Mutum biyar sun mutu bayan jirgi ya yi hatsari a Amurka

Asalin hoton, Reuters
Wani jirgin dakon kaya na kamfanin Amazon Air ya kauce daga titin saukar jiragen sama yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jiragen sama na Miami International Airport, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyar tare da jikkata wasu biyar da munanan raunuka.
Jirgin dakon kayan ƙirar Boeing 767-300 ya yi hatsarin ne jim kaɗan kafin ƙarfe biyu na rana agogon ƙasar (19:00 agogon GMT), bayan da ya tashi daga filin jirgin sama na Luis Muñoz Marín da ke San Juan, Puerto Rico.
Har ila yau, jirgin ya bugi wasu motoci da ke kusa da wurin da hatsarin ya auku.
Kamfanin Amazon ya ce yana "aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomi da sauran jami'an da abin ya shafa domin gano ainihin abin da ya faru."
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) ta dakatar da duk wani tashin da saukar jirage a filin jirgin saman, yayin da jami'an kashe gobara da na agajin gaggawa suka garzaya wurin da hatsarin ya faru.
Hatsarin ya afku ne a daidai lokacin hutun Ranar Ma'aikata - ɗaya daga cikin lokutan tafiye-tafiye mafi yawan cunkoso a shekara.
Magajin garin gundumar Miami-Dade, Daniella Levine Cava, ta bayyana a wani taron manema labarai da yammacin ranar Lahadi cewa, "Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata."

