Daniel Maldini ya rasa lasisin tuƙi bayan hatsarin mota, Daniel Maldini

Asalin hoton, Getty Images
An karɓe lasisin tukin mota na dan wasan tawagar Italiya, Daniel Maldini, bayan da aka same shi da adadin barasa mai yawa fiye da wanda doka ta amince a samu a jikin mutum, sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a birnin Milan da sanyin safiyar Lahadi.
Wata majiya daga ƴansandan yankin ta ce a ranar Litinin aka baza batun da kowa ya san me ake ciki.
Maldini, wanda ke taka leda a ƙungiyar Cagliari, na cikin mutane shida da suka samu ƙananan rauni, bayan motarsa kirar Porsche Carrera 4 ta yi karo da wata mota a Arewacin birnin Milan da misalin ƙarfe 5:15 na safiyar Lahadi.
An kai ɗan wasan mai shekaru 24 asibiti domin duba lafiyarsa, kafin daga bisani aka sallame shi a wannan rana.
A cewar majiyar, gwajin farko da ƴansandan yankin suka yi a wurin da hatsarin ya faru, adadin barasa da aka samu a jininsa ya kai gram 0.91 a kowace lita.
Gwaji na biyu kuma ya nuna gram 0.89 a kowace lita, yayin da dokar Italiya ta kayyade iyakar adadin barasa a jini da gram 0.5 a kowace lita.
Bayan an kai shi asibiti domin ƙarin bincike, Maldini ya kuma yi gwajin amfani da miyagun ƙwayoyi. Sai dai sakamakon gwajin ba zai fito ba sai bayan kwanaki uku zuwa huɗu, kamar yadda ƴansandan suka bayyana.
Lauyan Maldini, Danilo Buongiorno, ya ƙi yin karin bayani kan lamarin.
Kafin hatsarin, Maldini ya zura ƙwallo a raga daga bugun fenareti a wasan da Cagliari ta doke Atalanta da ci 2-1 a gasar Serie A ranar Asabar da dare.
Cagliari ta bayyana a ranar Litinin cewa an yi wa Maldini gwajin sinadarai a jikinsa, kuma dukkan sakamakon da aka samu ya kasance ba shi da wata matsala.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa ɗan wasan zai koma sansanin ƴanwasanta.
Daniel Maldini ɗa ne ga tsohon ɗan tsaron bayan tawagar Italiya da AC Milan, Paolo Maldini.
A baya ya buga wa wasu ƙungiyoyin Serie A wasa, ciki har da Lazio, Atalanta da AC Milan. Ya kuma buga wa tawagar ƙasar Italiya wasanni shida.


