Ghana ta koka da nuna ƙyamar mutanensu da ake a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Ghana ta ce mahukuntan Afirka ta Kudu sun fara gudanar da bincike kan wasu hare-haren nuna kyama da ake kai wa ƴan ƙasar mazauna Afirka ta Kudu.
Hotunan bidiyo da ke nuna ana cin zarafin 'yan Ghana a Afirka ta Kudu sun karaɗe shafukan sada zumunta na Intanet a ƴan kwanakin nan.
Hare-haren ƙyamar baƙi wani lamari ne mai sarƙaƙiya, wanda matsalolin tattalin arziƙi da labaran ƙarya da rashin fahimtar tarihi ke haifarwa.
Ana dai samun ƙaruwar zanga-zanga da tashin hankali kan nuna ƙyama ga waɗanda ba ƴan asalin Afrika ta Kudu ba musamman a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ƙasar.




