Rufewa
Masu bi shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo Ĉarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a faÉin duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin kawo muku sabbin labarai.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/06/2026.
Daga Aisha Babangida
Masu bi shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo Ĉarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a faÉin duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin kawo muku sabbin labarai.

Asalin hoton, Getty Images
Za a ci gaba da jigilar jiragen sama daga Tehran zuwa Dubai daga gobe Litinin, makonni bayan Iran ta kai hari cikin HaÉaÉÉiyar Daular Larabawa, yayin yaĈin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban filin jirgin sama na Imam Khomeini ya ce an kammala duk wasu shirye-shirye domin ci gaba da jigila tsakanin Ĉasashen biyu.
Kafin yaĈin filin jirgin sama na Dubai ne kan gaba a jerin filayen jirgin sama da fasinjoji ke zirga-zirga a duniya.
Hukumar sadarwar Uganda ta ce tana bincike kan matakin da aka Éauka na rufe manyan kafafen yaÉa labarai masu zaman kansu a Ĉasar, bisa umarnin babban hafsan sojin Ugandan Janar Muhoozi Kainerugaba.
Hukumar ta ce tana tuntuÉar mahukunta domin gane abin da ya faru.
Kamfanin da ya mallaki kafafen yaÉa labaran da aka rufe ya ce da tsakar dare jami'an tsaro suka dakatar da aiki a sashin kafar na Talabijin da na Rediyo da kuma na jarida, kuma suka hana shiga ofishin su na birnin Kampala.
Wani jirgin sama Éauke da Ĉ´an wasan zamiya ya yi hatsari a Gabashin Faransa kuma dukkan mutane 11 da ke ciki sun rasu.
Mutanen sun haÉa da masu horaswa biyar da Éalubansu biyar da kuma matuĈin jirgin.
Jirgin ya yi hatsari ne jim kaÉa bayan ya tashi, kuma wasu daga cikin Ĉ´an uwan mutanen da ke ciki suna kallo lokacin da ya faÉo.
Jirgin ya faÉo ne kusa da wata unguwa, kuma babu wanda abin ya shafa.
Kawo yanzu babu tabbacin abin da ya jnyo hatsarin.

Asalin hoton, Benue State Govt.
Gwamnan Jihar Beneu, Hyacinth Alia ya buĈaci jami'an tsaron jihar su gaggauta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa jagodan makiyayan jihar Alhaji ArÉo Risku da wasu suka kashe a jihar ranar juma'a.
Cikin wata sanarwa da sakataren ya da labaran gwamnan, Tersoo Kula ya fitar ya ce gwamnan ya bayar da umarni kamo wadanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban shari'a.
Gwamnan ya buĈaci hukomomin jihar su yi aiki tare da jagororin al'ummar jihar domin tabbatar da zaman lafiya.
Haka ma gwamnan ya buĈaci mambobin Ĉungiyar MACBAN da na sauran al'umma su kwantar da hankali domin bin doka da oda.
Daga Ĉarshe gwamnan ya miĈa saĈon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da duka mambobin Ĉungiyar makiyaya ta MACBAN.
Rundunar yansandan jihar ta ce ta kama wasu mutum 10 bisa zargin hannu a kisan ArÉo Risku.
Masu aikin ceto a Venezuela na ci gaba da zaĈulo mutanen da girgizar Ĉasar Venezuela ta ritsa da su.
Hukumomin Ĉasar sun ce fiye da mutum 1,400 ne suka mutu tun bayan girgizar Ĉasar da ta auku a Ĉasar cikin makon nan.
Wani bidiyo da masu aikin ceton su wallafa a ranar Asabar ya nuna yadda suka ceto wani jariri da mahaifiysa a daga ĈarĈashin Éaraguzai.

Asalin hoton, Gombe State Govt
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Gombe ta lashe duka zaÉukan Ĉananan hukukomin jihar 11 da aka gudanar ranatr Asabar 27 ga watan Yunin da muke ciki.
Yayin da yake bayyana sakamakon, shugaban hukumar zaÉen jihar, Abdullahi Garba, ya ce jam'iyyar APC ce ta lashe duka zaÉukan shugabannin Ĉananan hukumomin da na kansilolin jihar 240.
Dama dai a Najeriya galibi jam'iyyar da ke mulkin jiha ce ke lashe duka zaÉukan Ĉananan hukumomin jihar.
shugaban hukumar zaÉen jihar ya bayyana zaÉen a matsayin gagarumin ci gaba bayan da aka faÉaÉa Ĉananan hukukomin jihar zuwa gundumomin mulki 24.
Hukumomin tsaro a Ĉasar Iraq sun kama jamiâan gwamnati da Ĉ´an siyasa 47, ciki har da âyan majalisar dokoki, a wani samame da suka kai domin yaĈi da rashawa.
An gudanar da wannan farmaki ne a yankin Green Zone da ke Baghdad, wurin da ake tsaurara tsaro sosai a babban birnin Ĉasar.
Rahotanni sun ce wannan mataki na daga cikin sabuwar Ĉudirin yaĈi da rashawa da firaministan Ĉasar Iraq na yanzu, Ali Zaidi ke jagoranta.
Tun da farko ma an kama mataimakin ministan man fetur, Adnan Jalili.
Wani jamiâi a gwamnatin Iraq da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa ana zargin waÉanda aka kama da laifuka ciki har da wawure dukiyar gwamnati da safarar dala da kuma man fetur ba bisa Ĉaâida ba.

Asalin hoton, Seyi Makinde/X
Gwamnatin Jihar Oyo ta sanar da Éage dokar hana fita da ta sanya a Ĉananan hukumomi 10, biyo bayan sace mutanen da aka yi a yankin Oriire.
Tun farko gwamnati ta saka dokar hana fita na sa'o'i 16 kafin daga bisani ta Ĉara wani yini, domin daĈile matsalolin tsaro a yankin.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai, Prince Dotun Oyelade ya fitar, ya ce yanzu mazauna yankunan da abin ya shafa za su iya komawa gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Haka kuma ya gode musu kan haÉin kai da fahimtar juna da suka nuna a lokacin da dokar ke aiki.
Oyelade ya Ĉara da cewa gwamnati na ci gaba da sanya ido kan alâamuran tsaro a yankin, tare da tabbatar wa alâumma cewa ana ĈoĈarin ganin an shawo kan lamarin sace mutanen.
Lamarin sace mutanen ya faru ne a ranar 15 ga Mayu, lokacin da wasu âyanbindiga suka kai hari makarantu uku a yankin Oriire, inda suka sace Éalibai da malamai har 45. Bayan wasu kwanaki, rahotanni sun nuna cewa Éaya daga cikin malaman da aka sace, wanda ke koyar da lissafi, ya mutu a hannun maharan.

Asalin hoton, Getty Images
Wani jirgin ruwa mallakin wani kamfanin Faransa ya tsallaka mashigar Hormuz da izinin Iran, inda aka kuma tabbatar da cewa ya wuce cikin aminci ba tare da wata matsala ba.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya tashi ne daga kusa da Dubai a Hadaddiyar Daular Larabawa, kafin ya bi mashigar Hormuz zuwa gabar tekun Oman, inda yake a halin yanzu.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan yadda aka tsara wannan wucewar ba ko irin tsarin tsaron da aka tanada ba, duk da cewa kamfanin na da sauran jiragen ruwansa guda 10 a yankin Tekun Farisa.
Ministan sufuri na Faransa, Philippe Tabaro, ya yaba da wannan izini da Iran ta bayar, yana mai cewa jirgin na Éauke da tutar Faransa kuma maâaikatansa âyan Ĉasar Faransa ne.
A gefe guda kuma, Ĉasar Oman ta sanar da kirkirar wata hanya da za a bi a gaar tekunta, sai dai Iran ta jaddada cewa hanyarta ce kaÉai mai aminci, tare da gargaÉin cewa za ta Éauki mataki kan duk wanda ya karya wannan umarni.

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Israâila sun sanar a ranar Lahadi cewa Éaya daga cikin sojojinsu ya mutu yayin artabu a kudancin Lebanon, kwanaki biyu kacal bayan Israâila da Lebanon sun rattaÉa hannu kan wata yarjejeniya da ke nufin kawo Ĉarshen rikicin.
Wata sanarwa daga jamiâan sojin ta bayyana cewa mamacin, Kyaftin David Hazot Nezami mai shekaru 21, wanda ke jagorantar runduna, ya mutu ne lokacin da sojojin suka yi arangama da Ĉungiyar Hezbollah a yankin Deir Saryan.
Rahoton ya kuma ce wasu daga cikin sojojin Israâila sun samu raunuka sakamakon arangamar.
A gefe guda kuma, kafar yaÉa labarai ta gwamnatin Lebanon ta ruwaito cewa Israâila ta kai wani hari ta sama a wajen garuruwan Deir Ezzor da Tayyiba a kudancin Ĉasar.
Tun bayan Éarkewar rikicin Israâila da Hezbollah a farkon watan Maris, an tabbatar da mutuwar sojojin Israâila 38 da kuma farar hula Éaya da ke aiki tare da su.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon mataimakin shugaban Ĉasa kuma Éan takarar shugaban Ĉasa a ĈarĈashin jamâiyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi allawadai da abin da ya kira yunĈurin daĈile rajistar jamâiyyar NDC, yana mai zargin cewa hakan wani yunĈuri ne na karkatar da Najeriya zuwa tsarin jamâiyya daya Ĉarkashin Shugaba Bola Tinubu.
Atiku ya yi wannan martani ne bayan wata kotun tarayya da ke Lokoja jihar Kogi ta soke hukuncinta na ranar 10 ga Disamba 2025 wanda ya bai wa hukumar zaÉe mai zaman kanta (INEC) umurnin yi wa NDC rajista a matsayin jamâiyya.
Mai shariâa Isah Dashen ya ce ya kamata a shigar da jamâiyyar PMP a cikin Ĉarar, domin shariâar ta shafi muradunta.
A cikin wata sanarwa da ofishin yaÉa labaran Atiku ya fitar, ya ce bai yi mamakin wannan hukunci ba, yana mai gargaÉin cewa idan aka ci gaba da abin da ya kira shirin raunana âyan adawa domin bai wa Tinubu damar sake tsayawa takara a 2027, hakan na iya janyo mummunan sakamako ga dimokuraÉiyya.
Ya Ĉara da cewa shiga cikin zaÉuÉÉuka ginshiĈin dimokuradiyya ne, kuma duk wani yunĈuri na hana âyan kasa âyancin zaÉe na iya jawo ârikici da tarzoma.â
Haka kuma ya buĈaci Éangaren shariâa su kiyaye mutuncinsu tare da kauce wa shiga siyasa, yana mai cewa kotuna su ne mafakar talakawa, don haka bai kamata a lalata amincinsu ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya yi gargaÉin cewa duk wani yunĈuri na katsalandan a yadda Iran ke tafiyar da mashigar Hormuz zai Ĉara tsananta rikici a yankin.
Araqchi, wanda ke ziyara a birnin Baghdad, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai tare da takwaransa na Iraq, inda ya ce bisa fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, za a dawo da zirga-zirgar mashigar cikin kwanaki 30, a ĈarĈashin cikakken ikon Iran kaÉai.
Ya jaddada cewa Iran ce ke da alhakin aiwatar da wannan tsari, yana mai cewa duk wani ĈoĈari na ĈirĈirar wata hanya dabam ko tsoma baki daga waje zai janyo tsaiko da kuma Ĉarin rikice-rikice, wanda a cewarsa tuni an fara gani a abubuwan da suka faru cikin dare biyu a yankin.
A cikin kwanaki uku da suka gabata, an kai hari kan aĈalla jiragen ruwa biyu da ke wucewa mashigar Hormuz, lamarin da ya haddasa musayar wuta tsakanin Iran da Amurka, inda kowanne Éangare ke zargin Éaya da karya yarjejeniyar tsagaita wuta..

Asalin hoton, Hyacinth Alia/X
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya umarci hukumomin tsaro da su fara bincike nan take kan kisan shugaban Ĉungiyar makiyaya ta MACBAN a jihar, Alhaji Ardo Risku, tare da abokinsa.
Ya bayyana matuĈar kaÉuwarsa da alhini kan lamarin, yana mai cewa ya zo ne a wani lokaci da jihar ke fara samun zaman lafiya a yankuna daban-daban.
Gwamnan ya ce wannan kisan ba wai kawai abin takaici ba ne, har ma wata ĈoĈari ce ta karya zaman lafiya da sulhun da gwamnatinsa ke ĈoĈarin tabbatarwa, musamman ganin cewa ya faru ne jim kaÉan bayan wani muhimmin taron tsaro.
Saboda haka ya buĈaci a gudanar da bincike mai zurfi da gaskiya, tare da kamo waÉanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban shariâa
Haka kuma ya yi kira ga alâumma su kwantar da hankalinsu, yana mai gargaÉin cewa bai kamata a bari masu anfani da rikici su tayar da tarzoma ba, tare da miĈa taâaziyya ga iyalan mamatan.

Asalin hoton, Getty Images
Adadin waÉanda suka mutu a girgizar Ĉasa mai Ĉarfi guda biyu da suka afkawa Ĉasar Venezuela ya haura 1,400, yayin da har yanzu ake ci gaba da ayyukan ceto.
Kwana uku bayan afkuwar girgizar, ana neman mutane da dama da suka Éace, yayin da jamiâan agaji ke ci gaba da tono waÉanda suka maĈale a ĈarĈashin Éaraguzai.
A lokaci guda, Ĉorafe-Ĉorafen jamaâa na Ĉaruwa kan yadda gwamnati ke tafiyar da lamarin.
Wakilin BBC da ke garin La Guaira, wanda ya fi fuskantar iftilaâin, ya ce halin da ake ciki na da matuĈar tsanani, inda har yanzu ba a san adadin mutanen da ke maĈale a ĈarĈashin gine-ginen da suka rufta ba.
Ĉungiyoyin agaji na Ĉasa da Ĉasa sun isa yankin, inda Ĉungiyoyi daga Ĉasashen Mexico, Brazil, da sauransu ke aiki ba dare ba rana wajen ceto da taimakawa waÉanda balaâin ya shafa.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito cewa wani jamiâin Amurka ya tabbatar da cewa Iran ta harba makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuĈa zuwa wasu Ĉasashe makwabta, ciki har da Bahrain da Kuwait.
Tuni rundunar IRGC ta Iran ta sanar cewa ta kai hari kan wuraren sojojin Amurka, inda ta ce ta nufi sansanin Ali al-Salem da ke Kuwait, da kuma hedikwatar rundunar ruwa ta Amurka da ke Bahrain.
Rundunar ta ce ta kai waÉannan hare-hare ne da makamai masu linzami da jiragen yaĈi marasa matuĈa.

Asalin hoton, Getty Images
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, zai kai ziyara Ĉasar Iraq a yau Lahadi tare da wata tawaga ta diflomasiyya.
Mai magana da yawun maâaikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baghai, ya ce a yayin ziyarar, za a tattauna dangantakar Ĉasashen biyu tare da nazarin halin da ake ciki a yankin da kuma duniya baki Éaya, a tattaunawa da manyan jamiâan gwamnatin Iraq.
Ya Ĉara da cewa Éangarorin biyu za su yi musayar raâayi kan muhimman batutuwa da suka shafi siyasa da tsaro a yankin, da kuma Ĉarfafa haÉin gwiwa tsakanin Iran da Iraq.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar juyin juya halin Iran IRGC ta Iran ta sanar cewa da safiyar Lahadi ta kai hari kan muhimman wuraren sojojin Amurka a Ĉasashen Kuwait da Bahrain, ta da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuĈa.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta kai harin ne a wurare takwas na sojojin Amurka, ciki har da sansanin jiragen sama na Ali al-Salem Air Base da ke Kuwait, da kuma hedikwatar rundunar ruwa ta Amurka ta Fifth Fleet da ke Bahrain.
Rundunar ta IRGC ta ce wannan hari martani ne ga hare-haren da Amurka ta kai a baya.
Sai dai har yanzu jami'an Amurka ba su yi tsokaci ba kan girman Éarnar da aka yi ko yiwuwar asarar rayuka.
Haka kuma IRGC ta zargi Amurka da kai hari kan sansanonin ruwan Iran guda biyar, tana mai cewa an yi hakan ne da sunan cewa rundunar ruwan IRGC ta tare wani jirgi.
Sanarwar ta jaddada cewa bisa yarjejeniyar da aka cimma, Iran ce ke da alhakin kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, kuma daga yanzu rundunar IRGC za ta Éauki matakai masu tsauri kan duk wani jirgin ruwa da ta Éauka a matsayin âmai karya doka.â
Masu bibiyarmu a shafinmu na BBC hausa kai tsaye barkanmu da safiyar yau Lahadi.
Kamar dai yadda aka saba wannan shafi ne da zai kawo muku labarai na abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, da Najeriya da sauran sassan duniya.
Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.
Za ku iya leĈawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.
Ku kasance tare da mu.