KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Laraba 09/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir

Rahoto kai-tsaye

Daga Muslim Muhammad Yusuf

  1. Najeriya ta yi Allah-wadai da sabbin hare-haren Houthi a Saudiyya

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da sabbin hare-haren da mayaƙan Houthi a Yemen suka kai wa Saudiyya ranar Litinin 7 ga Satumba 2026, waɗanda suka jikkata fararen hula da dama tare da lalata wasu muhimman gine-ginen farar hula.

    A wata sanarwa da kakakin ma'aikatar Oluwafemi Adeniyi ya fita, Najeriya ta ce tana kallon sabbin hare-haren a matsayin babbar barazana ga tsaro da ikon Saudiyya, da kuma zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

    Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa, kuma su yi taka-tsantsan tare da kauce wa duk wani mataki da ka iya ƙara ruruta rikicin.

    Ta ce ƙara dagulewar lamarin na iya jefa rayukan fararen hula cikin haɗari, barazana ga tsaron yankin da kuma ƙara kawo cikas ga samar da makamashin da ake buƙata a duniya.

    "Najeriya na goyon bayan gwamnati da al’ummar Saudiyya a wannan lokaci mai wahala, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa," in ji sanarwar.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da goyon bayan matakan samar da zaman lafiya da sasanta rikice-rikice da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

  2. Amurka ta ƙara faɗaɗa takunkuman kasuwanci kan kayayyakin Kanada

    Amurka da Kanada

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta faɗaɗa takunkuman kasuwanci kan kayayyakin Kanada, inda ta haramta shigar da wasu kayayyaki gaba ɗaya, yayin da saɓanin tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara kamari.

    Sabbin matakan sun haɗa da hana shigar da barasa, kayayyakin madara da babura daga Kanada zuwa Amurka.

    Shugaba Donald Trump ya zargi Kanada da nuna wariya ga Amurka, bayan da gwamnatin Kanada ta fara aiwatar da harajin ramuwar gayya na kashi 50 cikin 100, daidai da matakan da Washington ta ɗauka kan kayayyakin Kanada.

    Ana sa ran sabbin takunkuman na Amurka, waɗanda suka haɗa da ƙara yawan kayayyakin Kanada da za a ƙaƙaba wa haraji, za su fara aiki a ƙarshen wannan watan.

    Firaministan Kanada, Mark Carney, ya gargaɗi ƴan ƙasar cewa rage dogaro da makwabciyarsu Amurka ba zai rasa tasiri ga tattalin arzikin Kanada ba.

    Sai dai ya ce, hakan shi ne mafi alheri fiye da ci gaba da sayen kayayyakin Amurka.

  3. Ƴan jarida 5 sun yi ɓatan dabo a kan hanyarsu ta zuwa ɗauko rahoto

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƴan jarida biyar na Indonesia sun ɓace bayan da suka yi tafiya da jirgin ruwa domin ɗauko rahoto kan fashewar wani dutse mai aman wuta na Mount Anak Krakatau.

    Jami’an agaji na ci gaba da neman ƴan jaridar tare da wasu mutum uku da ke cikin jirgin a lokacin da suka ɓace.

    Fashewar dutsen mai aman wutar, wadda ta fara a daren Juma’a, ta janyo dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tare da rufe sararin samaniya da toka mai kauri a birane da dama, ciki har da babban birnin ƙasar, Jakarta.

    Ana ci gaba da aikin bincike da ceto, sai dai igiyar ruwa mai ƙarfi da rashin kyakkyawar hango nesa na haifar da jinkiri wajen aikin ceton.

    Hatsarin teku ya kasance ruwan dare a wannan yanki, sakamakon rashin tsauraran matakan kiyaye lafiya a harkar sufuri ta ruwa da kuma matsanancin yanayi da ake fuskanta a lokuta daban-daban.

  4. Farashin ɗanyen man Brent ya kai dala 100

    Brent

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen man Brent ya haura dala 100 kan kowace ganga a kasuwar duniya a yau.

    Wannan ne karon farko tun watan Yuli da farashin mai ya haura dala 100, yayin da ake ci ga gaba da zaman ɗar-ɗar a Gabas ta Tsakiya.

    Farashin man ya ci gaba da hauhawa a hankali a cikin ƴan makonnin nan, har ya haura wannan dala 100.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa harin da ƴan Houthi na Yemen suka kai kan cibiyoyin mai na Saudiyya a wannan makon ya haddasa gobara a cibiyar.

    Rahoton ya ce lamarin na iya yin barazana ga jigilar ɗanyen mai ta Tekun Maliya, wadda ke zama wata hanya ta daban bayan mashigar Hormuz.

  5. Kotu ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM

    Robert Orya

    Asalin hoton, @officialEFCC/X

    Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 490 a gidan yari da aka yanke wa tsohon shugaban bankin shige da fitar da kayayyaki a Najeriya na NEXIM, Robert Orya.

    Kotun ta ce ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume 49, inda aka yanke masa hukuncin shekaru 10 a kan kowanne tuhuma, wanda ya kai jimillar shekaru 490, kuma hukuncin zai gudana ne a lokaci guda.

    Robert Orya ya rike muƙamin Manajan Daraktan bankin NEXIM tsakanin shekarar 2009 da 2016 a zamanin mulkin marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua, sannan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya sake naɗa shi a 2014.

    Bayan ya bar muƙaminsa, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2021 kan tuhume-tuhume 49 da suka haɗa da karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da zamba da suka kai naira biliyan 2.4.

    A ranar 5 ga Fabrairu 2026, wata Babbar Kotun Babban Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 490 a gidan yari, wanda za a yi a lokaci guda.

    A hukuncin da kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara suka yanke, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muhammed Danjuma, kotun ta ce alkalin kotun farko, Mai Shari’a Messiri, ya yi daidai wajen yanke hukuncin.

    Mai Shari’a Danjuma, tare da sauran alkalan biyu, Ntong Ntong da Ele Enenche, sun ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa Orya ba tare da wata tantama ba.

  6. Iran ta ce ta kai harin makamai masu linzami kan tankokin yaƙin Amurka

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran, IRGC, ta ce ta kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka guda biyu da makamai masu linzami.

    A cikin wata sabuwar sanarwa da rundunar ta fitar a safiyar Laraba, ta ce ta kai harin ne kan jiragen ruwan yaƙin Amurka DDG-119 da DDG-53, waɗanda ke ɗauke da makamai masu linzami na cruise da na Aegis.

    Rundunar ta yi iƙirarin cewa harin ya lalata jiragen.

    Hakan na zuwa ne sa'a guda bayan da Rundunar Tsakiyar Sojin Amurka, CENTCOM, ta ce ta kai hari tare da lalata tankokin ɗaukar ɗanyen man Iran guda biyar, a matsayin martani ga yunƙurin Iran na kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka.

  7. Batun addini ne ke taka rawa a shari'ar El-Rufai - NSCIA

    El-Rufai

    Asalin hoton, El-Rufai/X

    Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta nuna damuwa kan abin da ta kira alamun nuna wariyar addini a shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

    A wata sanarwa da Sakataren Janar na majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya fitar, NSCIA ta ce ta daɗe tana ƙoƙarin ganin ta kaurace wa yin tsokaci kan shari'ar, saboda tun farko ta ɗauke ta a matsayin shari'a ta yau da kullum, tare da tunanin cewa kotuna za su iya tabbatar da adalci.

    Sai dai majalisar ta ce wasu abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, sun sa ta fara ganin akwai alamun wariyar addini ce ke taka rawa a shari'ar.

    Wannan ya biyo bayan kalaman Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, wanda ya zargi El-Rufai da shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamna.

    NSCIA ta ce waɗannan kalamai sun sa ta sauya matsayinta na ƙin tsoma baki a batun, tana mai cewa akwai abubuwan da ke nuna yiwuwar wani "son zuciya na wariyar addini" a kan tsohon gwamnan.

    Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ɓangaren shari'a da su tabbatar da cewa ba a yi amfani da hukumomin gwamnati ko tsarin shari'a wajen aiwatar da wata manufa ta bangaranci a kan El-Rufai ba.

    Ta kuma yi kira ga jama'a da su guji kalaman tunzura jama'a da ka iya yin tasiri kan shari'ar El-Rufai ko kuma ƙara dagula yanayin tsaro a Najeriya.

  8. Amurka ta mayar da martani kan iƙirarin Iran na kama jirgin ruwanta

    Jirgin ruwan Amurka da Iran ta ƙwace

    Asalin hoton, Getty Images

    Hedikwatar Rundunar Sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta mayar wa BBC martani kan ikirarin da Iran ta yi na cewa ta kama wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku maras matuƙi na Amurka a mashigin Hormuz.

    A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun CENTCOM, Laftanar Kyaftin Tim Hawkins, ya ce jirgin ruwan ƙarƙashin tekun ya lalace ne fiye da kwana ɗaya da ya gabata.

    Ya ce jirgin yana sintiri ne a ruwan yankin domin tallafa wa ayyukan da sojojin Amurka ke ci gaba da gudanarwa.

    Hawkins ya ƙara da cewa, "jirgin tsohon samfuri wanda ba ya tattara muhimman bayanan sirri, kuma ba ya ɗauke da na'urorin radar ko na'urorin gano bayanai masu sirri."

    Ya kuma ce ayyukan sojojin Amurka a ruwan yankin na ci gaba kamar yadda aka saba.

    A sa'o'in da suka gabata ne kamfanin dillancin labarai na Fars, mai alaƙa da rundunar juyin juya halin Iran, ya ba da rahoton cewa Iran ta "kama" wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku mai fasahar zamani na Amurka.

    A cewar Fars, jirgin na daga cikin sababbin jiragen ruwa marasa matuƙi masu zamani da sojojin Amurka ke amfani da su.

    Kamfanin ya kuma ce an kama jirgin ne a bakin shiga mashigar Hormuz.

  9. Laraba ta Bawa!!!

    Barka da Safiya daga BBC.

    Asalin hoton, Getty Images

    Barka da Safiya daga BBC Hausa a wannan rana ta Laraba.

    Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin kallon wasu hotuna da bidiyon hirarraki da muke wallafawa tare da yin tsokaci a kai.