Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 11 ga watan Yulin 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. KACRAN ta buƙaci Tinubu ya tabbatar da aikin ma'aikatar bunƙasa kiwo

    Ƙungiyar makiyaya Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria, KACRAN buƙaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya dage wajen ganin ma'aikatar bunƙasa harkokin kiwo ta gudanar da ayyukanta kamar yadda aka tsara a farkon ƙirƙiro ta.

    Ƙungiyar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da shugabanta na ƙasa Khalil Mohd Bello ya fitar, inda a ciki ya yaba wa jajircewar shugaban wajen nuna muhimmancin bunƙasa harkar kiwo a Najeriya ta hanyar kafa kwamitin na musamman a ƙarƙashin jagorancinsa, tare da Farfesa Attahiru Jega a matsayin mataimakin shugaban kwamitin.

    "Fiye da shekara 60 makiyayan Najeriya sun kasance suna kokawa kan watsi da su, da cin zarafi da kuma nuna musu wariya daga gwamnatocin da suka gabata. Saboda haka, kafa wannan kwamitin da samar da ma'aikatar bunƙasa kiwo abin farin ciki ne ga miliyoyin makiyaya a faɗin ƙasar," in ji shi, sannan ya ya yaba da naɗa Alhaji Idi Mukhtar Maiha a matsayin minista.

    Sai dai ya ce KACRAN, "wadda ta kasance cikin ƙungiyoyin da suka yi fafutukar kafa ma'aikatar kiwo, tana tunatar da shugaban ƙasa cewa har yanzu kwamitin na musamman da ma ma'aikatar ba su da cikakken ƙarfin gudanar da aikinsu, sakamakon ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa da kuma rashin cikakken tsarin aiki."

    Ya ƙara da cewa idan ma'aikatar ta fara cikakken aiki, za a samu abinci, za a samar da ayyuka ga matasa, sannan za a rage rikicin makiyaya da manoma a ƙasar.

  2. Hare-haren Rasha sun kashe mutum biyar, ciki har da ƴar shekara 13 a Ukraine

    Shugaban yankin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine ya ce mutum biyar sun mutu, yayin da wasu 30 suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai ta sama da Rasha ta kai yankin.

    Ƴansanda sun bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu yarinya ce mai shekara 13, wadda ke jiran abin hawa na sufuri a wata tashar mota lokacin da harin ya faru.

    A wani labarin daban, Magajin Garin Kyiv ya ce mutum 12 sun jikkata sakamakon hare-haren da Rasha ta kai cikin dare a babban birnin Ukraine.

    A nata ɓangaren, ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta kai hare-hare kan wuraren ƙerawa da adana jirage marasa matuƙa a birnin Kyiv.

    A lokaci guda kuma, rundunar sojin Ukraine ta sanar da cewa ta kai hari kan jiragen ruwa sama da 20 a cikin Tekun Azov, ciki har da tankokin ɗaukar mai mallakin Rasha.

  3. Yunwa ta yi ajalin mutum 16 a Uganda

    Gwamnatin Uganda ta fara aikin agajin gaggawa a yankin Karamoja da ke arewa maso gabashin ƙasar, bayan 16 sun mutu sakamakon yunwa da fari mai tsanani da suka addabi yankin.

    Firaministar ƙasar, Robinah Nabbanja, ta ce ofishinta zai nemi amincewar majalisar ministoci a ranar Litinin domin sayo ƙarin kayan agaji da za a kai yankunan da fari ya fi shafa.

    Manoma sun bayyana cewa sun yi asarar amfanin gona mai yawa bayan watanni da dama na ƙarancin ruwan sama ko rashin samun ruwan sama gaba ɗaya.

    Masana sun yi gargaɗin cewa matsalar ƙarancin abinci da ake yawan fuskanta a yankin na faruwa ne sakamakon sauyin yanayi, ƙarancin ruwan sama, sare itatuwa, yawan kiwo fiye da ƙarfin ƙasa, da kuma kwari da ke lalata amfanin gona.

  4. Hukumomi a Turkiyya sun buƙaci a kama mutum 36, ciki da Magajin Gari ɗan jam'iyyar adawa

    Masu gabatar da ƙara a Turkiyya sun buƙaci a kama mutum 36, ciki har da magajin garin wata gunduma a Ankara da jam'iyyar adawa ke jagoranta.

    An bayar da umarnin kamen ne a matsayin wani ɓangare na binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma bayar da kwangiloli ba bisa ƙa'ida ba.

    Ofishin masu gabatar da ƙara ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa jami'an tsaro sun riga sun kama mutum 27 daga cikin waɗanda ake nema, yayin da ake ci gaba da neman sauran.

    Hüseyin Can Güner, magajin garin gundumar Çankaya da ke Ankara kuma mamba na Jam'iyyar Republican People's Party (CHP), ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafin X cewa ya sanar da hukumomi inda yake, sannan ya ba su madadin mabuɗin gidansa domin jami'an da za su gudanar da bincike.

    Ya ƙara da cewa yana kan hanyarsa ta komawa Ankara.

    Jam'iyyar CHP ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa binciken yana da alaƙa da siyasa kuma an ƙaddamar da shi ne saboda dalilan siyasa.

  5. An kashe dakarun Basij biyu a Iran

    Dakarun juyin-juya-halin Iran sun sanar da cewa an kashe dakarun Basij biyu a garin Mashhad. Basij dai dakaru ne na sa-kai da ke ƙarƙashin dakarun juyin-juya-hali.

    Kakakin rundunar sashen Imam Reza Corps na dakarun juyi-juya-halin a birnin Mashhad ne ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar.

    Sanarwar ta bayyana cewa an harbe su ne a kusa da Dandalin Sarafrazan yayin da suke gudanar da aikinsu na sintiri domin tabbatar da tsaro.

    An kuma ce wani mai wucewa da wajen ya ji rauni a harin, amma an kai shi asibiti domin samun kulawar likitoci.

    Har yanzu dai babu tabbacin waɗanda suka ƙaddamar da harin.

    Tun da farko, Amirollah Shamqadri, mataimakin jami'in tsaro na gwamnatin lardin Khorasan Razavi, ya musanta rahotannin da ke cewa lamarin na da alaƙa da ta'addanci.

  6. Nawa ne albashin sojojin Najeriya idan aka kwatanta da sauran ƙasashen Afrika?

    Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa mai ritaya, ya yi wasu kalamai da suka haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar bayan da ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ƙara mafi ƙarancin albashin sojojin ƙasar zuwa naira 100,000 a wata..

    Janar Musa, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi ranar Laraba, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakan inganta walwalar sojoji.

    "Da can sojoji suna karɓar naira 49,000 a wata ne. Mun yi ƙoƙari sosai, yanzu suna karɓar naira 100,000," in ji shi.

  7. Mutum-mutumi da ke aikin gida

    Ina waɗanda aikace-aikacen gida ya sha musu kai?

    To za a iya cewa sauƙi ya samu domin a yanzu an fara bayar da hayar mutum-mutumin da zai iya gudanar da dukkan aikace-aikacen gida.

  8. Rasha ta kai harin makamai masu linzami kan Kyiv

    Jami’an Ukraine sun ce Rasha ta harba makamai masu linzami masu kan babban birnin ƙasar, Kyiv, da sanyin safiyar Asabar.

    Wani shaidar gani da ido ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya ji ƙarar manyan fashe-fashe da dama a birnin kafin a kai harin ta sama.

    Hukumar sojin Kyiv ta bayyana a shafinta na Telegram cewa harin ya yi sanadin lalacewar wani a yankin birnin, yayin da aka ga hayaki na tashi daga wani wuri dabam.

    Haka kuma, hukumar ta ce wani ginin ofis ya kama da wuta bayan harin, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan girman ɓarnar da harin ya haifar.

  9. Mutum ɗaya ya mutu, uku sun jikkata bayan ruftawar gini a Kano

    Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon ruftawar wani gini mai bene biyu da ake ginawa a kan titin Sultan da ke cikin birnin Kano a safiyar Juma’a.

    Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ma’aikatan ceto sun samu nasarar fitar da mutane uku daga ƙarƙashin baraguzan ginin da ransu.

    Shaidu sun ce ma’aikatan ginin sun lura da alamun cewa ginin na gab da rushewa, lamarin da ya sa da dama suka tsere domin tsira da rayukansu kafin faruwar hatsarin.

    An kai waɗanda suka jikkata, ciki har da mai gadin wurin ginin, zuwa Asibitin Kwararru na Sir Muhammadu Sanusi domin samun kulawa, yayin da hukumomi ke sa ran fara bincike domin gano musabbabin ruftawar ginin.

  10. Araghchi ya isa Oman yayin da masu shiga tsakani daga Qatar suna Iran

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya isa birnin Muscat na ƙasar Oman domin tattaunawa da jami’an gwamnatin Oman kan batutuwan tsaro da harkokin teku.

    Ana sa ran ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu za su tattauna kan yadda za a samar da hanyoyin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci ta mashigar Hormuz, bisa tanade-tanaden yarjejeniyar Islamabad.

    A lokaci guda kuma, wata tawagar masu shiga tsakani daga Qatar ta kai ziyara Iran da nufin sake farfaɗo da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka tare da rage zaman ɗarɗar da ke tsakanin ɓangarorin biyu.

    A wani labarin kuma, ma’aikatar lafiyar Iran ta ce mutum 17 sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da Amurka ta kai kan birane shida da ke kudancin ƙasar.

  11. Mojtaba Khamenei ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa

    Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa Ali Khamenei, wanda ya mutu a hare-haren Isra'ila da Amurka a ranar farko ta yaƙin.

    A wani saƙo da aka wallafa da sunansa domin gode wa waɗanda suka halarci jana'izar mahaifinsa, Mojtaba Khamenei ya ce za su ɗauki fansar jininsa da kuma na sauran waɗanda suka mutu a harin da Amurka da Isra'ila suka kai wanda ya bayyana a matsayin kisan gilla.

    Ya kuma jaddada cewa ɗaukar wannan fansa buri ne na al'ummar Iran, yana mai cewa dole ne a tabbatar an aiwatar da ita ba tare da gazawa ba.

    Tun bayan da aka ce ya maye gurbin mahaifinsa a matsayin jagoran Iran, Mojtaba Khamenei bai bayyana a bainar jama'a ba, kuma har yanzu ba a ji saƙon murya ko na bidiyo daga gare shi ba, sai dai rubuce-rubucen da ake wallafawa da sunansa.

  12. Yunwa ta kashe mutane 16 a Uganda sakamakon fari

    Gwamnatin Uganda ta ce aƙalla mutum16 sun mutu sakamakon yunwa a yankin Karamoja da ke arewa maso gabashin ƙasar, bayan dogon fari da ya lalata amfanin gona.

    Firaministar Uganda, Robinah Nabbanja, ta ce dubban iyalai sun rasa abinci bayan rashin ruwan sama tun daga watan Afrilu, lokacin da ake fara shuka amfanin gona.

    Manoma sun ce gonakin masara, dawa da waken soya sun lalace saboda ƙarancin ruwa, lamarin da ya rusa fatan samun girbi mai yawa a bana.

    Gwamnatin ta fara raba kayan agajin gaggawa, yayin da masana ke danganta matsalar da sauyin yanayi, sare itatuwa, yawan kiwo ba tare da kulawa ba da kuma ƙwarin da ke lalata amfanin gona. Sun yi kira da a ƙara zuba jari a ban ruwa da kuma iri masu jure fari.

  13. Ba mu nemi tattaunawa da Amurka ba – Iran

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce Tehran ba ta nemi wata tattaunawa da Amurka ba, sai dai ta amince da buƙatar wani mai shiga tsakani daga yankin domin tattauna sabbin abubuwan da ke faruwa.

    Baghaei ya bayyana cewa wakilin ya kai ziyara birnin Mashhad, inda Iran ta bayyana matsayinta ga ƙasar Qatar da ke taka rawa wajen shiga tsakani.

    Ya kuma zargi Amurka da karya wasu sassa na yarjejeniyar da aka cimma kwanan nan.

    A cewarsa, cikin kwanaki 21 zuwa 22 kacal bayan rattaɓa hannu kan yarjejeniyar, Amurka ta saɓa wa wasu tanade-tanadenta, ciki har da wasu abubuwan da suka faru a ranakun Laraba da Alhamis da kuma soke lasisin sayar da man fetur na Iran.

    Baghaei ya ƙara da cewa sabbin takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba wa Iran sun saɓa wa sashe na tara na yarjejeniyar, yana mai jaddada cewa Tehran na ganin waɗannan matakan a matsayin karya alƙawuran da aka ɗauka.

  14. Farashin fetur ya ƙaru a Amurka sakamakon yaƙin Iran

    Farashin man fetur a Amurka ya sake tashi bayan makonni da dama yana sauka, sakamakon ƙarin tashin hankalin da ke tsakanin Amurka da Iran da kuma hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce matsakaicin farashin galan ɗaya na fetur ya ƙaru da cent shida a wannan mako, inda ya kai dala $3.88, wanda shi ne ƙaruwa mafi girma cikin mako guda tun tsakiyar watan Mayu.

    Hare-haren da aka kai kan wasu tankokin dakon mai a mashigar Hormuz da kuma musayar hare-hare tsakanin Amurka da Iran sun taimaka wajen haɓaka farashin ɗanyen mai na Brent da kusan kashi 5.5 cikin ɗari a wannan mako.

    Rahotanni sun ce zirga-zirgar man fetur ta mashigar Hormuz har yanzu ba ta koma yadda take kafin rikicin ba.

  15. Yau wa'adin Amurka ga Iran kan mashigar Hormuz zai ƙare

    Yau ne ake sa ran wa’adin da Amurka ta bai wa Iran zuwa ƙarshen ranar yau Asabar zai ƙare, inda ta buƙaci Tehran ta ba da tabbacin cewa mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a buɗe kuma ba za a kai hare-hare kan jiragen kasuwanci ba.

    Jami’an Amurka sun ce Iran ta shaida musu a sirrance cewa wasu masu tsattsauran ra’ayi da ba sa aiki ƙarƙashin cikakken ikon gwamnati ne ke da hannu a hare-haren da aka kai kan wasu jiragen ruwa, da nufin kawo cikas ga tattaunawar da ake yi.

    A daidai lokacin da ake fargabar ƙarin tashin hankali a yankin, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya kai ziyara ƙasar Oman domin tattauna rikicin da ya shafi mashigar Hormuz.

    Haka kuma, wata tawagar masu shiga tsakani daga Qatar ta gana da jami’an Iran a Tehran, a wani yunƙuri na hana rugujewar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka da kuma rage zafafan takun-saƙar da ke ƙara ƙamari a yankin.

    Mashigar Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin jigilar man fetur a duniya, kuma duk wani rikici a yankin na iya yin tasiri ga kasuwancin duniya da kuma farashin mai.

  16. Yadda aka kuɓutar da ɗalibai da malamai 44 da aka sace a Oyo - Sojoji

    Rundunar Sojin Najeriya ta ce an kuɓutar da ɗalibai da malamai 44 da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo bayan wani samamen haɗin gwiwa da ya ɗauki fiye da wata guda, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da na leƙen asiri daban-daban.

    Mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Danjuma Jonah Danjuma, ya ce aikin ya mayar da hankali kan gano waɗanda suka shirya garkuwar da kuma lalata hanyoyin tallafi da maɓoyarsu da ke cikin dajin Old Oyo National Park.

    Ya ƙara da cewa kama wasu da ake zargi ya tarwatsa ƙungiyar, lamarin da ya kai ga sakin waɗanda aka sace ba tare da wani sharadi ba.

    Tun da farko, mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da sakin ɗaliban da malaman tare da wallafa hotunansu a shafinsa na X.

    An sace ɗalibai 39 da malamai bakwai a wani hari da aka kai ranar 15 ga Mayun 2026, kuma rundunar sojin ta ce ana kula da lafiyar waɗanda aka ceto kafin a haɗa su da iyalansu.

  17. Idan Iran ta yi yunƙurin kashe ni, za ta fuskanci hare-hare mafi muni - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Iran gargaɗi cewa za ta fuskanci hare-hare mafi muni idan ta yi yunƙurin kashe shi, yana mai cewa sojojin Amurka sun shirya tsaf domin mayar da martani cikin ƙarfi.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, Trump ya ce:

    “Makaman roka dubu ɗaya a shirye suke su afka wa Iran idan ta aiwatar da duk wata barazana ta kashe ni, nan take za a harba ƙarin dubban makamai masu linzami.”

    Trump ya kuma ce ya bayar da umarnin da suka dace, yana mai cewa sojojin Amurka sun shirya su “lalata dukkan yankunan Iran gaba ɗaya” na tsawon shekara guda.

    Wannan barazanar na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an leƙen asirin Isra’ila sun gano wani sabon shiri da ake zargin Iran na yi na kashe Trump.

    Haka kuma, an ga wasu hotuna da kalamai masu nuna adawa da Trump a yayin jana’izar Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

    Sai dai jami’an Iran sun sha musanta zarge-zargen cewa suna da wani shiri na kashe Donald Trump.

  18. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Laraba.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.