KAI TSAYE, Champions League final: Havertz gives Arsenal early lead over holders PSG

Takaitaccen Bayanin Wasa

UEFA Champions League -
Final
Paris Saint-Germain 0 , Arsenal 0
Paris Saint-Germain
Arsenal
7 minutes , in progress

Key Events

Paris Saint-Germain

    Arsenal

    • K. HavertzGoal 6 minutes
    Venue:Puskás Aréna

    Taƙaitattu

    Rahoto kai-tsaye

    Mohammed Abdu

    1. An take leda kudi ya mutu, Paris St-Germain 0-0 Arsenal

      An fara wasan tsakanin Arsenal da Paris St Germain, Arsenal da jan riga da farin wanda da jar safa, PSG kuwa tana da riga da wanda da safa duk ruwan bula.

    2. An kammala taken Champions League, Paris St-Germain v Arsenal

      Tuni yan wasa na gaisawa da juna kuma filin wasa ya cika da yan kallo a wasan da za a kafa tarihi, ko PSG za ta lashe na biyu a jere ko kuma Gunners za ta dauka a karon farko a tarihi.

    3. Yan wasa na daf da fitowa fili, Paris St-Germain v Arsenal

      An fito da katafaren kofin Champions League cikin fili, yanzu yan wasa sun fara fitowa da shirin fara wasan da kowa ke jira.

      Wannan shi ne karo na takwas da za su kece raini bayan kowacce ta yi nasara biyu da canjaras uku.

    4. Dabarun da Arsenal za ta iya amfani da su ta lashe Champions League

      Arsenal da koci Mikel Arteta na fatan ƙara ɗaukar kofi mai suna Champions League a karon farko, bayan lashe Premier League, inda za ta kara da Paris St Germain a wasan karshe ranar Asabar.

      Arsenal ta yi fice a wasannin Turai ta hanyar mallakar ƙwallo da bani in baka da kuma rage damar bai wa abokan hamayya sararin cin ƙwallo. Hakan ya taimaka mata wajen yin wasa ba tare da ƙwallo ta shiga ragarta ba, mafi yawa a gasar kenan.

      A gefe guda, PSG ta fi kowace kungiya cin ƙwallaye a wannan kakar a Champions League, inda ta zura 44 a raga, yayin da Arsenal ke da 29.

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    5. Champions League: Damar da PSG ke da ita a kan Arsenal

      Da alama babu wani abu da ya fi ƙayatarwa a ƙarshen wannan kakar kamar karawar da za a yi tsakanin ƙungiyoyin Ingila da Faransa a wasan ƙarshe na gasar Champions League, bayan shafe tsawon kakar ana gwagwagwa.

      Ƙayataccen wasan da zai gudana a filin wasa na Puskas Arena da ke birnin Budapest na ƙasar Hungary, shi ne karawa ta 63 da Arsenal za ta yi a wannan kaka, wadda ta fara kakar da nufin lashe kofuna huɗu rigis, har sai zuwa farkon watan Afrilu inda ta tabbatar hakan ba zai yiwu ba.

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    6. Yan ƙwallon PSG 11 da za a fara wasan da su

      Liv

      Asalin hoton, BBC Sport

    7. Yan wasan Arsenal 11 da za a fara karawar da su

      Liv

      Asalin hoton, BBC Sport

    8. Wazai lashe Champions League, Za ku iya kada zaben wadda za ta lashe kofin kafin a tashi

    9. Sauran kasa da minti 30 a take leda

      Liv

      Asalin hoton, Reuters

      Liv

      Asalin hoton, Reuters

      Liv

      Asalin hoton, Reuters

    10. Tuni dai ya shiga kundin tarihi

      Kocin Paris Saint-Germain, Luis Enrique, ya gargadi Arsenal cewa ƙwazon da ƙungiyarsa ke da shi na kare kambun Champions League ya fi ƙarfin burin Gunners na lashe kofin a karon farko.

      PSG na neman zama ƙungiya ta biyu kacal a zamanin Champions League na zamani da za ta iya kare kambunta cikin nasara, bayan Real Madrid wadda ta lashe kofin sau uku a jere tsakanin 2016 da 2018.

      A kakar da ta gabata, PSG ta doke Arsenal a wasannin gida da waje a zagayen kusa da na ƙarshe, kafin daga bisani ta murƙushe Inter Milan da ci 5-0 a wasan ƙarshe, inda ta lashe kofin Champions League na farko a tarihinta.

      Yanzu Arsenal ce ke fuskantar irin wannan ƙalubale, yayin da take neman lashe kofin zakarun Turai karo na farko a tarihinta.

      Wannan ne wasan ƙarshe na biyu da Arsenal za ta buga a gasar, bayan ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Barcelona a wasan ƙarshe a shekarar 2006 da aka buga a birnin Paris.

      Saboda haka, wasan ƙarshe na bana zai kasance babban gwaji tsakanin PSG mai neman ci gaba da mulki a Turai da kuma Arsenal mai neman rubuta sabon tarihi.

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    11. Yadda Arsenal ta kai wasan karshe

      Karawar cikin rukuni

      • 2-0 Athletic Club (waje)
      • 2-0 Olympiacos (gida)
      • 4-0 Atletico Madrid (gida)
      • 3-0 Slavia Prague (waje)
      • 3-1 Bayern Munich (gida)
      • 3-0 Club Brugge (waje)
      • 3-1 Inter Milan (waje)
      • 3-2 Kairat (gida)

      Yan 16: 3-1 gida da waje da ta doke Bayer Leverkusen (1-1, 2-0)

      Kwata fainal: 1-0 gida da waje da ta yi nasara a kan Sporting (1-0, 0-0)

      Daf da karshe: 2-1 gida da waje da ta fitar da Atletico Madrid (1-1, 1-0)

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    12. Yadda PSG ta kai wasan karshe a Champions League

      Daga karawar cikin rukuni

      • 4-0 Atalanta (gida)
      • 2-1 Barcelona (waje)
      • 7-2 Bayer Leverkusen (waje)
      • 1-2 Bayern Munich (gida)
      • 5-3 Tottenham (gida)
      • 0-0 Athletic Club (waje)
      • 1-2 Sporting (waje)
      • 1-1 Newcastle (gida)

      Cike gurbi: ta ci 5-4 gida da waje a wasa da Monaco (3-2, 2-2)

      Yan 16: 8-2 gida da waje ta doke Chelsea (5-2, 3-0)

      kwata fainal: 4-0 gida da waje ta yi wa Liverpool (2-0, 2-0)

      Daf da karshe: 6-5 gida da waje ta fitar da Bayern Munich (5-4, 1-1)

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    13. Barkanmu da zuwa Budapest

      LIV

      Asalin hoton, Getty Images

      lIV

      Asalin hoton, Getty Images

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    14. Magoya baya sun taru a filin Emirates

      Liv

      Asalin hoton, Reuters

      Liv

      Asalin hoton, Reuters

      Liv

      Asalin hoton, Reuters

    15. Tarihin lashe European da Champions League daga Burtaniya

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

      A tarihin gasar European Cup da kuma UEFA Champions League, kungiyoyin Birtaniya sun lashe kofin har sau 16.

      Celtic ce ta fara kafa tarihi, bayan ta doke Inter Milan da ci 2-1 a wasan ƙarshe na kakar 1966-67.

      Shekara guda bayan haka, Manchester United ta zama kungiyar Ingila ta farko da ta lashe wannan babbar gasa ta Turai.

      Kungiyoyin Birtaniya da suka lashe kofin:

      • Celtic – 1967
      • Manchester United – 1968, 1999, 2008
      • Liverpool – 1977, 1978, 1981, 1984, 2005, 2019
      • Nottingham Forest – 1979, 1980
      • Aston Villa – 1982
      • Chelsea – 2012, 2021
      • Manchester City – 2023

      Yanzu kuma Arsenal na da damar shiga cikin wannan jerin masu daraja idan ta doke Paris Saint-Germain a wasan ƙarshe na Champions League 2026.

      Idan Arsenal ta yi nasara, za ta zama kungiyar Ingila ta bakwai da ta taba lashe kofin zakarun Turai.

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    16. Barkanmu da kasancewa

      BBC Hausa zai kawo muku wasan karshe tsakanin Paris St Germain da Arsenal a Champions League ranar Asanar 30 ga watan Mayu.

      Sunana Mohammed Abdu zan kasance tare da ku, za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook.

      Live

      Asalin hoton, Getty Images

    17. Ga Premier League ga Champions League

      Wannan na iya zama kaka mafi girma a tarihin Arsenal.

      Bayan shekara 22 suna jiran dawowar kofin gasar Ingila, a ƙarshe Arsenal ta sake zama zakarar Premier League, kuma yanzu tana da damar cimma wani abin tarihi da ba ta taɓa yi ba a rayuwarta.

      Kungiyar ta Landan na daf da zama zakarar Turai a karon farko idan ta samu nasara a wasan ƙarshe a UEFA Champions League Final.

      Sai dai akwai babban ƙalubale a gabanta. Mai rike da kambun gasar, Paris Saint-Germain (PSG), ita ce ke tsaye a hanyarta.

      Za a buga wannan babban filin Puskas Arena da ke birnin Budapest na ƙasar Hungary.

      Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    18. Liv

      Asalin hoton, Getty Images

    19. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

      Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu kawo muku wasan karshe a Champions League tsakanin Paris St Germain da Arsenal ranar Asabar 30 ga watan Mayun 2026.

      Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.