Arbeloa zai bar aikin kociyan Real Madrid a karshen kakar bana

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 24 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

  • Ingila za ta buga gasar kofin duniya ba tare da Foden da Palmer da Arnold
  • Burin Ronaldo ya ci ya lashe babban kofin Saudiyya a bana
  • Manchester United ta tabbatarwa da Carrick mukamin kociyanta
  • Guardiolazai bar Manchester City bayan sama da shekara 10 a Etihad
  • Mourinho na son Rashford a Madrid, Everton na harin Osula
  • Arbeloa zai bar Real Madrid a karshen kakar nan
  • Brazil ta saka Neymar cikin ƴan wasan da za su buga mata kofin duniya
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Romero ba zai kalli wasan karshe na Tottenham ba, yana Argentina, Tottenham

    Kocin Tottenham, Roberto De Zerbi, ya kare matakin ƙyaftin ɗin ƙungiyar, Cristian Romero na rashin halartar wasan ƙarshe a kakar da da za ta buga da Everton, amma ya ce ya “fahimtar ɗari bisa ɗari” dalilin da ya sa magoya baya suke jin haushi.

    Romero mai shekara 28 zai kasance a ƙasarsa ta Argentina maimakon kasancewa tare da Tottenham a wasan ranar Lahadi, inda ƙungiyar ke fafutukar kauce wa faduwa daga Premier League.

    Dan wasan tawagar Argentina ba zai buga karawar ba saboda raunin gwiwa da yake jinya, kuma yana kokarin murmurewa kafin fara gasar FIFA World Cup ta wannan kakar.

    Nasarar da Tottenham za ta samu za ta tabbatar mata da tsira daga faɗuwa, yayin da ko kunnen doki ma zai iya wadatar da ita, saboda tana da bambancin kwallaye fiye da naWest Ham United da ke matsayi na 18.

    Yayin da wasu ƴan wasan Tottenham da ba za su iya buga wasan ba, ciki har da Ben Davies, za su halarci karawar ana sa ran Romero zai kalli tsohuwar ƙungiyarsa ta yarinta Belgrano tana wasa da River Plate.

    De Zerbi ya bayyana cewa shawarar komawar Romero Argentina an yanke ta ne tare da amincewar ma’aikatan lafiyar ƙungiyar.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Salah ya ce ba zai manta da Liverpool ba tana cikin ransa har abada, Liverpool

    Mohamed Salah ya bayyana cewa zai ci gaba da son Liverpool har abada, yayin da zamansa na shekara tara a kungiyar ke karewa.

    Ɗan wasan Liverpool ya ce wannan kakar ita ce mafi wahala kuma mafi rashin jin dadi a rayuwarsa a Anfield, duk da manyan nasarorin da ya samu a Anfield ciki har da lashe Champions League, kofunan Premier League guda biyu da kuma kyautar Golden Boot sau huɗu.

    A watan Disamba an cire shi daga cikin ƴanwasan da ke fara taka leda a ƙungiyar bayan da ya yi ikirarin cewa an “jyi watsi da shi” , yayin da ya koma zaman benci, saboda rashin kyawun sakamakon da kungiyar ke samu. Haka kuma ya bayyana cewa dangantakarsa da koci Arne Slot ta lalace.

    Daga baya an sasanta rikicin har ya dawo cikin ƴan wasan, bayan gasar Africa Cup of Nations, amma shawarar da bangarorin biyu suka ɗauka na rabuwa duk da saura shekara daya a kwantiraginsa ta nuna cewa zaman lafiyar na wucin gadi ne kawai.

    Sakon da Salah ya wallafa a shafukan sada zumunta bayan shan kashin da suka yi a hannun Aston Villa a makon da ya gabata, inda ya yi kira da a dawo da salon taka leda na zamanin Jürgen Klopp, ya samu goyon bayan magoya baya amma bai nuna cewa shi da Slot suna fahimtar juna ba.

    Yayin da ranar bankwanarsa da Liverpool ke kara matsowa, kafin wasan da za su yi da Brentford ranar Lahadi, Salah ya yi magana mai cike da tausayawa game da ƙungiyar da magoya bayansa.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. , Daga Jarida

    Har ila yau Everton na sha'awar Wilson, wanda za a iya ɗaukarsa a cinikin kyauta idan kwantiraginsa ya kare a watan Yuni. (Sky Sports)

    Brighton na tattaunawa da Olympiacos kan cinikin Costinha ɗan ƙasar Portugal mai shekara 26 wanda ke ɗauke da farashin fam miliyan 11. (Athletic)

    Newcastle za ta yi zawarcin ɗan wasan gaban Porto ɗan ƙasar Belgium Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21, idan ɗan wasan gaban Ingila Anthony Gordon, mai shekara 25, ya bar kulob ɗin a bazara. (Mail)

    Manchester United na kallon ɗan wasan baya na Newcastle Lewis Hall a matsayin wanda zai iya bunƙasa tawagar ƴanwasanta a kakar wasa mai zuwa, yayin da Bayern Munich da Liverpool su ma su ke sanya ido kan ɗan wasan na Ingila mai shekara 21. (Teamtalk)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Newcastrle ba za ta yi kuskure kamar yadda ta yi a bara a kan Isak ba, Premier League

    Kocin Newcastle United, Eddie Howe, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ƙungiyar ba za ta sake fuskantar kuskure irin na bara ba, bayan tafiyar Alexander Isak da ya lalata shirye-shiryenta kafin fara kakar wasan bana.

    Tafiyar Isak zuwa Liverpool kan kuɗi fam miliyan 130, bayan ɗan wasan Sweden ya yi yajin aiki domin tilasta cinikin, ta bar babban gibi a cikin tawagar Newcastle, kuma rashin samun wanda zai maye gurbinsa cikin sauri ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin kakar wasansu mai wahala.

    Sai dai Howe ya yi imanin cewa yanzu Newcastle tana cikin matsayi mafi kyau domin aiwatar da shirye-shiryenta na gaba.

    Newcastle za ta shiga wasan ƙarshe a kakar wasa da Fulham ranar Lahadi tana matsayi na 11 a teburin Premier League, kuma ba za ta buga gasar Turai a kakar wasa mai zuwa ba. Duk da haka, Howe yana ganin akwai wani alheri a hakan.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Arbeloa zai bar aikin kociyan Real Madrid a karshen kakar bana, Real Madrid

    Kocin Real Madrid, Álvaro Arbeloa ya tabbatar da cewa zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan bana, yayin da ake sa ran José Mourinho zai maye gurbinsa.

    Arbeloa, mai shekara 43, ya karɓi aikin koyar da Real Madrid a matakin riƙon kwarya a watan Janairu, inda ya maye gurbin tsohon abokin wasansa, Xabi Alonso. Yanzu zai bar ƙungiyar bayan kakar da ba ta kawo kofi ba ga Real madrid karo na biyu a jere.

    Mourinho, wanda ke jagorantar Benfica a wannan kakar, yana cikin tattaunawa ta ƙarshe don dawo da Real Madrid kan ganiya, bayan da ya taɓa horar da su daga 2010 zuwa 2013.

    Arbeloa ya faɗa a taron manema labarai kafin wasan ƙarshe a kakar da za su buga da Athletic Club cewa ba zai shiga tawagar Mourinho ba idan ya zo ya kama aiki. Ya ce: “Mou yana da ƙwararrun ma’aikata, idan ya zo Madrid zai zo da tawagarsa. Ba zan kasance tare da shi ba.”

    Ya kuma ƙara da cewa yana fatan wannan wasan ba zai zama bankwana na ƙarshe da ƙungiyar ɗin ba, inda ya jaddada cewa Real Madrid ita ce “gidansa” bayan shekara 20 yana aiki da ita a matakai daban-daban.

    A bangaren ƙungiyar kuma, an tabbatar da cewa ɗan wasan baya David Alaba mai shekara 33 zai bar Real Madrid a ƙarshen kakar nan, bayan lashe kofuna 11 cikin shekara biyar, duk da raunin da ya yi fama da shi.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  6. , Daga jaridu

    Inter Milan na nazarin zawarcin golan Arsenal ɗan ƙasar Spain Kepa Arrizabalaga mai shekara 31. (Gazzetta)

    Naɗin Xabi Alonso a matsayin kocin Chelsea na iya lalata fatan Atletico Madrid na ɗaukar Marc Cucurella, mai shekara 27, inda kocin mai shekara 44 ke sha'awar ci gaba da riƙe ɗan wasan bayan na Spain. (Mundo Deportivo)

    Arsenal na shirin miƙawa ɗan wasan baya na ƙasar Netherlands Jurrien Timber mai shekara 24 da sabon kwantaragi. (Caught Offside)

    Liam Delap yana gab da barin Chelsea, inda Everton ke kan gaba wajen zawarcin ɗan wasan na Ingila mai shekara 23. (Football Insider)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Ƴan wasan Nottingham Forest hankalinsu na kwance - Pereira, Premier League

    Kociyan Nottingham Forest, Vitor Pereira ya bayyana cewa yanayin cikin ƙungiyar ya sauya bayan da suka tabbatar da tsira daga faduwa daga Premier League.

    Forest za ta je wasan karshe a kakar bana da Bournemouth a ranar Lahadi ba ta tafuskantar wata barazana, bayan da ta riga ta yi nisa daga yankin faduwa da tazarar maki shida.

    Nottingham Forest ta yi rashin nasara a wasan Premier League a makon da ya gabata bayan ta sha kashi 3-2 a hannun Manchester United.

    A wasan, kwallayen Luke Shaw da Matheus Cunha da Bryan Mbeumo sune ka bai wa Manchester United rinjaye, duk da ƙoƙarin da Morato da Morgan Gibbs-White suka yi wa Forest.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  8. ''Da ƙyar ne idan Chelsea za ta dawo Premier League a kaka ɗaya'', Premier League

    Mai rikon mukami kociyan Burnley, Mike Jackson, ya yi gargaɗi cewa babu tabbacin cewa ƙungiyar za ta koma Premier League kai tsaye, bayan sake faduwarsu karo na uku cikin shekaru biyar.

    Tun bayan kammala zaman shekara biyar a gasar Premier League a 2022, ƙungiyar Clarets ta samu nasarar dawowa daga EFL Championship sau biyu a jere a farkon yunƙurin da ta yi.

    Burnley ta yi nasara a wasa huɗu kacal daga cikin 37 da ta buga a kakar nan, kafin ta kammala kakar ta rashin nasara da wasa da Wolverhampton Wanderers a ranar Lahadi.

    Ɗaya daga cikin nasarorin gida biyu kacal da suka samu a wannan kakar ta zo ne a watan Oktoba, abin da ke nuna irin ƙalubalen da ƙungiyar ta fuskanta a kakar wasa mai wahala.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  9. , Daga Jaridu

    Arsenal da Juventus suna sanya ido kan ɗan wasan tsakiyar Manchester City Tijjani Reijnders, mai shekara 27, yayin da ɗan wasan na Netherlands ke samun taƙaitacen lokacin buga wasa tun zuwansa a bazarar da ta gabata. (TeamTalk)

    Manchester United na da ƙwarin gwiwar kulla cinikin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Newcastle da Italiya Sandro Tonali, mai shekara 26, da ɗan wasan Atalanta da Brazil Ederson mai shekara 26 a bana. (Sky Sports Italia)

    Chelsea ta bi sahun Arsenal wajen zawarcin ɗan wasan gaban Bournemouth ɗan ƙasar Faransa Eli Junior Kroupi, amma Cherries ta ce ɗan wasan mai shekaru 19 ba na sayarwa bane. (Mail)

    Ɗan wasan Fulham ɗan ƙasar Wales,Harry Wilson mai shekara 29, yana cikin jerin sunayen ƴan wasan da kocin Aston Villa Unai Emery zai yi zawarci a bazara bayan da aka ba shi kasafin kudin sayan ƴan wasa fam miliyan 100 sakamakon nasarar da kulob ɗin ya samu a gasar cin kofin Europa League. (Mirror)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Ƴanwasan Premier League da ba su yi ƙoƙari ba a 2025/26, Premier League

    A kakar Premier League ta 2025/26, an shaida labarai masu jan hankali da dama. Wasu ƙungiyoyi da ƴan wasa suna taka rawar gani da take burge magoya baya, wasu kuwa suna jin dadi da rawar da suke takawa. Amma akwai wasu da suka kasa taka rawar gani ko komawa kan ganiya a kakar nan.

    Sabbin ƴan wasa da aka saya su ne suka fi fuskantar matsin lamba. Yawancinsu sun je sabbin ƙungiyoyinsu cikin farin jini da fatan za su daga darajar ƙungiyoyinsu. Sai dai bayan watanni ana buga gasar bana, wasu daga cikin waɗannan fata da aka yi ya koma takaici da tambayar ko da gaske an bukaci sayensu, ko ya dace da aka sayo su.

    A lokacin kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo kan fara kakar nan, an kulla cinikin sayen manyan ƴan wasa har guda 155 a gasar Premier League, sannan aka kara wasu sababbin ƴan ƙwallon a watan Janairu. Yanzu mafi yawan ƴan wasan sun yi watanni suna taka leda, ana iya tantance waɗanda suka yi tasiri da kuma wadanda suka gaza. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Kompany ba zai fayyace kwazon da suka yi a bana ba, sai bayan DFB-Pokal, Bundesliga

    Kocin Bayern Munich, Vincent Kompany, ya ce ba zai fayyace kwazon da suka yi a bana ba, har sai bayan wasan ƙarshe a DFB-Pokal da za su buga da masu riƙe da kofin VfB Stuttgart ranar Asabar.

    Ƙungiyar Bayern ta lashe Bundesliga cikin sauƙi a wannan kakar, amma ta rasa damar cin kofuna uku (treble) bayan da masu riƙe da kofin, Paris Saint-Germain suka fitar da ita da jimillar kwallaye 6-5 a wasan kusa da ƙarshe a UEFA Champions League a farkon watan Mayu.

    Wannan ne karo na farko cikin shekara shida da Bayern za ta buga wasan ƙarshe a German Cup, tun bayan da ta lashe kofin cikin gida biyu a lokaci guda (domestic double) a baya. Kompany ya ɗauki Bundesliga sau biyu a jere a kakar wasanninsa biyu na farko tare da Bayern, yayin da ƙungiyarsa ta karya tarihin yawan cin ƙwallayen da aka ci a kakar wasa guda a bana.

    Nasarar da za su samu a Berlin ranar Asabar za ta kuma rage radadin ficewarsu daga gasar Turai a hannun PSG.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Jamhuriyar Congo za ta killace kanta, saboda cutar Ebola, kafin ta shiga Amurka, Gasar kofin duniya

    Sakamakon barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Congo, an umarci ƴan tawagar ƙwallon ƙafa ƙasar da su killace kansu kafin su shiga Amurka, domin gasar FIFA World Cup.

    Andrew Giuliani, daraktan zartarwa na kwamitin Fadar White House mai kula da gasar kofin duniya, ya tabbatar wa ESPN a ranar Juma’a cewa tawagar Congo dole ne ta ci gaba da killace kanta da yin atisaye a Belgium na kwanaki 21, ko kuma ta iya fuskantar hana shiga Amurka.

    Congo tana cikin rukuni na 11 a gasar kofin duniya da za a buga a bana. Wasanta na farko zai kasance da Portugal a ranar 17 ga watan Yuni a Houston, sannan za ta kara da Colombia a ranar 23 ga watan Yuni a Guadalajara, kafin ta fafata da Uzbekistan a ranar 27 ga watan Yuni a Atlanta.

    Dukkan ƴan wasan tawagar Congo, tare da kocinsu ɗan Faransa, Sebastien Desabre, suna zaune ne a wajen ƙasar ta tsakiyar Afirka. Yawancinsu suna taka leda a Turai, ciki har da mai tsaron baya, Aaron Wan-Bissaka na West Ham United da Yoane Wissa na Newcastle United a gasar Premier League, da kyaftin kuma mai tsaron baya, Chancel Mbemba na Lille OSC a gasar Ligue 1.

    A farkon wannan watan, Congo ta tabbatar da barkewar wata nau’in Ebola da ake kira Bundibugyo Ebola. Sama da mutane 130 sun mutu daga cikin kusan mutane 600 da ake zargin sun kamu da cutar.

    Congo ta soke sansanin atisayenta a babban birnin ƙasar, Kinshasa, saboda barkewar cutar, sannan ta koma Belgium inda take da wasan sada zumunci da Denmark a Liege ranar 3 ga watan Yuni. Haka kuma tana da wani wasan sada zumunci da Chile a kudancin Sifaniya ranar 9 ga watan Yuni.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Manchester City ta sanar da ajiye aikin Pep Guardiola

    Pep

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Manchester City ta tabbatar cewa mai horas da ƴan wasanta Pep Guardiola zai bar ƙungiyar bayan wannan kaka.

    Guardiola zai bar City ne bayan horas da ƙungiyar a wani lokaci da ta fi samun nasara a tarihinta.

    Pep ya je Manchester City ne a watan Fabarairun 2016, inda tun daga lokacin ya jagorance ta wajen lashe kofuna 17, ciki har da kofunan Premier 6 a cikin kakar wasa 10.

    Wasan da Guardiola zai jagoranta na ƙarshe shi ne karawar City da Aston Villa a ranar Lahadi 24 ga watan Mayu.

    Lokacin da ya sanar da batun barin sa daga ƙungiyar a shafinta na intanet, Pep ya ce: "Kada ku tambaye ni dalilin bari na. Babu wani dalili, amma a cikin zuciyata na san cewa lokaci ya yi. Babu wani abu da zai ɗore har abada, in da akwai, to da na ci gaba da zama a nan. Abin da zan ci gaba da tunawa har abada shi ne abubuwan da suka faru, da yadda na riƙa ji da kuma soyayyar da nake yi wa Manchester City."

  14. Ingila ba ta gayyaci Foden da Palmer da Arnold gasar cin kofin duniya 2026, Gasar kofin duniya

    Phil Fodenda Cole Palmer da Trent Alexander-Arnold ba sa cikin jerin ƴan wasa 26 da tawagar Ingila karkashin koci, Thomas Tuchel ya zaɓa domin buga gasar kofin duniya a bana.

    Mai tsaron bayan Manchester United, Harry Maguire, shi ma ba a gayyace shi ba, inda ɗan wasan mai shekaru 33 ya ce ya “yi mamaki kuma ya ji takaici sosai” da wannan hukunci.

    Ɗan wasan gaba na Aston Villa, Ollie Watkins, ya samu shiga cikin ƴan wasan, bayan da ya taimaka wa ƙungiyarsa ta lashe gasar UEFA Europa League a ranar Laraba. Haka kuma an saka ɗan wasan gaba na Al-Ahli, Ivan Toney, wanda ya ci ƙwallaye 32 a wasa 32 a gasar Saudiyya ta bana.

    Ɗan wasan Nottingham Forest, Morgan Gibbs-White, bai samu shiga ba duk da kasancewarsa ɗan Ingila mafi yawan cin ƙwallaye a Premier League a wannan kakar, tare da Watkins da Dominic Calvert-Lewin, inda kowannensu ya ci ƙwallo 14.

    Ɗan wasan Manchester City, Foden da na Chelsea, Palmer — waɗanda dukkansu suna buga tsakiya, sun ci karo dakoma baya a bana, saboda ba sa kan ganiya.

    A wani saƙo da ya wallafa a Instagram, Maguire ya tabbatar da cewa: “Na yi imanin zan taka muhimmiyar rawa ga ƙasata a wannan gasar kofin duniya. Na yi mamaki kuma na ji takaici da wannan hukunci. Ina yi wa ƴan wasan fatan alheri.”

    Mahaifiyar Maguire, Zoe Maguire, ta bayyana rashin jin daɗinta a shafukan sada zumunta, inda ta ce ta “fusata” da wannan hukunci.

    Abokin wasan Maguire a Manchester United, Luke Shaw, shi ma an cire shi duk da ƙwazon da ya yi a kakar nan.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Ronaldo ya cimma burinsa na lashe kofin Saudi Pro League

    Cristiano Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Al-Nassr da tauraron ɗan wasanta Cristiano Ronaldo sun ɗaga kofin gasar ƙungiyoyin Saudiyya na Saudi Pro League.

    A watan Disamban 2022 ne Al-Nassr ta sayi Ronaldo bayan ya bar Manchester United – lamarin da ya girgiza duniyar ƙwallon ƙafa da kuma fito da gasar ƙungiyoyin Saudiyya a idon duniya.

    Sai dai wani babban abin mamakin shi ne yadda ɗan wasan ya kwashe shekara uku a Saudiyya ba tare da lashe babban kofi ba.

    Amma wannan jira ta zo ƙarshe a ranar Alhamis, inda Ronaldo ya ci ƙwallo biyu a karawar da Al-Nassr ta lallasa ƙungiyar Damac da ci 4-1, a wasan ƙarshe na kakar.

    Wannan lamari ya daƙile wa babbar abokiyar hamayyarsu - Al-Hilal - damar lashe kofin.

    Inda wannan ne karon farko da Al-Nassr ta lashe kofin tun daga shekarar 2019.

    Ronaldo wanda a baya-bayan nan ya jefa ƙwallo ta 100 a gasar Saudi Pro League, ya zura ƙwallo 129 a ƙungiyar a dukkanin gasanni – sai dai lashe wannan kofi shi ne babban aikin da ƙungiyar ta ɗauke shi domin ya yi.

  16. Jamus ta gayyaci Neuer gasar kofin duniya duk da ritaya da ya yi a baya, Gasar kofin duniya

    Mai tsaron ragar Bayern Munich, Manuel Neuer, ya dawo daga ritayar, bayan da aka gayyace shi cikin tawagar Jamus da za ta je gasar cin kofin duniya ta 2026, inda koci, Julian Nagelsmann ya bayyana cewa zai yi amfani da ɗan wasan mai shekaru 40 a matakin mai tsaron ragar Jamus a gasar.

    Neuer, wanda ya taimaka wa Bayern ta lashe kofin Bundesliga tare da kai wa wasan kusa da ƙarshe a Champions League a wannan kakar, ya buga wasansa na ƙarshe a Euro 2024, wanda ya yi wa kasar karawa 124.

    Daga baya ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasa wasanni, bayan da ya taimaka wa Jamus ta lashe kofin duniya a 2014 a Brazil.

    Neuer ya buga kofin duniya sau huɗu, kuma yana daga cikin jerin ƴan wasan da shekarunsu suka kai 40 ko fiye da haka da aka zaɓa domin gasar ta bana da za a gudanar a Canada da Mexico da kuma Amurka.

    Sauran ƴan wasan da suka kai shekara 40 ko fiye da haka da za su buga gasar kofin duniya a bana sun haɗa da ɗan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo mai shekaru 41 da na Croatia Luka Modric mai shekaru 40 da mai tsaron raga Scotland, Craig Gordon mai shekaru 43 da da Edin Dzeko na Bosnia-Herzegovina mai shekaru 40.

    Nagelsmann ya gayyaci ƴan wasan Premier League guda biyar a cikin tawagar mutane 26, ciki har da Kai Havertz na Arsenal da Pascal Gross na Brighton da Florian Wirtz na Liverpool tare da masu taka leda a Newcastle United, Malick Thiaw da Nick Woltemade.

    Matashin ɗan wasan Bayern, Lennart Karl mai shekara 18 da kuma mai wasa a Galatasaray, Leroy Sane su ma suna cikin tawagar.

    Jamus, wadda ta lashe kofin duniya sau huɗu, za ta fara wasanta da Curacao ranar 14 ga watan Yuni kafin ta kara da Ivory Coast da Ecuador a sauran wasannin rukuni.

    Tun bayan lashe gasar a 2014, an fitar da Jamus daga matakin rukuni a kofin duniya a 2018 da kuma 2022.

    Tawagar Jamus da za ta buga gasar kofin duniya 2026:

    Masu tsaron raga: Oliver Baumann (Hoffenheim), Manuel Neuer (Bayern Munich), Alexander Nubel (Stuttgart)

    Masu tsaron baya: Waldemar Anton (Borussia Dortmund), Nathaniel Brown (Eintracht Frankfurt), Joshua Kimmich (Bayern Munich), David Raum (RB Leipzig), Antonio Rudiger (Real Madrid), Nico Schlotterbeck (Borussia Dortmund), Jonathan Tah (Bayern Munich), Malick Thiaw (Newcastle United)

    Masu buga tsakiya: Nadiem Amiri (Mainz), Leon Goretzka (Bayern Munich), Pascal Gross (Brighton and Hove Albion), Jamie Leweling (Stuttgart), Jamal Musiala (Bayern Munich), Felix Nmecha (Borussia Dortmund), Aleksandar Pavlovic (Bayern Munich), Angelo Stiller (Stuttgart), Florian Wirtz (Liverpool)

    Masu cin ƙwallaye: Maximilian Beier (Borussia Dortmund), Kai Havertz (Arsenal), Lennart Karl (Bayern Munich), Leroy Sane (Galatasaray), Deniz Undav (Stuttgart), Nick Woltemade (Newcastle United)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Aston Villa ta lashe Europa League na bana, Europa League

    Aston Villa ta lashe Europa League na bana, bayan doke Freiburg 3-0 a ranar Laraba.

    Babban kofin Turai da ta lashe tun bayan European Cup a 1982.

    Da wannan sakamakon, Unai Emery ya shiga cikin fitattun kociyoyin da suka lashe manyan kofunan gasar Turai sau biyar bayan da Aston Villa ta yi nasara a Istanbul.

    Emery yanzu shi ne koci na huɗu da ya lashe manyan kofin gasar zakarun Turai sau biyar, bayan fitattun koci da ya haɗa da ɗan Italiya Giovanni Trapattoni da Carlo Ancelotti, da kuma tsohon kocin Chelsea da Manchester United José Mourinho.

    Ga yadda kowannensu ya cimma wannan bajinta:

    Unai Emery

    Mai shekara 54 ya kara yawan kofunan Europa League da ya lashe zuwa biyar, bayan nasarorin da ya samu da Sevilla a shekarar 2014 da 2015 da kuma 2016, sannan ya ɗauka a Villarreal a 2021.

    Yanzu shi ne koci na biyu kacal da ya lashe kofi iri ɗaya daga gasar zakarun Turai sau biyar ko fiye da haka, bayan Ancelotti. Haka kuma, ya kai wasan karshe a gasar sau shida — inda ya zo na biyu tare da Arsenal a Europa League a 2019 — adadin da ya yi daidai da na Ancelotti da Sir Alex Ferguson da Mourinho, yayin da Trapattoni ne kadai ke gabansa.

    Emery shi ne koci na farko da ya lashe UEFA Cup ko Europa League tare da kungiyoyi uku daban-daban.

    Giovanni Trapattoni

    Tsohon kocin tawagar Italy da Jamhuriyar Ireland, Trapattoni mai shekara 87, ya kai wasan karshe a manyan kofunan zakarun turai Turai sau bakwai — mafi yawa a tarihi — inda ya lashe guda biyar.

    Ya jagoranci Juventus zuwa lashe European Cup a 1985, sannan ya ɗauki Cup Winners Cup a 1984 da UEFA Cup sau biyu a 1977 da 1993 tare da ƙungiyar Turin din.

    Har ila yau, ya lashe UEFA Cup tare da Inter Milan a 1991.

    Sai dai ya sha kashi a wasan karshe a Cup Winners Cup a 1974 a matsayin rikon kwarya a AC Milan a hannun FC Magdeburg, sannan Juventus dinsa ta sha kashi a hannun Hamburger a wasan karshe a European Cup a 1983.

    Carlo Ancelotti

    Kocin tawagar Brazil shi ne kaɗai kocin da ya taba lashe UEFA Champions League sau biyar.

    Ya ɗauki kofin sau biyu tare da AC Milan a 2003 da 2007, sannan sau uku tare da Real Madrid a 2014 da 2022 da kuma 2024.

    Kocin mai shekaru 66 ya kuma kai Milan wasan karshe a Champions League a 2005, inda suka sha kashi a bugun fanareti a hannun Liverpool.

    José Mourinho

    Mourinho mai shekara 63 ya lashe UEFA Cup tare da ƙungiyarsa ta farko FC Porto a 2003, sannan ya kai su ga lashe Champions League a 2004.

    Daga baya ya sake lashe babbar gasar zakarun Turai tare da Inter Milan a 2010.

    Har ila yau, Mourinho ya ɗauki Europa League tare da Manchester United a 2017, sannan ya dauki kofinsa na biyar a Turai, yayin da yake jagorantar AS Roma zuwa lashe kofin farko a UEFA Europa Conference League a 2022.

    Kocin dan Portugal din ya kai wasan karshe a gasar zakarun Turai karo shida a 2023, lokacin da Roma ta sha kashi a bugun fanareti a hannun Sevilla a wasan karshe a Europa League.

  18. Fermin Lopez ba zai buga wa Sifaniya gasar kofin duniya ba, Gasar kofin duniya

    Fermín López ba zai buga wa tawagar Sifaniya gasar gasar kofin duniya ba, bayan da aka yi masa tiyata domin gyaran karayar kafarsa ta dama, kamar yadda ya sanar a shafukan sada zumunta ranar Laraba.

    An yi masa tiyatar ne ranar Litinin, kuma ana sa ran ɗan wasan zai yi jinyar kusan wata uku.

    Fermín mai shekara 23 ya ji raunin ne ranar Lahadi a wasan da Barcelona ta doke Real Betis da ci 3-1 a gasar La Liga.

    Rahotanni sun kuma nuna cewa ɗan wasa, Lamine Yamal ba zai iya buga wasan farko na tawagar Sifaniya a gasar cin kofin duniya ranar 15 ga watan Yuni da Cape Verde a Atlanta.

    Yamal ya ci ƙwallaye shida a wasa 25 da ya bugawa tawagar ƙasarsa.

    Yayin da yake buga wa Barcelona tamaula, Yamal mai shekaru 18 ya ji rauni ne a ƙafarsa ta hagu bayan da ya ci fenariti ranar 22 ga watan Afrilu da Celta Vigo.

    Har yanzu akwai shakku ko zai buga wasan cikin rukuni a karawa ta biyu da Sifaniya za ta yi da Saudi Arabia ranar 21 ga watan Yuni a Atlanta.

    Wasan ƙarshe na Spain a rukuni zai kasance ranar 26 ga watan Yuni da Uruguay a Guadalajara.

    Spain, wadda yanzu ke matsayi na biyu a jadawalin ƙasashen da ke taka leda a duniya, ana sa ran za ta sanar da jerin ƴan wasa ranar Litinin da za su wakilceta a gasar kofin duniya.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  19. , Gasar kofin duniya

    Gwamnatin lardin Ontario ta amince cewa za a tsawaita lokacin rufe mashaya da gidajen abinci masu lasisi a lokacin gasar FIFA World Cup 2026, inda za a ba su damar ci gaba da sayar da barasa har zuwa ƙarfe 4 na safe a wasu lokuta.

    Matakin zai fara aiki daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli — ranar da za a buga wasan karshe na gasar — domin biyan bukatun magoya baya, yayin gasar da za ta gudana a ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka.

    Birnin Toronto zai karɓi wasa shida a filin BMO, ciki har da wasan farko na Kanada da Bosnia a ranar 12 ga watan Yuni.

    A Ontario, yawanci ana rufe sayar da barasa da ƙarfe 2 na safe, amma an riga an yi irin wannan sassauci na wucin gadi a baya, misali lokacin wasannin karshe na hockey tsakanin Canada da Amurka.

  20. Canada za ta kashe makudan kuɗi wajen shirya gasar kofin duniya 2026, Fifa World Cup

    Ana sa ran Canada za ta kashe sama da dala biliyan ɗaya na kudin Canada (kimanin dala miliyan 727 na Amurka) domin karɓar bakuncin gasar FIFA World Cup 2026 a wannan bazarar, kamar yadda wani rahoto daga jami’ar kula da kasafin kudin majalisa ya bayyana ranar Laraba.

    Ofishin Parliamentary Budget Officer ya ce ana hasashen kashe kimanin dala miliyan 82 na kudin Canada a kowane wasa, yana mai cewa wannan ya yi daidai da irin kuɗin da gwamnatoci suka kashe a irin waɗannan manyan abubuwan wasanni a baya.

    Za a buga wasa 13 a Toronto da Vancouver tsakanin 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga Yuli, yayin da Canada ke karbar bakuncin gasar tare da Amurka da Mexico.

    Daga cikin jimillar kuɗin da aka kiyasta na dala biliyan 1.066 na kuɗin Canada, gwamnatin tarayya za ta bayar da dala miliyan 473, yayin da sauran matakan gwamnati za su samar da sauran dala miliyan 593.

    Tun daga watan Afrilu, birnin Toronto ya shirya kashe dala miliyan 380 domin karɓar bakuncin wasa shida, ciki har da tallafin gwamnatin tarayya. Ita ma jihar British Columbia ta tsara kashe dala miliyan 578 domin karɓar bakuncin wasa bakwai a Vancouver.

    A watan Afrilu, gwamnatin Canada ta kuma sanar da ware har zuwa dala miliyan 145 domin tsaro a lokacin wasannin babbar gasar tamaula ta Ingila..

    Tawagar Canada za ta fara wasan farko da Bosnia and Herzegovina a Toronto ranar 12 ga watan Yuni.

    Liv

    Asalin hoton, ge