KAI TSAYE , Sakamakon zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka da sauran abubuwan da ke faruwa a duniya, Laraba 04/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 04/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. A shirye nake na yi aiki da Demokrats - Trump

    Trump

    Yayin da ƴan takarar jam'iyyar Democrat ke ci gaba da samun nasara a zaɓukan tsakiyar wa'adin mulkin Amurka, Shugaba Donald Trump ya ce zai karɓi tsakamakon zaɓen.

    Cikin wata hira da Jaridar New York Times, Shugaba Trump ya ce a shirye yake "ya amince da wannan sakamakon", kuma yana shirye ya yi aiki tare da jam'iyyar adawa.

    "Gaskiya, muna sa ran yin aiki tare da su," in ji shi.

    "Mai yiwuwa mu cimma wata matsaya tare."

  2. Ministan sufurin Sifaniya ya ajiye muƙaminsa ya kuma haƙura da takara saboda hatsarin jirgin ƙasa

    Ministan sufurin Sifaniya

    Ministan Sufuri na Spain, Óscar Puente, ya yi murabus, kwanaki shida bayan hatsarin jiragen ƙasa wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 69 tare da jikkata wasu da dama.

    Ya sanar da matakin nasa a Majalisar Dokoki, bayan ya bayar da bahasi kan bala'in da ya faru a ranar Larabar da ta gabata kusa da garin Urda, da ke kudancin babban birnin ƙasar, Madrid, inda wani jirgin ƙasa ya buga bayan wani jirgin da ke tsaye.

    "Wani ministan sufuri a ƙasa irin Spain ba zai iya ci gaba da zama a muƙaminsa ba bayan hatsari biyu masu muni cikin ƙasa da shekara guda," in ji shi, yana mai nuni da hatsarin da ya faru a watan Janairu a kan wannan layin dogo, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 46.

    jiragen da suka yi hatsari

    Hatsarin da ya faru a makon da ya gabata na ɗaya daga cikin munanan bala'o'in jirgin ƙasa mafi muni a tarihin Turai a wannan zamani, kuma shi ne mafi munin hatsarin jirgin ƙasa a Spain tun shekarar 2013.

    Puente ya sanar da matakin nasa ne a ƙarshen dogon zaman majalisar dokoki da aka yi a yammacin ranar Talata, inda ya yi bayani kan sabbin matakan tsaron layukan dogo, sannan kuma ƴan adawa suka yi masa tambayoyi masu tsauri.

    Ministan ya kuma sanar da janye takarar majalisar dokokin ƙasar da yake a zaɓen ƙasar da ke tafe

    "Ba wai kawai zan sauka daga muƙamina na ministan sufuri ba, na kuma janye daga takarar majalisar dokokin Sifaniya a zaɓe mai zuwa."

  3. Demokrats na kan hanyar ƙwace majalisun dokokin Amurka

    Obama
    Bayanan hoto, Jagoran jam'iyyar Demokrats, Barack Obama

    Babbar jam'iyyar hamayya ta Demokrats a Amurka na kan hanyar ƙwace iko da majalisun dokokin Amurka biyu.

    Yayin da sakamakon zaɓen ke ci gaba da fitowa Demokrats ta samu kureru 53 cikin 100 na majalisar dattawan ƙasar.

    Yayin da majalisar wakilai zuwa yanzu ta samu kujeru 224, yayin da Republican ta samu 134 cikin kujeru 358 da aka kammala fitar da sakamakonsu a yanzu.

    Zuwa yanzu dai ana dakon sakamakon zaɓen kujerun majalisar wakilai 77.

    Jagoran jam'iyyar, wanda kuma shi ne tsohon shugaban ƙasar, Barack Obama ya ce sakamakon alama ce da ke nuna cewa ƙarara Amurkawa na buƙatar chanji.

  4. Jam'iyyar Trump na shan mummunan kaye a zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka

    Trump

    Jam'iyyar Republican ta Shugaba Trump na ci gaba da shan gagarumin kaye a zaɓukan tsakiyar Amurka.

    Yayin da sakamakon zaɓen ke ci gaba da fitowa, jam'iyyar hamayya ta Demokrats ta kama hanyar ƙwace rinjayen majalisar dattawa da ta wakilan ƙasar.

    Kafin wannan zaɓen dai jam'iyyar Republican ce kje da rinjaye a duka majalisun biyu.

    Tun kafin zaɓen ne dai masu nazarin siyasar ƙasar suka yi hasashen Demokrats za ta ƙwace iko da majalisar wakilai, amma ba a yi zaton za ta ƙwace iko a majalisar dattawa ba.

  5. Sallama

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman sakamakon zabukan tsakiyar wa'adin Amurka.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.