Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman bayanai dangane da yaƙin Iran da ma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 21/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Ghana ta kama aƙalla baƙin haure 600, ciki har da ƙananan yara 400

    Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin ƙasar Ghana sun kama sama da mutum 600 ƴan ci-rani da ba su da takardun izinin zama, a birni na biyu mafi girma a ƙasar, wato Kumasi.

    Rahotanni sun ce daga cikin waɗanda aka tsare akwai kusan yara 400 da kuma mata 72. Hukumomin Ghana sun ce samamen wani ɓangare ne na wani shiri da ke nufin ƙaƙƙabe mabarata ‘yan ƙasashen waje da ke taruwa a cikin biranen ƙasar.

    Ana ci gaba da tantance waɗanda aka kama domin gano ƙasashensu da kuma duba ko su ne waɗanda ake safarar su da masu ɗaukar nauyin su.

  2. An gyara bututun da ke kai mai daga Rasha zuwa Turai - Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce an gyara bututun man da ke kai mai daga Rasha zuwa Turai, wanda zai iya bai wa Kyiv wata dama ta ƙarbar wani babban rance daga ƙungiyar Tarayyar Turai.

    Bututun man na Druzbah shi ke kai mai daga Rasha zuwa Hungary da Slovakia ta hanyar da ta ratsa Ukraine. Ba a sake ganin wucewar mai ta bututun ba tun daga watan Janairu, lokacin da Ukraine ta ce wasu hare-haren Rasha sun lalata mata shi.

    Firaministan Hungary mai barin gado, Viktor Orban, ya jinkirta amincewa da rancen dala biliyan 100 na Tarayyar Turai ga Ukraine har sai an gyara bututun.

    Amma ana sa ran Tarayyar Turai za ta amince da wannan rance mai mutuƙar mahimmanci ga Ukraine.

  3. Har yanzu babu tabbacin tattaunawar Amurka da Iran a Pakistan

    Iran Amurka

    Asalin hoton, Getty images/Tasnim

    Har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa Amurka ko Iran za su tura tawagoginsu zuwa Pakistan domin shiga sabuwar tattaunawa, yayin da lokaci ke ƙara ƙurewa kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu da aka cimma na ɗaga ƙafa a yaƙin.

    Wakiliyar BBC ta ce wanda ake sa ran zai jagoranci tawagar Iran a tattaunawar ya ce ƙasar sa ba za ta shiga tattaunawar ba mutuƙar aka yi mata barazana.

    An dakatar da shirin tafiyar mataimakin shugaban Amurka JD Vance daga Washington halartar tattaunawar, yayin da ita ma Iran ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar ko za ta shiga tattaunawar ba.

    Iran da Pakistan da ke taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikicin, sun ce yarjejeniyar za ta ƙare cikin sa’o’i masu zuwa, amma Shugaban Amurka Donald Trump ya ce za ta ƙare ne da yammacin gobe Laraba agogon Washington.

  4. An kashe Falasɗinawa biyu, ciki har da ɗan shekara 13 a gaɓar yamma da kogin Jordan

    Ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta ce Falasɗinawa 2 ciki har da wani yaro mai shekara 13 sun mutu a wani hari da Yahudawa ƴan kama guri zauna suka kai a yankin gaɓar yamma da Kogin Jordan.

    Wakilin BBC ya ce ƙungiyar agajin ta Red Crescent dake Falasɗinu ta ce an jikkata ƙarin wasu mutane 4 da harbin bindiga inda aka kai su asibiti a kauyen Al-Mughayyir.

    Magajin garin kauyen ya ce sojojin Isra’ila ne suka kai harin. Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ce tana binciken lamarin. A karshen watan da ya gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun kusan hare-hare 6 a kowace rana daga Yahudawa ‘yan kama guri zauna.

  5. Tinubu ya cire ministan kuɗi da na gidaje

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wasu sauye-sauye a majalisar ministocin ƙasar, inda ya cire ministan kuɗi, Wale Edun da ministan gidaje, Ahmed Musa Dangiwa.

    A wata sanarwa da sakataren gwamnatin ƙasar, Sanata George Akume ya fitar, ya ce an buƙaci ministan kuɗin ya miƙa aiki ga ƙaramin ministan kuɗin ƙasar, Taiwo Oyedele, wanda zai maye gurbinsa a matsayin sabon babban ministan kuɗin sannan kuma mai jagorantar harkokin tattalin arzikin ƙasar.

    Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu ya naɗa Muttaqa Rabe Darma a matsayin sabon ministan gidaje, a yayin da aka buƙaci Dangiwa ya miƙa aiki ga ƙaramin ministan ma'aikatar na wucin-gadi.

    Bugu da ƙari, sanarwar ta buƙaci a miƙa aikin daga yau Talata zuwa ranar Alhamis, 23 ga watan Afirlun.

    Shugaba Tinubu ya yi godiya ga tsofaffin ministocin, sannan ya musu fatan alheri a ayyukansu na gaba.

  6. Donald Trump ya ce yana gab da samun galaba kan Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana ganin Amurka na matsayin da za ta iya samun galaba akan Iran a tattaunawar da take yi, yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu ke shirin ƙarewa a gobe Laraba.

    A sabon kalamin da yayi, Mista Trump ya ce ba ya son a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar, yana mai cewa Amurka a shirye take ta ɗauki matakin soja idan buƙatar hakan ya zama dole.

    Har yanzu dai ba a tabbatar ko tattaunawar yarjejeniyar zaman lafiyar da ake shirin yi a Pakistan za ta gudana ba.

    Iran ba ta tabbatar ko za ta tura tawaga ba, yayin da mataimakin shugaban Amurka J. D. Vance wanda zai jagoranci tawagar Amurka, har yanzu rahotanni na cewa bai baro Washington ba.

    Wakiliyar BBC ta ce kalaman dake futowa daga bakin Iraniyawa a wannan lokaci na cike da fushi da kuma rashin tabbas.

  7. Claudia Sheinbaum ta Mexico ta jajanta kan harin wani ɗan bindiga a ƙasar

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta bayyana goyon bayanta ga waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka jikkata a wani harin bindiga da ya faru a ɗaya daga cikin muhimman wuraren yawon buɗe ido na ƙasar.

    Wani ɗan bindiga, wanda ba a san asalinsa ba ne ya buɗe wuta kan masu yawon buɗe ido a tsohon wurin tarihi na Teotihuacan, inda ya kashe wata mata ‘yar ƙasar Canada tare da jikkata aƙalla mutane 13.

    Daga bisani kuma ya kashe kansa. Yanzu haka, saura kusan makonni bakwai kacal a fara wasan farko na gasar cin kofin duniya ta ƙwallon ƙafa ta maza, wadda za a gudanar a birnin Mexico City.

  8. Firaiministan Japan ta janyo cece-kuce kan aikewa da hadaya wurin bauta

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministar Japan, Sanae Takaichi, ta aika da hadayar addini zuwa wani wurin ibada mai ciki da cece-kuce da ke girmama waɗanda suka mutu a yaƙin ƙasar.

    Wannan wuri da ke Tokyo yana ɗauke da sunayen mutane fiye da miliyan biyu, ciki har da wasu shugabannin Japan da aka yanke musu hukunci kan laifukan yaƙi.

    Ana ganin matakin zai iya tayar da hankalin makwabtan Japan din. Takaichi ta jima tana yawan kai ziyara zuwa wannan wuri tun kafin ta hau mulki a shekarar da ta gabata.

    China da kuma Korea Ta Kudu suna kallon wurin a matsayin alamar zaluncin Japan a lokacin yaƙi.

  9. Japan za ta fara sayar da jiragen yaƙi ga Turai

    Gwamnatin Japan ta bayyana cewa za ta soke wasu ƙa’idojin hada-hadar makamai da kasashen duniya a karon farko cikin shekaru da dama.

    Wannan sauyi, wanda majalisar ministoci ta amince da shi, an yi shi ne da nufin ƙarfafa masana’antar tsaron Japan.

    Wakiliyar BBC ta ce Japan ta jima da haramta fitar da makamai, kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin kasar da aka amince da shi bayan yakin duniya na biyu, sai dai matakin na yanzu ya nuna a shirye take ta dawo da huldar tsaro da kasashen duniya a karfon farko cikin gwamman shekaru.

    Sabbin dokokin za su buɗe ƙofa ga yiwuwar sayar da makamai kamar makamai masu linzami, jiragen ruwa na yaƙi, da sauran makaman soja ga ƙasashen Turai da Asiya da ke neman hanyoyin sauya dogaro daga masu samar da makamai na Amurka.

  10. Apple ya naɗa John Ternus a matsayin shugaba

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Apple ya nada John Ternus a matsayin sabon shugabansa, inda zai maye gurbin ɗaya daga cikin manyan shugabanninsa da suka yi tasiri a masana’antar fasaha, Tim Cook.

    Mr Ternus, wanda a halin yanzu ke shugabantar sashen injiniyanci da kayan aiki na kamfanin, zai karɓi ragamar mulki a watan Satumba.

    Mr Cook zai sauka daga mukaminsa ne bayan shekaru goma sha biyar (15) yana jagorantar Apple, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen mayar da kamfanin ɗaya daga cikin manyan kamfanoni masu darajar tiriliyyoyin daloli a duniya.

    Sai dai a ‘yan shekarun nan, kamfanin ya dan fuskanci jan kafa musamman wajen rungumar fasahohin AI da zamani ya zo da su.

  11. Gwamnatin Najeriya ta yi ƙarar mutanen da ta zarga da kitsa juyin mulki

    ..

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar mutanen da ta zarga da kitsa juyin mulki ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda take tuhumar su da laifuka 13.

    Mutanen da gwamnatin ke ƙara sun hada da tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma ministan mai na ƙasar, Timipre Sylva da wani tsoffin sojoji da jami'in ƴan sanda da kuma wasu ƙarin mutum uku.

    Wasu takardu da BBC ta gani sun nuna yadda gwamnati ta shigar da ƙarar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ake sa ran mutanen da ake zargin za su bayyana a ranar Laraba, a gaban mai shari'a Joyce Abdulmalik.

    Daga cikin laifukan da ake tuhumar mutanen da su sun haɗa da cin amanar ƙasa da laifuka masu alaƙa da ta'addanci da kuma ƙin bayyana bayanan tsaro.

    A ƙarƙashin dokar Najeriya dai, cin amanar ƙasa na ɗaya daga cikin manyan laifuka da ka iya janyo hukunci mai tsananin da ya haɗa da ɗaurin rai da rai.

  12. Kotu ta umarci ICPC ta ci gaba da tsare Malam Nasiru El-Rufai har zuwa Yuni

    ..

    Asalin hoton, ElRufai/X

    Babbar kotun jihar Kaduna ta ɗage zaman sauraron bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru ElRufai har zuwa farkon makon watan Yuni.

    Mai Shari'a Darius Khobo wanda ya sanar da hukuncin ya yi umarnin cewa Nasiru ElRufai ya kasance a hannun hukumar ICPC domin cigaba da tsarewa.

    Kotun ta kuma sanar da tsohon gwamnan cewa ya kame bakinsa daga yin maganganu sannan kuma dole ne ya rinƙa halartar dukkannin zaman kotu.

    A makon da ya gabata ne dai hukumar ICPC ta gurfanar da Malam Nasiru ElRufai a gaban kotun bisa tuhume-tuhume guda 9.

  13. Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun yi ƙarar Mali

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama guda uku sun shigar da ƙasar Mali ƙara a kotun kare haƙƙoƙin ɗan adam bisa zargin ƙasar da gaza kare cin zarafin da sojoji suka yi a 2022.

    Ƙungiyayoyin sun ce ba ta taɓa jin faruwar irin wannan al'amari ba kuma hakan ka iya janyo abin da zai saka a tuhumi ƙasar saboda aikin da ta yi da sojojin.

  14. Harin Yahudawa ƴan kama wuri zauna ya kashe Falasɗinawa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce Falasdinawa biyu ciki har da wani yaro mai shekara 13 sun mutu a wani hari da Yahudawa ƴan kama wuri zauna suka kai a Yamma da Kogin Jordan.

    Kungiyar ta ce wasu ƙarin mutane huɗu sun jikkata a ƙauyen Al-Mughayyir da ke kusa da Ramallah.

    Magajin garin ƙauyen ya ce sojojin Isra’ila ne suka kashe su. Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ce tana binciken lamarin.

    A ƙarshen watan da ya gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun kusan hare-hare 6 a kowace rana daga ‘yan kama wuri zauna.

  15. Babu tabbas Iran za ta shiga gasar cin kofin duniya ta 2026

    Ministan harkokin wasannin ƙasar Iran Ahmad Donyamali ya ce shawarar aikewa da tawagar ƴan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar zuwa gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na 2026 ya rataya a wuyan dakarun soji.

    Amurka dai na ɗaya daga cikin ƙasashe uku da ke karɓar baƙuncin gasar da za a fara a watan Yuni.

    Ministan ya ce Iran za ta duba yiwuwar aika tawagar ko akasin haka ne bayan da al'amura suka daidaita sannan kuma idan Amurka ta daina nuna halinta na "rashin kirki".

  16. Sojoji Iran sun ce jirgin ƙasar ya kutsa ta shingen Amurka zuwa tashar ruwa

    Sojojin jamhuriyar Musulunci ta Iran sun ce wani jirgin dakon mai mallakar Iran ya bujere wa shingen da Amurka ta saka inda ya shiga tashar ruwan ƙsar da ke kudanci.

    A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, sojojin sun ce " duk da yawan gargaɗi da barazanar da sojojin ruwan Amurka ke yi, jirgin na Iran mai suna Silica City, ya kutsa ya shiga tashar da taimakon sojojin ruwan Iran ɗin a daren da ya gabata, bayan ratsawa ta ruwan Arabian sea.

    Amurka dai har kawo yanzu ba ta ce uffan ba dangane da iƙrarin sojojin ƙasar Iran din.

    Cibiyar sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM, a wata sanarwa jiya ta ce tun bayan toshe tashoshin Iran, sojojin sun tilasta wa jiragen ruwa 27 ƙin shiga tashoshin ruwan Iran.

  17. Wane tasiri toshe hanyoyin ruwa ke yi a yaƙin Iran?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta kaddamar da hare-haren jirage mara matuki kan jiragen ruwan sojin Amurka a yankin Oman, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran Tasnim ya ruwaito, bayan da Amurka ta ƙwace wani jirgin ruwa ɗauke da tutar Iran.

    Amurka ta ce an tarwatsa jirgin na Iran bayan "kasa yin biyayya ga gargadin da aka yi ta yi" daga sojojin ƙasar na kusan sa'o'i shida.

    Bayanai sun nuna cewa jirgin na Touska ya kasance yana da nisan mil 40 da tashar jiragen ruwa na Chabahar, a kudu maso gabashin Iran, bayan barin tashar Klang, a Malaysia, a ranar 12 ga Afrilu.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sun yi ta "gargaɗin dakatar da zirga-zirga" bayan kokarin bi ta hanyar da Amurka ta kulle a tashar jiragen ruwa na Iran.

    "Ma'aikatan jirgin na Iran sun ki bin umarni, saboda haka ne sojojin ruwan mu suka ɓula wani wuri a injin jirgin," in ji shi. A yanzu katon jigin ruwan yana karkashin ikon Amurka, a cewar Trump. Ya kuma kasance cikin takunkuman Amurka "saboda tarihin aikata ba daidai ba".

  18. Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC

    ..

    Asalin hoton, BBC Hausa Collage

    Magoya bayan tsoffin ƴan takarar shugaban ƙasa a Najeriya Peter Obi, da kuma Rabiu Musa Kwankwaso sun kafa wata ƙungiya mai suna Obi–Kwankwaso (OK Movement) da ta soma tattaunawa domin ganin jam'iyyar ADC ta tsayar da su takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027 da ke tafe.

    Ƙungiyar, wadda aka kafa a Abuja a ranar Litinin, ta ce tuni ta soma samar da rassanta a jihohi 36 na ƙasar da Abuja, tare da naɗa shugabanninta na jihohi da yankuna domin jagorantar yaɗa ayyukanta.

    Sakataren watsa labaran ƙungiyar na ƙasa, Justin Ijeh, ya bayyana ta a matsayin gamin gambiza, don haɗa karfi da karfe tsakanin ƙungiyar magoya bayan Peter Obi ta Obidient Movement, da kuma ta magoya bayan Kwankwaso, wato Kwankwasiyya.

    Wannan dai na nuna wani irin sabon salo na sake ɗaure ɗamara yayin da ake ta ƙulla mu'amalar siyasa, sakamakon rashin tabbacin wanda zai lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na ADC kafin babban zaɓen 2027.

    Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin kungiyar ya bayyana cewa sabuwar kungiyar ta kunshi mambobi daga Kwankwasiyya, da Obidients, da jam'iyyar NNPP, da Labour da kuma wasu daga ADC.

  19. Dalilai huɗu da suka sa tattaunawar Iran da Amurka ke cikin ƙila-wa-ƙala

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Makomar tattaunawar Iran da Amurka ta shiga cikin rashin tabbas yayin da lokacin da aka kebe na tsagaita wuta ke daf daƙkarewa. Abin da ya sa ake gani a yanzu ba wai rashin cimma matsayar diflomasiyya ba ce kaɗai, har ma da kalamai masu zafi da tsauri tsakanin ɓangarori, barazana da kuma bayanai masu cin karo da juna daga dukkan ɓangarori.

    A cewar rahotanni da dama, babu tabbas cewa Iran za ta shiga tattaunawar da aka tsara za a yi wanda Pakistan ke shiga tsakani. Yayin da wasu majiyoyi ke bayyana cewa Iran na duba yiwuwar shiga tattaunawa, wasu kuwa sun ce ƙasar za ta iya janye wa watakila saboda yanayin da ake ciki.

    A ɗaya gefe, lamarin yana ci gaba da zama mai tsarkakiya bayan da rahotanni suka ce mataimakin shugaban Amurka wanda ke jagorantar tawagar tattaunawar, JD Vance, bai ma je Pakistan ba watakila saboda rashin tabbas da ake da shi kan tattaunawar.

    A nan, tattaunawar za ta iya kawo fatan cimma matsayar diflomasiyya ko kuma barazanar komawa fagen daga.

  20. Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami'an tsaro uziri

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A jamhuriyar Nijar hukumomin tsaron ƙasar na kira ga al'ummar yankunan da ke fama da matsalolin tsaro da su yi uzuri ga dakarun ƙasar dangane da jinkirin zuwan jami’an tsaro idan aka kai hari, kamar yadda al’ummar ƙasar suka gani.

    Minista tsaron ƙasar ne Janar Salifou Mody ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da kafar Television ta RTN, inda ya ƙara da kira ga yan Nijar da su fahimci cewa jami’an tsaro ba za su iya kasancewa a kowane ƙauye ba, duba da cewa Nijar na da kusan ƙauyuka 32,000.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan ta'adda musamman a kan sojojin ƙsar.