KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Lahadi 06/09/2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Za mu lalata jiragen dakon man fetur ɗin Iran - Amurka

    Pete Hegseth

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Tsaron Amurka ya yi barazanar cewa idan Iran ta kai wa jiragen ruwan Amurka hari, Amurka za ta mayar da martani ta hanyar “lalata tare da nutsar da jiragen dakon man fetur ɗinta.”

    Pete Hegseth ya wallafa a shafin X, yana magana kan sabon sanarwar Rundunar Sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM), cewa: “Abu ne mai sauƙi: Idan Iran ta kai wa jiragen ruwan Amurka hari, za mu lalata (tare da nutsar da) jiragen dakon man fetur ɗinta.”

    A cewarsa, abin da Iran ke bukata kawai shi ne “kada ta kai wa Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka hari.”

    Mista Hegseth ya ce: “Rundunar jiragen dakon man fetur ta Iran ba ta da kariya. Iran ba ta da rundunar sojin ruwa ko ta sama. Jiragen samanmu, jiragen ruwanmu da kuma jiragen ruwa masu tafiya ƙarƙashin ruwa na iya kai musu hari gaba ɗaya.”

    Sa’o’i kaɗan da suka gabata, CENTCOM ta ce ta kai hari kan jiragen dakon man fetur uku na Iran, yayin da Admiral Brad Cooper, kwamandan CENTCOM, ya aika da saƙo cewa: “Saƙon da muke son ya isa ga IRGC ya zama a bayyane: Idan kuka yi wa biyu daga cikin jiragen ruwanmu hari, za mu jefa muku wani ƙarin tsadar tattalin arziki; wato, za mu lalata jiragen ruwanku uku.”

  2. Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare a kudancin Lebanon

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce mutane huɗu sun mutu, yayin da wasu kuma suka jikkata.

    Isra'ila ta ce hare-haren nata martani ne ga wani harin jirgin sama maras matuƙi na Hezbollah kan dakarunta a wani yanki na Lebanon da Isra'ila ta ayyana a matsayin yankin tsaro.

  3. Gwamnatin Nijar ta gode wa Rasha bisa daƙile yunƙurin juyin mulki

    Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya gana da jakadan Rasha a Nijar, Viktor Voropaev, a ranar 4 ga Satumba, inda ya gode masa da taimakon da rundunar Africa Corps ta Rasha ta bayar wajen daƙile wani yunƙurin hambarar da gwamnatinsa.

    Shafin labarai mai zaman kansa na ActuNiger ne ya ruwaito hakan a ranar 5 ga Satumba, inda rahoton ya ce Jakadan na Rasha ya gana da Janar Tchiani ne bayan majalisar ministocin Nijar ta zargi Faransa a hukumance da hannu wajen shirya wani yunƙurin juyin mulki da wasu jami'an rundunar musamman ta sojoji suka yi a ranar 29 ga Agusta.

    Rahotanni sun ce gwamnatin Rasha ta Kremlin ta nuna sha'awar goyon bayan zargin da Nijar ke yi na cewa wasu ƙasashen waje suna da hannu a wannan yunƙuri.

    A cewar ActuNiger, Voropaev ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Rasha cewa akwai zargin cewa jami'an sojin da ke da hannu a yunƙurin juyin mulkin suna ƙarƙashin umarnin wasu ƙasashen waje da ba a bayyana sunayensu ba.

    Gwamnatin Rasha ta sha alwashin ci gaba da bai wa ƙawayenta masu mulkin soji a yankin Sahel goyon baya wajen yaƙi da abin da ta kira "masu tsattsauran ra'ayi da kuma magoya bayansu na Turai".

  4. Mun kuɓutar da mutum 211 daga masu garkuwa a wata 17 - ƳansandaN Enugu

    Enugu

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴansanda a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun kuɓutar da mutum 211 da aka yi garkuwa da su, tare da kama mutum 6,240 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban a cikin wata 17 da suka gudanar da aiki na musamman.

    Jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito wannan labari a ranar 6 ga Satumba.

    Kwamishinan ƴansandan jihar, Mamman Giwa, ya ce a ranar 5 ga Satumba cewa sun kuma kai ga ƙwato bindigogi 156 da kuma harsasai 1,486, a wani yunƙuri na ci gaba da yaƙi da garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran munanan laifuffuka a faɗin jihar.

    Giwa ya ce daga cikin waɗanda aka kama akwai mutum 158 da ake zargi da garkuwa da mutane da 186 da ake zargi da fashi da makami da 188 da ake zargi da kisan kai da kuma 57 da ake zargi da fyaɗe da lalata da yara.

    Ya ƙara da cewa rundunar ta kuma kama mutum 273 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri, yayin da aka kama wasu 63 bisa zargin mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba.

    Kwamishinan ya ce sauran mutane 5,315 an kama su ne bisa zargin aikata wasu laifuffuka daban-daban, ciki har da sata, ɓarna ta hanyar kutse da kuma lalata dukiyoyi.

  5. Kotu ta yanke wa ƴar jarida hukuncin kisa saboda yunƙurin safarar miyagun ƙwayoyi

    Sarah Khalifa

    Asalin hoton, Sarah Khalifa Instagram account

    Wata kotu a Masar ta yankewa mutane goma sha biyu hukuncin kisa - ciki har da mai gabatar da shirye-shirye a talabijin - sakamakon samun su da laifin mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba da kuma haɗa miyagun ƙwayoyi.

    An yanke wa mutum 9 daga ciki hukuncin ɗaurin rai da rai daga ciki.

    Wakilin BBC ya ce mai gabatar da shirye-shiryen telebijin ɗin, Sarah Khalifa sananniya ce a ƙasashen labarabawa musamman da shirinta "Mission Impossible'' inda ake tattauna batutuwan tsaro da laifuka.

    Kotun manyan laifukan ta ce ƴansanda sun ƙwace kilo 750 na sinadaran da ake amfani da su wajen haɗa miyagun ƙwayoyin da kudinsu ya kai dalar Amurka miliyan 40.

    Lauyan Khalifa ya ce za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin, inda ta ƙara da cewa ita ba ta taɓa sanin ƙwaya ba, sannan ta ƙara da cewa kawai ganin hoto ta yi an ɗauke ta da tulin ƙwayoyi a gabanta a ofishin hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.

  6. Iran ta ce ta kai hari kan jirgin Amurka a mashigar Hormuz

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun juyin-juya-hali na Iran sun ce jami'ansu sun kai wa wani jirgi maras matuƙi na Amurka hari a daidai mashigar Hormuz.

    Harin ya afku sa’o’i ƙalilan bayan rundunar sojin Iran ta yi barazanar ramuwar gayya, idan sojojin Amurka suka ci gaba da kaiwa jiragen ruwan Iran hari.

    Gargadin ya biyo bayan harin da Amurka ta kaiwa tankokin man Iran 3 ranar Asabar. Amurka ta bayyana cewa hare-haren da ta kai na matsayin martanin harba makamai masu linzami da Iran ta yi kusa da jiragen ruwa na Amurka.

  7. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da safiyar ranar Lahadi daga nan sashen Hausa na BBC.

    Yau ma mun dawo kamar kullum da labarai da rahotanni da sharhi kan muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasance da wannan shafi na kai tsaye na sashen Hausa na BBC. Ka da ku manta za ku iya leƙawa sauran shafukan namu na sada zumunta domin samun ƙarin labarai da rahotanni da ma hirarraki.