KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 18/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 18/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. ADC ta nemi kotu da hana INEC sauya shugabanninta

    David Mark

    Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) tsagin Sanata David Mark ta nemi ƙotun ɗaukaka ƙara ta hana hukumar zaɓen ƙasar INEC sauya bayanan shugabancinta da kuma bayanan ƴan takararta na shugaban ƙasa da gwamnoni, har sai an yanke hukunci kan ƙarar da ta ɗaukaka game da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke.

    Jam’iyyar ta ce ta shigar da ƙorafi mai ƙunshe da buƙatu 17 ga kotun ɗaukaka ƙarar.

    Tsagin na David Mark na ƙalubalantar hukuncin da aka yanke a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, wanda ta bayyana da kuskure.

    A hukuncin da ta yanken babbar kotun tarayyar da soke shugabancin tsagin David Mark da duka abubuwan da tsagin ya aiwatar ciki har da takatar Atiku.

    Sai dai a ƙarar da ta shigar gaban kotun ɗaukaka ƙarar, ADC tsagin David Mark ta ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron taƙaddamar shugabancin jam’iyyar.

    A wata sanarwa da daraktan sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Talata, jam’iyyar ta ce tana kuma ƙalubalantar wani hukunci da ya bai wa Bala Gombe damar yin gyara ga ƙarar da ya shigar tun farko, duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale kan hurumin kotun na sauraron shari’ar.

    Jam’iyyar ADC ta yi gargaɗin cewa idan aka bai wa INEC damar aiwatar da hukuncin ranar 5 ga Nuwamba kafin kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan batutuwan da aka gabatar, hakan na iya raunana tasirin ƙarar da ta ɗaukaka tare da jefa ƴan takararta cikin rashin tabbas.

    Saboda haka, ta buƙaci kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da cewa bayanan shugabancinta da na ƴan takararta sun ci gaba da kasancewa yadda suke a halin yanzu har sai an kammala shari’ar.

  2. Iran ta ce ta kai hari sansanin sojin Amurka a Kuwait

    Iran

    Rundunar sojin Iran ta sanar da kai hari kan sansanin sojin Amurka na Ali al-Salem da ke Kuwait.

    Cikin sanarwar da sojojin Iran suka fitar da safiyar Laraba, sun ce jiragen yaƙinta marasa matuƙa sun kai hari kan dakarun Amurka da ke sansanin Ali al-Salem da ke Kuwait.

    Sanarwar Iran ɗin na zuwa ne sa'a guda bayan rundunar sojin Kuwaiti ɗin ta sanar da kunna tsarin kariyar sararin samaniyarta domin daƙile makaman da ake harbowa.

    "Domin kare Iran, ba za mu rusuna wa wata ƙasa ko wata runduna ba. Duk da haka, martaninmu ga duk wata barazana ko hari zai kasance mai tsauri, kuma ba tare da iyakancewa da wani yanki na duniya ba," a cewar sanarwar ta Iran.

    A safiyar Laraba, baya ga Kuwait, an kuma kunna ƙararrawar gargaɗin hare-haren sama a Bahrain, yayin da rahotanni suka ce an ji fashe-fashe da dama a ƙasar.

    Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (Revolutionary Guard) ta ce tsarin radar na sojojin Amurka da ke Bahrain ne ya kasance manufar waɗannan hare-haren.

  3. Putin ya yaba da ganawar da aka shirya tsakaninsa da Trump da Xi

    shugabanni

    Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya ce yana sa ran ganawar da aka shirya yi tsakaninsa da Shugaban Amurka Donald Trump da kuma Shugaban China Xi Jinping, za ta kasance mai matukar amfani.

    Da yake jawabi a wani taron tattalin arziki na yanki da ake gudanarwa a birnin Shenzhen na ƙasar China, Mista Putin ya ce akwai matuƙar buƙatar haɗin kai a wannan lokaci da tattalin arzikin duniya ke ƙara taɓarɓarewa.

    Ganawar shugabannin za ta kasance karon farko da mutanen uku za su haɗu a wuri guda.

    Ana sa ran batutuwan da suka haɗa da yaƙin Ukraine, da rikicin Iran, da batun ƙirƙirarriyar basira ta AI da kuma makaman nukiliya za su kasance cikin abubuwan da za a tattauna.

  4. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Kamar dai jiya, Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Muna sanar da ku cewa mun buɗe sabuwar manhajar da za su iya samun labaranmu da bidiyoyin da muke wallafawa.

    Ku shiga Play Store ko Apple Store domin sauke manhajar.