KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 26 ga watan Agustan 2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Wace ce Dolly Parton, fitacciyar mawaƙiyar Amurka da ta rasu?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitacciyar mawaƙiya, jaruma kuma marubuciyar waƙoƙi ta Amurka, Dolly Parton, ta rasu tana da shekara 80 a duniya.

    An haifi Dolly Rebecca Parton a ranar 19 ga Janairun 1946 a jihar Tennessee ta Amurka, inda ta taso cikin iyali mai yara 12.

    Tun tana ƙarama ta fara rubuta waƙoƙi kuma ta shiga harkar kiɗa, lamarin da ya sa daga baya ta zama ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan waƙoƙin country a tarihin Amurka.

    Dolly Parton ta yi fice da waƙoƙi irin su Jolene, I Will Always Love You da kuma 9 to 5, waɗanda suka samu karɓuwa a faɗin duniya.

    Baya ga harkar waƙa, ta yi fice a fina-finai da dama, sannan ta kafa cibiyar nishaɗi ta Dollywood da kuma shirin Imagination Library, wanda ke raba littattafai kyauta ga yara domin ƙarfafa karatu.

    A tsawon aikinta, ta lashe lambobin yabo da dama ciki har da Grammy, kuma ta sayar da sama da kwafi miliyan 100 na ƙundin waƙoƙinta.

    Mutuwar Dolly Parton ta jawo alhini daga magoya bayanta da masu sha'awar kiɗa a duniya, inda ake yi mata kallon ɗaya daga cikin fitattun mata da suka canza fagen waƙoƙin country.

    Ba saboda nasarorin da ta samu a harkar nishaɗi kaɗai aka santa ba, har ma saboda ayyukan jin ƙai da tallafin da ta riƙa bayarwa ga yara da al'ummomi masu buƙata.

  2. Iƙirarin Amurka na cire nakiyoyi a mashigar Hormuz farfaganda ce - Iran

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya yi watsi da ikirarin shugaban Amurka Donald Trump cewa an cire dukkan nakiyoyin da ke mashigar Hormuz, yana mai cewa wannan "ƙarya ce ta farfaganda".

    Ya ce idan har Amurka ta cire nakiyoyin kamar yadda take ikirari, me ya sa har yanzu babu jiragen ruwa da ke iya wucewa ta mashigar.

    Gharibabadi ya kuma yi barazanar cewa Iran za ta kai wa jiragen Amurka masu aikin gano da cire nakiyoyi za su zama hari idan suka shiga yankin.

    Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da Iran da Oman ke ci gaba da tattaunawa kan samar da wata hanya ta musamman domin zirga-zirgar jiragen kasuwanci a mashigar Hormuz.

    Jami'in na Iran ya ce ko da an kammala yarjejeniyar da ake tattaunawa da Oman, ba za a sake buɗe mashigar nan take ba.

    Ya bayyana cewa sabuwar hanyar za ta kasance ta wucin-gadi, inda jiragen ruwa za su riƙa shiga Tekun Fasha ta ruwan Iran sannan su fita ta ruwan Oman.

    Ya kuma ce idan cikin kwanaki 30 zuwa 60 ba a cimma matsaya kan wata yarjejeniya ta dindindin da za ta biya buƙatun Iran ba, to mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe.

  3. Shugabannin ƙasashen Iran da Rasha za su gana mako mai zuwa

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jakadan Iran a Rasha, Kazem Jalali, ya ce shugaban Iran Masoud Pezzekiyan da takwaransa na Rasha Vladimir Putin za su gana a mako mai zuwa a gefen taron ƙungiyar haɗin gwiwar Shanghai (SCO) da za a gudanar a Bishkek, babban birnin Kyrgyzstan.

    Jalali ya bayyana cewa wannan ita ce ganawa ta shida tsakanin shugabannin biyu tun bayan da gwamnatin Masoud Pezzekiyan ta hau mulki.

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za tan kasance da ku a wannan lokaci.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.