin tattaunawa na talabijin a Iran, jami'in ya ce har sai an cika sharuɗɗa bakwai da ƙasarsa ta gindaya tare da kawo ƙarshen yaƙi baki ɗaya.

    "Ba za mu ba wa hukumar damar shiga cibiyoyin nukiliya ba an sai an cika waɗannan sharuɗa."

    A cewarsa, "Iran mamba ce a yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya ta NPT, amma hukumar ta yi aiki bisa manufofin siyasa kuma ba ta mutunta wajibcin ɓangarorin biyu ba... kuma matuƙar yaƙin bai ƙare ba, sannan Amurka ba ta cika nauyin da ya rataya a wuyanta ba, ba za a ba hukumar damar shiga cibiyoyin nukiliyar ba."

    Ya zuwa yanzu, Tehran ba ta bai wa masu bincike na IAEA damar komawa ko ɗaya daga cikin cibiyoyin nukiliyar Iran da hare-haren Isra'ila da Amurka suka kai wa hari ba.

    A sabon rahotonta, hukumar IAEA ta amince cewa hare-haren Amurka da Isra'ila sun haifar da “yanayi da ba a taɓa fuskanta ba”, amma ta yi kira ga Iran ta bai wa masu binciken Majalisar Dinkin Duniya damar komawa cibiyoyin nukiliyar ƙasar.

  11. 'Jiragen ruwa biyu sun tarwatse a mashigar Hormuz'

    Jiragen ruwa

    Rundunar juyin juya halin Iran, IRGC ta ce wasu jiragen dakon mai biyu sun kama da wuta a mashigar ruwa ta Hormuz bayan sun yi taka nakiyoyin da aka dasa a cikin teku.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jiragen biyu sun yi ƙoƙarin bi ta hanyar da IRGC ta haramta wa jirage bi ta mashigar.

    "Jiragen sun yi ƙoƙarin bi ta haramtacciyar hanyar kudancin mashigar ƙarƙashin jagorancin jami'an Amurka sun taka nakiyar teku, lamarin da ya haifar da wasu manyan fashe-fashe masu ƙarfi tare da kama da wuta."

    Sashen hulɗa da jama'a na IRGC ya kuma ce tankokin biyu sun fashe ne "a ɗan tazara kaɗan daga inda tankokin biyu da suka gabata suka fuskanci irin wannan haɗari."

    Rundunar ta ƙara da cewa tun daga jiya Lahadi, jimillar tankokin dakon mai guda shida ne suka kama da wuta a mashigar ruwa ta Hormuz.

  12. Netanyahu barazana ce ga dimokraɗiyyar Isra'ila - Eisenkot

    Netanyahu da Gadi

    Abokin hamayyar siyasa na Benjamin Netanyahu, Gadi Eisenkot, wanda shugaban ƙasar Isra'ila ya ɗora wa alhakin kafa sabuwar gwamnati bayan zaɓen ƙasar, ya ce halayen Benjamin Netanyahu na zama "barazana ga dimokuraɗiyyar Isra'ila".

    Mista Eisenkot ya ƙara da cewa a ra'ayinsa bai kamata Netanyahu ya ci gaba da riƙe mulki ko na ƙarin minti ɗaya ba.

    "Halayen Benjamin Netanyahu da na waɗanda ke kewaye da shi babbar barazana ce ga dimokuraɗiyyar Isra'ila. Babu wani ɓangare na ƙasar da ya tsira daga cin hanci da rashawa, karkatar da gaskiya da kuma amfani da hukumomi domin tabbatar da rayuwar siyasarsa'', in ji shi.

    Ya kuma zargi Netanyahu da daina mutunta iyakoki.

    ''Kuma babu wata jan layi da bai tsallaka ba. A kowane hali, bai kamata Netanyahu ya ci gaba da kasancewa kan mulki na ko da minti ɗaya ba."

  13. Iran ta ce ta kai hari sansanin sojin Amurka a Bahrain

    Bahrain

    Rundunar tsaron juyin juya halin Iran IRGC ta ce ta kai hari kan wani sansanin soji a Bahrain a ranar Lahadi, yayin da Saudiyya ta sanar da harbo makamai masu linzami da aka harbo daga Yemen.

    Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin hukuma suka ce birnin Sanaa ya fuskanci hare-haren sama daga Saudiyya.

    A wata sanarwa da kafafen yaɗa labaran gwamnati a Iran suka wallafa, IRGC ta ce dakarunta sun kai hari da jirage marasa matuƙa kan wani tsarin na'urar rada da Amurka ke amfani da shi a wani sansanin soji da ke Bahrain.

    Sanarwar, wadda aka wallafa a tashar hukuma ta Iran a manhajar Telegram, ta ce jirage marasa matuƙa guda shida na rundunar sararin samaniya ta IRGC ne suka kai hari kan tsarin kariyar sararin samaniya da rada na Amurka da ke sansanin jirage masu saukar ungulu na Riffa a Bahrain.

    "An rufe mashigar ruwa ta Hormuz, kuma za a mayar da martani cikin ƙarfi da tsauri ga duk wani hari daga abokin gaba na Amurka," in ji shi.

    Har ila yau, IRGC ta ce a ranar Juma'a dakarunta sun kai hari kan wani tsarin rada da Amurka ke amfani da shi wajen gano hare-hare tun kafin su kai ga kai hari, wanda ke Bahrain.

  14. Manyan jiragen yaƙin Amurka uku na shawagi a Gabas ta Tsakiya

    ..

    Wani jami'in sojan Amurka ya tabbatar wa CBS News - abokiyar hulɗar BBC a Amurka - cewa jirgin ruwan yaƙi mai ɗaukar jiragen sama na USS Theodore Roosevelt ya isa yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya haɗu da USS George H.W. Bush da kuma USS George Washington, waɗanda tuni suke gudanar da ayyuka a yankin.

    Ana sa ran kasancewar waɗannan manyan jiragen yaƙi masu ɗaukar jiragen sama guda uku a lokaci guda zai kasance na ɗan lokaci ne kawai.

    Saboda rundunonin irin waɗannan jiragen na ci gaba da yin zirga-zirga a yankin bisa tsarin sauya sheƙar aiki da ake bi akai-akai.

  15. Shahararren mai safarar ƙwaya a Mexico ya rasu

    Gallardo

    Mahukunta a Mexico sun sanar da mutuwar shahararren jagoran fataucin miyagun ƙwayoyi, Miguel Ángel Félix Gallardo, wanda ya kafa ƙungiyar Guadalajara da ta aka daina jin ɗuriyarta yanzu.

    Félix Gallardo ya mutu yana da shekaru 80 a duniya.

    Kwanaki biyu da suka gabata ne aka sauya shi daga wani gidan yari da ke jihar Jalisco zuwa wani asibiti mai zaman kansa, ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.

    Ya dai taka muhimmiyar rawa wajen assasa ƙungiyoyin fataucin miyagun ƙwayoyi a Mexico.

    Kafin shekarun 1980, ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi a Mexico sun fi mayar da hankali ne kan noman tabar wiwi da kuma shigar da ita zuwa Amurka, yayin da safarar hodar Iblis ta kasance ƙarƙashin ikon fitattun dillalan miyagun ƙwayoyi na Colombia.

    Sai dai Miguel Gallardo mutum ne mai babban buri, wanda ya hango wata sabuwar dama ta kasuwanci.

    Ya shafe shekaru da dama a gidan yari bayan da aka ɗaure shi tun a shekarar 1989.

  16. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta da muhawara domin kawo muku halin da duniya ke ciki.