Ƙungiyoyin Championship sun ƙi amincewa a fara mafani da VAR a baɗi, Championship

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyoyin da ke buga Championship gasa mai daraja ta biyu a Ingila, sun kada kuri’a ƙin amincewa da a fara amfani da fasahar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato VAR a baɗi.
Tsarin da aka yi wa lakabi da Football Video Support (FVS) – wani salo ne na VAR da ke amfani da na'urar abinda ya faru ya yin wasa da ake bai wa kowane koci damar neman bitar hukunci har karo biyu a kowace wasa – ana sa ran a iya fara amfani da shi daga watan Agusta. Sai dai kungiyoyin Championship suka yi watsi da shirin.
Hukumar alƙalan gasar ƙwararru, PGMO, ta gabatar da bayani kan tsarin FVS a taron shekara-shekara na EFL a watan da ya gabata.
Bayan haka, EFL ta nemi ra’ayoyin ƙungiyoyi, amma yawancin ƙungiyoyin suna adawa da duk wani nau’i na tsarin nazarin bidiyo a gasar Championship.
A halin yanzu, ana amfani da VAR a gasa mai daraja ta biyu a ƙasashen Spain da Italiya da Jamus. Haka kuma, ana shirin shigo da tsarin a Ligue 2 ta Faransa, amma shirin ya rushe ne bayan durƙushewar yarjejeniyar haƙƙin nuna wasannin a talabijin, sakamakon matsalolin kuɗi.

















