Gobara ta hallaka jarirai 15 a asibiti a Pakistan
Aƙalla jarirai 15 ne suka mutu bayan wata gobara ta tashi a wani asibiti da ke birnin Islamabad na Pakistan, inda ɗaya kacal daga cikin jariran da ke sashen kula da jarirai aka samu nasarar cetowa da ransa.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun ce gobarar ta tashi ne bayan na'urar sanyaya ɗaki ta fashe a sashen kula da mata masu juna biyu na Cibiyar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Pakistan (PIMS).
Gobarar ta bazu zuwa sashen jarirai, lamarin da ya haddasa asarar rayuka masu yawa.
Jami'ai sun ce an kashe gobarar, kuma jami'an agajin gaggawa na ci gaba da aikin sanyaya wurin da kuma tantance irin ɓarnar da gobarar ta yi.
Hukumomi sun kuma fara bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.