Ba za mu amince da duk wata yarjejeniya ba sai mun tabbatar za a biya mu diyya - Iran
Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa Iran ba za su amince da kowace yarjejeniya ba har sai sun tabbatar an kare haƙƙin al’ummar kasar gaba ɗaya.
A jawabin da ya yi kafin fara zangon shekara ta uku na majalisar, Qalibaf ya ce sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci shi ne abun da za su yi amfani da shi yana mai jaddada cewa ba za a dogara da kalmomin makiya ba.
Ya kuma ce dole ne majalisa ta guji rikice-rikicen da ke lalata aiki, tare da mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, musamman wajen tabbatar da sakamako mai kyau a fili ga jama’a.
A bangaren dangantakar kasa da kasa, rahotanni daga kafafen yada labarai na Amurka sun ce shugaban Amurka, Donald Trump, ya kara tsaurara sharuɗɗa a sabon daftarin farko na yarjejeniya da Iran, inda aka ce an tura shi zuwa Tehran don nazari.
A gefe guda kuma, sojojin Isra’ila sun ce suna ci gaba da faɗaɗa hare-haren a kudancin Lebanon, abin da ke ƙara tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.