Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya.
A cikin saƙon ta'aziyyarsa, Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Bamanga Tukur, wanda ke riƙe da sarautar Tafidan Adamawa, a matsayin wani giɓi da aka rasa a tarihin siyasa da tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban ya ce marigayin ya kasance fitaccen jagora wanda ya taka rawar gani a fannoni da dama da suka haɗa da aikin gwamnati, shugabanci, harkokin kasuwanci, siyasa da kuma bunƙasa kasuwancin Afirka.
An haifi Alhaji Bamanga Tukur ne a ranar 15 ga Satumba, 1935. Ya yi fice a matakin ƙasa lokacin da ya kasance Babban Manajan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) daga shekarar 1975 zuwa 1982, inda ya taimaka wajen zamanantar da ayyukan tashoshin jiragen ruwa da inganta harkokin sufurin teku a ƙasar.
Shugaba Tinubu ya tuno da yadda Bamanga Tukur ya shiga siyasa a Jamhuriya ta Biyu, abin da ya kai ga zaɓensa a matsayin Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola a shekarar 1983. Jihar Gongola ta wancan lokaci ita ce ta rabu zuwa jihohin Adamawa da Taraba na yanzu.
Bayan kammala aikinsa a siyasa, marigayin ya yi fice a harkokin kasuwanci inda ya jagoranci kamfanonin BHI Holdings da DADDO Group of Companies, waɗanda ke da hannun jari a fannoni kamar masana'antu, noma, sufuri da kasuwanci.
Haka kuma ya taɓa zama Ministan Masana'antu na Tarayya a gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha daga shekarar 1993 zuwa 1995.
A nahiyar Afirka kuwa, Bamanga Tukur ya kasance babban mai rajin farfaɗo da tattalin arzikin Afirka. Ya yi aiki a matsayin Shugaban African Business Roundtable da kuma shugaban NEPAD Business Group, inda ya riƙa fafutukar bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka, ƙarfafa zaman kansa a harkokin kasuwanci da ci gaba mai ɗorewa.
Marigayin ya kuma kasance Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa daga Maris 2012 zuwa Janairu 2014. Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da ya bayar wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya ta hanyar tabbatar da ladabtarwa a cikin jam'iyya da kuma samar da haɗin kai.
A cewar Shugaba Tinubu: "Alhaji Bamanga Tukur mutum ne mai ilimi, karamci da mutunci. Ya kasance mai kishin hidima ga al'umma da kuma mai cikakken yarda da ƙarfin da Najeriya ke da shi na samun ci gaba. Ƙasar nan za ta yi matuƙar kewar hikimarsa da shawarwarinsa na uba," kamar yadda Bayo Onanuga mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai.
Shugaban Ƙasar ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan Tukur, masarautar Adamawa, gwamnatin da al'ummar Jihar Adamawa, da kuma dukkan al'ummar siyasa da kasuwanci a Najeriya da faɗin Afirka.