'Amurka ta nemi Rasha ta hana Iran bayanan sirri'

Asalin hoton, Reuters
Majiyoyi masu tushe sun shaida wa kafafen yaɗa labaran Amurka cewa daraktan Hukumar Leken Asirin Amurka (CIA), John Ratcliffe, ya roƙi jami’an leken asirin Rasha kada su bai wa Tehran bayanan da za su iya amfanarta.
Bayanai sun ce yayin wata ziyarar sirri da ya kai Moscow, batun goyon bayan da Rasha ke bai wa Iran na daga cikin muhimman abubuwan da aka tattauna.
Wannan ita ce ziyara ta farko da aka bayyana a fili da wani shugaban CIA ya kai Moscow tun shekarar 2021.
Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa Mista Ratcliffe ya gana da jami’an leken asirin Rasha, amma ba da Shugaba Putin ba.
Baya ga batun Iran, rahotanni sun ce Ratcliffe ya tattauna da jami’an Rasha kan damuwar Amurka game da tsaron ƙasashen ƙungiyar NATO.
Sai dai jami’an Amurka da na Rasha ba su fitar da cikakkun bayanai a hukumance kan abin da aka tattauna ba, yayin da CIA ta ƙi yin tsokaci kan ziyarar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana ziyarar a matsayin irin ta yau da kullum, yana mai cewa irin waɗannan tattaunawa na iya taimakawa wajen ciyar da wasu batutuwa gaba, ciki har da kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Sai dai bai bayar da cikakken bayani kan tattaunawar da aka yi da Rasha ba.
A cikin watannin baya-bayan nan, an sha samun rahotannin da ke magana kan taimakon da hukumomin leƙen asiri na China da Rasha suka bai wa Iran a lokacin yaƙinta da Amurka da Isra’ila.
A nata ɓangaren, Moscow ta sha zargin Washington da ƙawayenta na Turai da bai wa Ukraine taimakon leƙen asiri, tare da yin kira ga Amurka ta dakatar da irin wannan taimako.




















