KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 15 ga watan Yunin 2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • XXX
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Usman MINJIBIR

  1. Za a gurfanar da 'ƴan Boko Haram' 400 a gaban kotu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla ƴan Boko Haram 400 ne za a gurfanar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a yau kan zargin aikata laifukan ta’addanci, a ɗaya daga cikin manyan shari’o’in ta'addanci da aka taɓa yi a Najeriya.

    Shari’ar na nuni da wani muhimmin mataki a ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa ɗaukar alhaki da kuma magance matsalar tsaro da ƙasar ke fama da ita tsawon lokaci.

    Waɗanda ake tuhuma na fuskantar zarge-zarge daban-daban da suka haɗa da kai hare-hare da tallafawa ayyukan ƙugiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ta'addaci.

    Wannan na zuwa ne bayan wata babbar shari’a a watan Afrilun 2026, inda aka gurfanar da sama da mutane 500 kan zargin aikata laifukan ta'addanci kuma an samu kusan 400 da laifi.

    Mahukunta sun ce wannan mataki na da nufin kammala sauran shari’o’i da kuma gurfanar da ƙarin waɗanda ake zargi domin a hukunta su.

    Najeriya na ci gaba da fama da rikicin ta’addanci na tsawon shekaru 16, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da miliyan biyu da muhallansu, yayin da matsalar garkuwa da mutane ke ci gaba da ƙaruwa a sassa daban-daban na ƙasar.

  2. Farashin mai ya sauka bayan cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin hannayen jari ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Asiya, yayin da farashin mai ya ragu, bayan sanar da cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran.

    Farashin ɗanyen man fetur na Brent ya fara sauka da kusan kashi huɗu cikin ɗari, inda ya ragu zuwa ƙasa da dala 84 kan kowace ganga.

    Farashin man ya sakko ƙasa duk da rashin ƙarin bayani kan abun da ke ƙunshe cikin yarjejeniyar, abun da ke nuna yadda 'yan kasuwa suka yi imanin cewa komi zai daidaita da zarar an sake buɗe mashigar Hormuz.

    Kafin rikicin, kusan kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya na bi ta wannan muhimmiyar hanya da ke yankin Tekun Fasha.

    A lokacin da faɗan ya ɓarke, Iran ta kusan hana zirga-zirgar jiragen ruwa ta wannan mashiga gaba ɗaya.

  3. Rikici ya ɓarke tsakanin ‘yansanda da masu zanga-zanga kafin taron G7 a Turai

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu rikici tsakanin ‘yansanda da masu zanga-zanga a dab da fara taron ƙasashen G7, inda suka gwabza a wajen hedkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Geneva, ƙasar Switzerland.

    Rikicin ya faru ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen taron a birnin Évian-les-Bains na Faransa, wanda ke kusa da Geneva, inda biranen biyu ke gefen tafkin Geneva amma a ƙasashe daban-daban.

    An gudanar da zanga-zangar a ranar Lahadi ne karkashin jagorancin wata ƙungiya da ake kira “No-G7”, wadda ta haɗa ƙungiyoyi sama da 60, ciki har da masu fafutukar kare hakkin Falasdinawa da masu rajin kare haƙƙin mata da kuma masu kare muhalli

    Masu zanga-zangar sun jefa kwalabe da duwatsu da kuma gurneti masu ƙara ga jami’an tsaron, yayin da ‘yansandan suka mayar da martani ta hanyar amfani da hayaƙi mai sa hawaye da kuma ruwan zafi wajen tarwatsa su.

    Rahotanni sun ce an kai hari kan wasu gine-gine a yayin rikicin, abin da ya ƙara nuna tashin hankali a yankin.

    Ana sa ran shugabannin ƙasashen G7 da dama za su sauka a filin jirgin saman Geneva kafin su wuce Évian ta cikin tafkin Geneva domin halartar taron.

    Jami’an tsaro na yin shiri ne don tinkarar zanga-zanga makamanciyar wadda aka fuskanta shekaru 23 da suka wuce.

    Haka kuma, babban asibitin birnin ya fara shiri na musamman domin karɓar mutane da ka iya jikkata, inda aka kafa tantuna na wucin gadi domin jinyar gaggawa.

  4. Birtaniya, Faransa, Jamus da Italiya sun yi maraba da yarjejeniyar Iran da Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Birtaniya, da Faransa, da Jamus da Italiya sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa inda suka yi maraba da yarjejeniyar, suna masu cewa sake buɗe mashigar Hormuz abu ne mai matuƙar muhimmanci.

    Sanarwar ta kuma jaddada cewa bai kamata Iran ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba.

    Kasashen huɗu na Turai sun ce a shirye suke su ɗage takunkuman da suka sanya wa Iran din idan har ta ɗauki matakai bayyanannu da za su ba da damar bibiyar shirinta na makamashin nukiliya don tabbatar da cewa ba ta sauka daga layi ba.

  5. Iran da Amurka za su rattaɓa hannu kan yarjejeniya ranar Juma'a a Switzerland

    .....

    Asalin hoton, BBC collage/getty/IRNA

    Iran da Amurka sun sanar da cewa sun cimma wata yarjejeniyar fahimtar juna domin kawo ƙarshen yaƙin da ke tsakaninsu, bayan watanni na rikici da tattaunawa.

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a wani saƙo cewa yarjejeniya da Iran “ta kammala gaba ɗaya,” yana mai taya kowa murna kan wannan ci gaba.

    Shi ma firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif, ya sanar cewa an cimma wannan yarjejeniya, tare da ƙara da cewa za a yi bikin rattaba hannu a hukumance ranar Juma’a, 19 ga watan Yuni, a ƙasar Switzerland.

    Haka zalika, Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ta tabbatar da cewa an cimma wannan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin kawo ƙarshen yaƙin da aka ɗauki watanni ana yi inda ta ce za a dakatar da dukkan ayyukan soja nan take a dukkan wurare.

    Wannan yarjejeniya na daga cikin manyan matakai da ake ganin za su iya rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya tare da buɗe hanya ga zaman lafiya mai ɗorewa.

  6. Assalamu alaikum

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.