Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya a sauran sassan duniya, Juma'a 28/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya a sauran sassan duniya, Juma'a 28/08/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ya kamata a kyautata rayuwar talaka bayan cire tallafin mai - Atiku

    Kusan mako biyu ke nan ana ta ce-ce-ku-ce tun bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana aniyarsa ta cire tallafin man fetur idan ya hau kan mulki a 2027.

    Kamar mutane da dama a Najeriya, Atiku na ganin cewa cire tallafin man fetur shi ne silar matsalolin matsin tattalin arziƙi da al'ummar ƙasar ke ciki.

    "Ana cikin ƙunci, ana cikin rashi da rashin aikin yi, wannan tallafin man fetur da aka janye shi ne babban abin da ya haifar da hakan. Ban taɓa ganin an sha wahala ba a ƙasar nan kamar wannan lokaci," in ji Atiku a tattaunawar da BBC.

    Gwamnatin Najeriya ta mayar wa Atiku martani, inda ta bayyana cewa batun tamkar rashin fahimtar abin da ke faruwa ne da tattalin arziƙin ƙasar.

    Sai dai a tattaunawar da BBC, Atiku ya ce cire tallafin man fetur da zai yi ya dogara ne da halin da ya tsinci ƙasar idan ya kama mulki.

    Atiku ya ce: "Ko za ka cire tallafin man fetur, ba a lokaci ɗaya za ka yi shi ba , kuma sai ka kyautata rayuwar talakawa kafin ka fara cirewa a hankali".

    A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ƙasar.

    Lamarin ya haifar da tashin farashin man fetur nan take, wani abu da ya shafi dukkanin fannonin rayuwa na al'ummar ƙasar.

    Haka nan Najeriya na fama da tashin farashin kayan masarufi, wanda duk ake alaƙantawa da cire tallafin na man fetur.

    Tun farko gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin samar da shirye-shirye da za su sauƙaƙa wa al'ummar ƙasar tsananin rayuwa, to amma sama da shekara uku bayan cire tallafin al'umma da dama a ƙasar na cewa ba su ga wannan tallafi ba.

    Ministan Kuɗin Najeriya, Taiwo Oyedele ya ce an tara jimillar naira tiriliyan 15.8 daga kuɗaɗen tallafin man fetur ɗin tsakanin watan Yunin 2023 da Disamban 2025.

    Ministan ya ce gwamnatin ta kashe kuɗaden ne ta hanyar raba wa jihohi da yin ƙarin albashi da alwus ɗin ma'aikata da biyan basukan da ake bin ƙasar da kuma gudanar da manyan ayyuka.

  2. 'Amurka na yunƙurin mallakar wani kaso na man Venezuela'

    Rahotannin daga kafafen yaɗa labaran Amurka sun ce gwamnatin shugaba Donald Trump na tattaunawa da gwamnatin riƙon ƙwaryar Venezuela kan yiwuwar Washington ta mallaki wani kaso na ɗimbin arzikin man fetur ɗin ƙasar.

    Rahotannin sun ce tattaunawar ta shafi fiye da filayen hako man fetur 12 masu samar da mai, waɗanda ke ɗauke da ganga biliyan 90 na ɗanyen mai, wato kusan kashi ɗaya bisa uku na man da Venezuela ke da shi.

    Kamfanin dillancin labarai na Axios( Acius) ya ce, a ƙarƙashin shirin, kamfanoni masu zaman kansu ciki har da na Amurka za su bunƙasa waɗannan filayen mai, yayin da Venezuela kuma za ta ƙara samun kuɗaɗen shiga daga man.

  3. Tun da na zama gwamnan Kaduna ban karɓi bashin kobo ba - Uba Sani

    Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ba ta karɓi wani sabon bashi ba tun bayan da ya hau mulki a 2023, duk da cewa tana ci gaba da biyan bashin da ta gada daga gwamnatocin baya.

    Uba Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar talabijin ta Channels TV a ranar Alhamis, yayin da yake amsa tambayoyi kan yadda gwamnatinsa ke kashe kuɗaɗe da kuma ƙarin kuɗaɗen shiga da jihar ke samu.

    A cewar gwamnan, a halin yanzu Jihar Kaduna tana ware kimanin naira biliyan 6.7 a kowane wata domin biyan bashin da ta gada daga gwamnatocin da suka gabata.

    “Tun da na zama gwamna, ban karɓi koda kwabo ɗaya na bashi ba,” in ji gwamnan.

    Ya danganta wannan mataki da abin da ya bayyana a matsayin tsantsar kula da harkokin kuɗi cikin hikima da kuma yin taka-tsantsan wajen tsara abubuwan da gwamnati za ta kashe kuɗinta a kansu.

    “Batu ne na yin taka-tsantsan da yin abin da ya kamata, da kuma ta zaɓar wuraren da suka dace a zuba jari cikin kulawa sosai,” in ji shi.

    Gwamna Uba Sani ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori masu yawa, yana mai nuni da ci gaban da aka samu a fannonin noma da ilimi da bunƙasa sana’o’i da kuma tsaro.

    Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin arewacin ƙasar da ke fuskantar matsalolin tsaro, musamman yanbindiga masu garkuwa da mutane.

  4. 'Da mun shirya kai wa Trump hari a Turkiyya ba abin da zai hana mu aiwatarwa'

    Sakataren Majalisar Tsaron Iran, Mohsen Rezaei ya ce Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ne ya kitsa cewa Iran ta yi yunƙurin kashe Trump domin ƙara harzuka shi ya ci gaba da yaƙi da Iran.

    Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta Al-Manar mai watsa shirye-shirye da harshen Larabci, mai alaƙa da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, Mista Rezaei ya ce zarge-zargen da ke cewa Iran ta yi yunƙurin "kashe" Donald Trump a lokacin ziyararsa zuwa Turkiyya, tare da "barazanar" kashe ƙaramin ɗansa, wata makarkashiya ce daga Isra'ila.

    Ya ce Benjamin Netanyahu, ne ya ƙirƙiro wannan shiri domin ya tsoratar da kuma hgarzuƙa shugaba Trump da nufin Amurka ta ci gaba da yaƙi da Iran.

    A cikin bidiyon hirar, wadda kafafafen yaɗa labaran Iran ciki har da kamfanin dillancin labarai na ISNA suka wallafa wasu ɓangarorinta, Rezaei ya ce “Netanyahu ya tsorata Trump ta hanyar yaɗa labaran ƙarya game da wata maƙarkashiyar da Iran ke yi domin kashe shi, lamarin da ya rikita masa tunani kan matakan da zai ɗauka.

    ''Waɗannan bayanai sun razana Trump, inda ya kiɗime har ya koma kamar mai sayar da abinci a motar raba abincin jirage (a yayin bulaguronsa daga Turkiyya).

    Sakataren tsaron ya ce ko kusa ko alama Iran ba ta ƙudiri wannan aniya ba.

    ''In da mun yanke shawarar yin hakan, babu abin da zai hana mu aiwatar da shi. Amma wannan labarin ba komai ba ne illa dabarar yaudara ta Netanyahu.”

  5. Adadin waɗanda suka mutu a ambaliyar Nepal ya kusan 500

    Mahukuntan ƙasar China sun ce masu aikin ceto sun kwashe fiye da mutum 1,000 daga yankunan da ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa suka shafa a kudancin yankin Tibet, bayan mummunar ambaliya da zaftarewar ƙasar da ta afku a ranar Laraba.

    Kafar talabijin ɗin China, ta ce fiye da masu yawon buɗe ido 500 na daga cikin waɗanda aka ceto.

    A arewacin Nepal kuwa, ana ci gaba da neman waɗanda suka tsira cikin dare, yayin da ake ci gaba da fargabar aukuwar wata sabuwar ambaliyar.

    An tabbatar da mutuwar kusan mutum 500 a Nepal, amma har yanzu fiye da mutum 800 ba a san inda suke ba.

    Adadin waɗanda suka mutu da jikkata na ci gaba da ƙaruwa a mummunan bala'in da Nepal ta fuskanta tun bayan girgizar ƙasar da ta afku a shekarar 2015.

    Fiye da rabin waɗannan mutanen dai baƙi ne masu yawon buɗe ido da kuma wadanda suka je ibada.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, hajji babbar rana, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku ci gaba da tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muharawa.