Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya
Wannan shafi na kawo muku sahihan bayanai dangane da wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 15/04/2026
Buhari Muhammad Fagge, Muslim Muhammad Yusuf da Haruna Kakangi
'Hare-haren Isra'ila ya kashe ma'aikatan jinya 3 a Lebanon'
Asalin hoton, Getty Images
Jami’an gwamnatin Lebanon sun ce jerin hare-hare uku da Israel ta kai sun kashe akalla ma’aikatan jinya 3, ciki har da wani da aka nuna a wani rahoton BBC.
Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce an kai harin ne kan wata tawagar masu aikin ceto, yayin da suke kokarin taimakawa mutane a wurin da aka kai harin Isra’ila a garin May-fa-doon.
A cewar wakilin BBC, lokacin da wata tawagar masu aikin ceto ta 2 da ta 3 suka isa wurin domin taimakawa, su ma an kai musu hari.
Daga cikin wadanda suka mutu har da Faa-dil Ser-kaar, wanda BBC ta shafe kwanaki tana tare da shi a farkon wannan wata, yayin da tawagarsa ke aiki a wani tanti na wucin gadi.
Jami’an Lebanon sun zargi Isra’ila da kai hare-hare da gangan kan ma’aikatan lafiya.
Sai dai Sojojin Isra’ilar ba su mayar da martani ba.
Isra'ila ta shirya wa kowane irin yanayi - Netanyahu
Asalin hoton, @netanyahu via X
Firaminitan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa ta shriya wa fuskantar kowane irin yanayi a yaƙin da take yi da Iran da Lebanon.
A wani saƙon bidiyo, Netanyahu ya Isra'ila tana kan lalata ɗaya daga cikin manyan sansanonin Hezbollah a kudancin Lebanon.
Firaministan Isra'ila ya ce ya buƙaci sojojin da su "ci gaba da tsaron yankin" a tare da fadaɗa shi zuwa gabas.
Ya ƙara da cewa manufofin Isra'ila sun yi daidai da na Amurka.
Tattaunawa tsakanin Amurka da Iran na tafiya yadda ya kamata - Fadar White House
Asalin hoton, Getty Images
Fadar White House ta ce tattaunawar tsawaita yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta tsakanin Amurka da Iran na tafiya yadda ya kamata.
Ta ce ana samun ci gaba, awanni kadan bayan isowar masu shiga tsakani daga Pakistan a birnin Tehran.
Wakiliyar BBC ta ce gwamatin Trump na son tattaunawar ta ci gaba ta hannun Pakistan da ta shiga tsakani.
Mai magana da yawun Shugaban Amurka, Karoline Leavitt, ta shaida wa manema labarai cewa, ba a sanya wa’adin lokacin fara tattaunawa kai tsaye ido-da-ido domin kawo karshen yakin ba, amma ta ce akwai yiwuwar a gudanar da irin wadannan tattaunawa a kasar Pakistan.
A halin yanzu, wata babbar tawaga daga Pakistan karkashin jagorancin babban hafsan sojin kasar, Asim Munir, na birnin Tehran a wani bangare na kokarin Islamabad na sasanta rikicin.
Amurka ta sake ƙaƙaba sabbin takunkumai kan Iran
Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Ma'aikatar kuɗi ta Amurka ta sanar da ƙaƙaba wasu sabbin takunkumai kan ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da kuma jiragen ruwa masu alaƙa da Iran.
Cikin takunkumin akwai mutane uku, jiragen ruwa tara, da kuma hukumomi 17, kamar yadda ofishin Baitulmalin ya sanar a shafinsa.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da sakataren Baitulmalin ƙasar Scott Bessent ya bayar, cewa Amurka ba za ta sake ɗaga ƙafa kan takunkumin da ta ƙaƙaba ma Iran na sayen manta da na Rasha ba.
Wannan ce takarata ta ƙarshe - Atiku
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya ce ba zai sake neman takarar shugaban ƙasar daga 2027 ba.
Ya ce idan aka yi la'akari da shekarunsa da kuma damar da yake da ita ba lallai ya ci gaba da neman damar daga shekara mai zuwa ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Laraba.
Da aka tambaye shi game da cikarsa shekaru 80 a shekarar 2027 da yadda hakan zai iya daƙile masa damarsa, Atiku ya ce: "Tabbas za a samu ƙarin masu nema, kuma ita ce dama ta ƙarshe da zan fito takarar"
Atiku ya yi takarar shugaban ƙasar a lokuta da dama.
Ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 1993 a karkashin jam’iyyar SDP inda daga baya ya bar wa Moshood Abiola, da kuma Action Congress a shekarar 2007, inda marigayi Umaru Musa Yar'Adua ya lashe zaɓen.
Atiku ya kuma tsaya takara a shekarar 2011 karkashin jam’iyyar ACN, inda ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ya koma jam’iyyar PDP ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019, inda ya sha kaye a hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A 2023, ya sake fitowa takarar a PDP amma ya sha kaye a hannun Shugaba Bola Tinubu na APC.
Kafar yaɗa labarai ta BBC za ta rage ma'aikata
Asalin hoton, Getty Images
Kafar yaɗa labaran Birtaniya BBC za ta rage yawan ma'aikatanta kusan 2,000 cikin shekaru uku masu zuwa.
A cewar muƙaddashin shugaban BBC, Rhodri Talfan Davies, za a ɗauki matakin ne saboda matsin tattalin arziki kuma hakan zai sa a rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa da kusan dala miliyan 700.
Yawanci BBC dai na samu kuɗaɗen shiga ne daga laisisin samun shirye-shirye da ƴan ƙasar Birtaniya ke biya.
Duk da yake kusan kashi 90 na biya, amma adadin na raguwa.
"Akwai bukatar mu yi nazari kan komai, kuma a batun rage fam miliyan £500m babu makawa zai a yanke wasu manyan hukunce-hukunce masu wahala, amma akwai bukatar mu bi matakin a hankali," kamar yadda Mr. Davies ya shaida wa BBC Radio 4.
Ya ce zai yi ƙarin bayani nan gaba a wannan shekara kan yadda tsarin zai kasance. BBC tana da kusan ma'aikata 21,500.
A halin yanzu BBC na tattaunawa da gwamnati game da makomarta, da kuma na kudin lasisi, gabanin sabunta yarjejeniya a karshen shekarar 2027.
An ceto rayuka mutum miliyan 20 a Afirka ta hanyar rigakafin ƙyanda
Asalin hoton, Getty Images
Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar ya bayyana cewa allurar rigakafin ƙyanda na yara da ake yi ya ceci rayukan kusan mutum miliyan 20 a Afrika cikin shekaru 25 na ƙarnin da ya gabata.
Alkaluman da aka tattara tare da haɗin gwiwar shirin rigakafin GAVI, sun nuna adadin mutuwar da ake samu sakamakon cutar kyanda ya ragu a tsawon wancan lokacin.
Kasashen Cape Verde da Mauritius da Seychelles a bara sun zama kasashe na farko a yankin kudu da hamadar Sahara da suka kawar da cutar gaba daya.
Ci gaban da aka samu ya ƙara bayyana ƙoƙarin da ake yi na faɗaɗa shirye-shiryen rigakafin yara ciki har da na cututtuka kamar ciwon sanƙarau da zazzaɓin cizon sauro.
Amma masana sun yi gargaɗin cewa hallau akwai ƙalubale saboda har yanzu miliyoyin yara ba su samu allurar kariya daga cutar ba..
Fafaroma Leo ya isa Kamaru domin ziyara
Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Leo ya isa Kamaru, a rana ta biyu ta balaguron da yake yi a nahiyar Afrika, bayan ya bar Aljeriya.
Ana sa ran zai gana da shugaban ƙasar Paul Biya, inda zai tattauna da manyan malaman ɗariƙar Katolika
Zai kai ziyara Bamenda a ranar Alhamis, inda aka shafe kusan shekara 10 ana rikici tsakanin masu tada ƙayar baya da ke neman ɓallewa daga ƙasar.
Ana hasashen zan yi huɗubar muhimmancin zaman lafiya tare da fahimtar juna.
Masu tada ƙayar bayan dai sun ayyana tsagaita wuta na tsawon kwanaki uku saboda ziyarar ta sa.
Yaƙin Iran ya ingiza hauhawar farashin kaya a Najeriya cikin watan Maris
Asalin hoton, Getty Images
Hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru sosai a watan Maris a karon farko cikin wannan shekara, kamar yadda alƙaluma daga hukumar ƙididiga ta ƙasar suka nuna.
Ana ganin lamarin zai ƙara haifar da cikas ga gwamnatin ƙasar ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓukan 2027 a watan Junairun baɗi.
Ƙasar wadda ta fi kowace ƙasa yawan al'umma a Afrika na ta ƙokarin rage hauhawar farashi kafin a fara yaƙin Iran, inda gwamnatin ke ta ɗaukar matakai da dama a cikin watanni 11 da suka gabata.
Sai dai yaƙin Gabas ta Tsakiya ya mayar da hannun agogo baya musamman sakamakon tashin farashin man fetur, inda ya shafi farashin kayan masarufi.
Hukumar NBS a ƙasar ta ce hauhawar farashi ta ƙaru daga 15.06% a watan Fabrairu zuwa 15.38% a watan Maris.
Hauhawar farashin kayan abinci kuma ta ƙaru daga 12.12% zuwa 14.31%
Wasu al'ummar ƙasar sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa hauhawar farashin da ake samu a Najeriya na ƙara jefa rayuwarsu cikin matsi da ƙunci.
Jamus na karbar bakuncin wani taron kasa da kasa kan yaƙin Sudan
Jamus na karbar bakuncin wani taron kasa da kasa na masu bayar da tallafi domin taimakawa Sudan, yayin da mummunan yakin basasar kasar ke shiga shekara ta 3.
Gwamnatin Jamus na fatan tara sama da dala biliyan 1 a matsayin tallafi a taron da ake yi a birnin Berlin, a wani bangare na kokarin tallafa wa samun mafita ta siyasa ga rikicin.
Rahotanni sun ce fargaba rashin kayan jinkai na ƙaruwa, yayinda aka ƙatse kafasin tallfin kasa da kasa, a daidai lokacin da aiyukan cin zarafi ke ƙaruwa.
Miliyoyin ‘yan Sudan sun rasa matsugunansu sakamakon yakin da ake tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun RSF.
Tattalin arzikin kasar ya durkushe, yayin da mafi yawan al’ummar kasar ke cikin tsananin bukatar abinci da ruwa da matsuguni da kuma magunguna.
Sai dai gwamnatin sojin Sudan ta soki taron na Jamus, tana mai cewa katsalandan ne, inda ta ce an shirya shi ba tare da tuntubarta ba.
Rundunar sojin Najeriya ta musanta tura tubabbun Boko Haram yaƙi
Asalin hoton, Boko Haram
Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ake yi cewa ana bai wa tsofaffin mayaƙan Boko Haram makamai tare da tura su zuwa fagen daga a karkashin shirin gyaran hali.
Mai kula da shirin, Birgediya Janar Yusuf Ali, ya ce zarge-zargen ba gaskiya ba ne, bayan wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna wasu tsofaffin mayaƙa, suna fafatawa tare da dakarun soji.
Ya ce mutanen da aka gani a cikin faifan bidiyon ba su da wata alaka da shirin, sannan wurin da aka nuna ba ya ɗaya daga cikin cibiyoyin shirin.
Ƙungiyar Boko Haram dai ta shafe fiye da shekara 10 tana kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda ta kashe dubban mutane.
An cire ɗaukar nauyin ta'addaci cikin zargin da ake wa Malami
Gwamnatin Tarayya ta sauya zarge-zargen da ta ke yi wa tsohon Ministan Shari'ar ƙasar Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdul'aziz inda aka cir zargin ɗaukar nauyin ta'addanci ciki.
A zaman kotun da aka yi a ranar Laraba, Akinlolu Kahinde wakilin hukumar farin kaya ta Naeriya DSS ne ya sanar da kotu kan sauya zargin da ake yi wa Malamin, kuma ya sa aka maye zargin da wani.
Cikin sauyin da aka samu har da cire zargin mallakar makamai.
Shu'aibu Aruwa, mai kare Malami, ya tabbatar da wanda yake karewa ya amince da cire tuhumar tare da sauya ta da wasu wanda aka karanto.
Dama tun lokacin da aka karanta masa tuhumar a baya, ya musanta zargin.
Yanzu an sake ɗage zaman kotun zuwa ranar 26 ga watan Mayu da kuma 15 ga watan Yuni domin ci gaba da saurare.
Wakilan Pakistan sun isa Iran kan maganar sasanci da Amurka
Asalin hoton, Gwamnatin Pakistan
Wata tawaga ta musamman daga Pakistan ta isa birnin Tehran domin ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran.
Tawagar na ƙarƙashin jagorancin babban hafsan sojin Pakistan, Asim Munir.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce ana ci gaba da musayar saƙonni tsakanin Washington da Tehran ta hannun Pakistan da ke shiga tsakani.
Sabuwar tattaunawar na zuwa ne bayan an gaza cimma matsaya a zaman sasancin da aka yi a Islamabad a makon da ya gabata.
Akwai rahotannin da ke cewa za a fara tattaunawa a karo na biyu a Pakistan nan da kwanaki kaɗan.
An binne Birgediya Janar Braimah da sauran sojojin da Boko Haram ta kashe a Borno
Asalin hoton, FB/Nigerian Army
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa an binne ɗaya daga cikin manyan jami'anta Birgediya Janar Omo Braimah da sauran sojojin da mayaƙan Boko Haram suka kashe a wani harin da suka kai kan sansanin soji a jihar Borno.
Braimah, wanda shi ne kwamandan ƙaramar rundunar sojin Najeriya ta 29 Join Task Force Brigade da ke aiki ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai, ya rasa ransa ne a samamen da mayaƙan na Boko Haram suka kai kan sansaninsu da ke garin Benisheikh na yankin ƙaramar hukumar Kaga.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na facebook, rundunar sojin Najeriya ta ce a yau Laraba 15 ga watan Afrilu ne aka binne Braimah, da kyaftin Ismail da kuma sauran sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu a bakin aiki.
An gudanar da jana'zar ne a barikin Maimalari da ke jihar Borno, gaban iyalai da ƴan'uwan mamatan.
Cikin waɗanda suka halarci binne mamatan akwai gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, da ministan tsaro na Najeriya Christopher Musa da babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya da kuma mutane da dama.
Asalin hoton, FB/Nigerian Army
Najeriya na ci gaba da fuskantar ƙalubalai daga ƙungiyar Boko Haram wadda a baya-bayan nan ta ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare kan cibiyoyin soji da kuma fararen hula a arewa maso gabashin ƙasar.
Ko a ranar Litinin ɗin wannan mako rundunar sojin ta sanar da mutuwar ɗaya daga cikin kwamandojinta yayin wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai kan dakarunta a ƙaramar hukumar Monguno da ke jihar ta Borno.
Asalin hoton, FB/Nigerian Army
Boko Haram ta shafe sama da shekara 15 tana ƙaddamar da hare-hare a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar rayukan dubban mutane da raba miliyoyi da muhallansu.
Hukumomi a Najeriya na ci gaba da iƙirarin samun nasara kan ƙungiyar, sai dai har yanzu matsalar na ci gaba da haifar da asarar rayuka da dukiya.
Dan wasan Barcelona na gaba Raphinya ya ce fitar da ƙungiyarsa da aka yi daga Champion Lig, "fashi aka yi wa Barcelona".
A duka wasanni biyun da suka buga na gida da waje an korar mata ɗan wasa daya, waɗanda abokiyar hamayyarta Atletico Madrid ta ci ta 3-2 gida da waje.
A wasan farko an ci Barceola har gida 2-0, yayin da a wasa na biyu Barcelonan ta ci 1-2, amma duk da haka an cire ta.
A duka wasannin sai da aka fara katin gargaɗi sa'annan daga baya a bayar da jan kati, bayan duba na'urar da ke taimakawa alƙalin wasa.
Raphina bai buga duka wasannin ba sakamakon raunin da ya ji: "a wajena fashi ne wannan wasan. Ba wai wannan ba har wanda aka fara".
"Alƙalin wasan bai iya komai ba, hukuncin da ya yi ba wanda hankali zai ɗauka ba ne.
"Ban san duka nawa Atletico suka yi wa 'yan Barcelona ba, amma alƙalin wasan bai basu ko katin gargaɗi ɗaya ba.
"Ban san tsoron me suke ji ba idan Barcelona ta yi nasara."
Matasa sun kai kaso 60 na 'yan kwayar da muka kama a shekara 5 - Marwa
Asalin hoton, Marwa X
Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA Buba Marwa ya ce sama da kashi 60 na masu ta'ammali da miyagun kwayoyi da suka kama cikin shekaru biyar da suka ggabata matasa ne.
Adadin mutanen da aka kama ya kai 77,859, wanda haka ke nuni da ta'azzarar ta'ammali miyagun kwayoyi tsakanin matasa.
Marwa ya bayyana hakan ne a yayin gudanar da maƙala kaso na 29 zuwa 30 a jami'ar Abuja, wadda ta zama Jami'ar Yakubu Gowon, kamar yadda sanarwar da Femi Babafemi daraktan yaɗa labaran hukumar ya fitar.
Ya gargaɗi matasan Najeriya musamman waɗanda suke makarantun gaba da sakandire, saboda shaye-shayen yana kassara rayuwar matasan Najeriya da ya kamata su zama masu amfani ga ƙasar.
Ya ce harkar shaye-shaye ta bar kan titunan Najeriya ta koma cikin makarantu.
An buɗe mashigar Hormuz kuma jirage na wucewa - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Kamar yadda muka rawaito cewa, Sojojin Iran sun yi wa jiragen ruwan yankin Gulf da Bahar Maliya, da Tekun Oman idan Amurka ta ci gaba da toshe tashoshin ruwan Iran.
A ranar Litinin ne Amurka ta ƙaddamar da shirinta na tsoshe tashoshin, a wani ƙarin haske da Amurka ta yi ta ce cikin awa 24 babu wani jirgi da ya wuce ta mashigar.
A wata tattaunawa da gidan talabijin na Fox, wadda aka naɗa gabanin barazanar ta Iran, Shugaban Amurka Trump yace an buɗe mashigar ta Hormuz kuma jiragen ruwa na dawowa, amma bai yi ƙarin bayani ba.
A Iran, Trump ya ce "ba mu kammala ba", amma ya ƙara da cewa yana ganin "yaƙi zai faru a kusa" kuma Amurka za ta so tattaunawa kan hakan da Iran.
ADC ta kori Nafi'u Bala Gombe daga jam'iyyar
Asalin hoton, Nafi'u Bala Facebook
Jam'iyyar adawa ta ADC ta kori tsohon maitaimakin jam'iyyar na ƙasa mai iƙirarin shugabancin Jam'iyyar Nafi'u Bala Gombe da wani mamba na jam'iyyar Leke Abejide. Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a yayin taronta na ƙasa da ta gudanar.
An kori Nafi'u Gombe ne dalilin "yi wa jam'iyya zagon ƙasa", kamar yadda Faisal Kabiru ɗaya daga cikin masu magana da jam'iyyar ya shaida wa BBC Hausa, wanda hakan ya jefe jam'iyyar cikin mawuyacin hali.
An kori nafi'u Gombe tare da wasu da suka haɗa da Kenneth Ehiator daga Abia wanda shi ma yake iƙirarin shugabancin jam'iyya a jihar, da Stella Chukwu da kuma Elias Adiukwu.
Nafi'u da ya dage kan zama shugaban jam'iyyar ya fitar da sanarwar waɗanda suka shiga jam'iyyar su Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso ba halastattun 'yan jam'iyya ba ne, saboda sun shiga ba ta hannunsa ba, kazalika katin 'yan jam'iyyarsu a shi da wani amfani.
Ya kuma jagoranci zanga-zangar da aka yi a Abuja, wadda ta mayar da hankali wajen neman hukumar zaɓe INEC ta yarda da shi a matsayin halastaccen shugaban ADC.
A babban taron da jam'iyyar ta gudanar na ƙasa, an amince da David Mark a matsayin shugaban ADC na ƙasa da Rauf Aregbesola a matsayin sakatare da dai sauransu.
Idan ba a manta ba, a wani taron manema labarai da ADC ta yi ta nemi Shugaban INEC ya sauka da muƙaminsa saboda cire sunan Sanata David Mark daga shugaban jam'iyyar da sauran muƙarrabansa.
Isra'ila tace tana kai hari da iyaka ƙarfinta a kudancin Lebanon
Asalin hoton, Reuters
Hukumar Dakarun tsaron Isra'ila ta ba ba da sanarwar mutane sun ƙauracewa yankin kudancin Lebanon inda tace "tana kai hare-harenta na sama a yanzu".
Hukumar tace ana kai harin ne da ƙurewar ƙarfi a yankin kudancin tekun Zahrani, kuma akwai buƙatar mutane su fice daga wajen cikin gaggawa su nufi yankin arewaci.
"Dun wani wanda a yanzu yake zaune a yankin da yake kusa da abubuwan Hezoullah, yana sanya rayuwarsa ne cikin haɗari," kamar yadda sanarwar ta ambato.
Ba a gane unguwannin Tehran, in ji wata mai aikin agani
Asalin hoton, Getty Images
Martje van Raamsdonk ya daɗe a Iran tare da hukumar ba da agaji ta Norwegian Refugee Council (NRC) - tun watan November.
NRC na daga cikin ƙungiyoyin agajin da ba su da yawa a cikin Iran kuma Martje ta shaida wa BBC yadda ta shaida ɓarnar da wannan rikici a ya yi a Tehran babban birnin Iran.
"Kusan kullum sai sun wurga bam cikin yankin da ke da cunkoson fararen hula a nan Tehran, wanda babban birni ne mai ɗauke da mutane sama da miliyan 10, an lalata gine-gine da yawa sannan ba ma a gane gine-ginen da ke makwabtaka," in ji ta.
"Abokiyar aikina ta bayyana wani labarin da ta gani mai taɓa zuciya. Suna zaune ne a yankin Tehran a garin Isfahan suna kusa da inda ake kai hare-haren, inda makami mai linzami ke faɗawa.
"Ƙarar fashewar kullum na girgiza tagoginsu da ƙofofinsu da gine-ginesu kuma hakan na tasiri kan rayuwarsu."