Za mu biya diyya daga kuɗaɗen Iran dake hannunmu - Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya sake bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da kuɗaɗen Iran da suke ƙarƙashin ikon Amurka wajen biyan diyya da kuma gyaran ɓarnar da ya ce ta faru sakamakon yaƙin baya-bayan nan.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da ƴan jarida a cikin jirginsa, inda ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen na Iran wajen biyan wasu daga cikin asarar da aka samu.
Haka kuma shugaban Amurkan ya yi watsi da damuwar da ake nunawa cewa Amurka na iya fuskantar ƙarancin makamai bayan shafe kusan watanni biyar tana kai hare-hare kan Iran.
Ya ce Amurka tana da tarin makamai da za su iya ci gaba da gudanar da duk wani aiki na soji idan buƙatar hakan ta taso.
Trump ya ce, "Muna da makamai masu yawa iri-iri," inda ya ƙara da cewa ƙasar tana da isassun makamai fiye da abin da za ta iya amfani da shi a kowane yanayi.