KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 21 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Yadda ƴansanda suka tilasta wa shugaban yaƙi da rashawa na Najeriya bayar da cin hanci

    ...
    Bayanan hoto, Shugaban hukumar ICPC a Najeriya

    Wani abu mai kama da almara ko? Amma da gaske ne ya faru.

    An daɗe ƴan Najeriya na kokawa game da ƙazancewar ayyukan rashawa a ma'aikatu da hukumomin gwamnati, kuma hukumar ƴansanda ta ƙasar na cikin waɗanda a kodayaushe ake nunawa, kan cewa jami'anta na yawan karɓar kuɗi daga al'umma sa'ilin da suke bakin aiki.

    Amma an ce kwana dubu ta ɓarawo, kwana ɗaya kuma ta mai kaya.

    A wannan karo shugaban hukumar yaƙi da rashawa da laifuka makamantan haka ICPC na Najeriya, Musa Aliyu ne ya faɗa hannun wasu jami'an ƴansanda a birnin Abuja, waɗanda suka buƙace shi ya ba su kuɗi bayan zargin shi da laifin karya doka.

    Tuni hukumar ƴansanda ta tabbatar da faruwar lamarin har ma ta bayyana cewa ta fara ɗaukar matakin kan lamarin.

  2. Bahrain da Jordan sun ce sun kakkaɓo makaman da Iran ta harba musu

    Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta gargaɗi al’umma da su gaggauta zuwa wuraren tsaro mafi kusa bayan da ta bayyana cewa ƙasar na fuskantar hare-hare daga Iran.

    Kafin wannan sanarwar, rundunar sojin Bahrain ta ce ta samu nasarar daƙile wasu hare-haren da aka ƙaddamar daga Iran.

    A gefe guda kuma, rundunar sojin Jordan ta sanar a yau cewa ta kakkaɓo makamai masu linzami guda uku da aka harba daga Iran.

    Tun da farko ma, Jordan ta ce ta yi nasarar kakkaɓo jiragen sama marasa matuƙa guda biyar da aka ƙaddamar daga Iran.

    Sojojin ƙasar sun ce babu wanda ya mutu ko ya jikkata sakamakon hare-haren.

    Tun farko dai rundunonin sojin Iran sun sanar da cewa sun kai hare-hare kan Bahrain da Jordan.

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta kuma yi iƙirarin cewa an kashe wasu sojojin Amurka a hare-haren da ta kai yankin Rukban na Jordan, sai dai har yanzu Amurka ba ta mayar da martani ba. .

  3. Qatar ta buƙaci iran ta biya ta diyyar hare-haren da ta kai mata

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Qatar ta miƙa wa Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Tsaro wasiƙu inda ta dora cikakken alhakin hare-haren da aka kai a kan ƙasarta kan Iran, tare da neman a biya ta diyya kan dukkan ɓarnar da aka yi.

    A cikin wasiƙun, Qatar ta ce Iran ta kai hari kan wani jirgin dakon man ta kusa da mashigar Hormuz a ranar 7 ga Yuli, sannan ta sake harba makamai masu linzami zuwa cikin ƙasar a ranakun 12 da 17 ga Yuli.

    Jami'an Qatar sun ce mutane uku, ciki har da wani yaro, sun jikkata a harin ranar 12 ga Yuli bayan gutsuttsuran makaman da aka tarwatsa sun faɗi a wuraren zama.

    Qatar ta bayyana harin Iran a kan yankinta a matsayin ƙeta huruminta da 'yancinta na kasa, tare da cewa hakan barazana ce kai tsaye ga tsaro da cikakken ikon kasar.

    Gwamnatin Qatar ta kuma jaddada cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar duk wani matakin da ya dace domin kare ikon ƙasarta da tsaron al'ummarta da rayukan 'yan ƙasarta.

    Sai dai Iran ta ce hare-haren da take kai wa ƙasashen yankin, tana kai su ne a cibiyoyin sojojin Amurka da dakarunta da ke jibge a waɗannan ƙasashe.

  4. Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin hukumomi 26

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin sabbin shugabanni da mambobi 26 a hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10.

    Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, wanda zai jagoranci Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA), yayin da Manjo Janar Junaid Bindawa zai kasance shugaban kula da Hukumar Albashin ma'aikata ta Ƙasa.

    Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Dr Abuh Mohammed a matsayin Darakta Janar na Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Dr Akinola Odeyemi a matsayin shugaban NBET, da Dr Anthony Inalegwu Godwin a matsayin shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Najeriya.

    Haka kuma shugaban ya kafa sabuwar Hukumar Kula da alhakin kasafin kuɗi ƙarƙashin jagorancin Dr Abdullahi Maikano Saidu, tare da naɗa Shuni Muhammad Dahiru a matsayin babban sakataren Hukumar Yaƙi da Jahilci ta Ƙasa.

    An ce duk naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.

  5. Cutar Ebola ta bazu zuwa sabon yankin Adja a DR Congo

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Cutar Ebola da ke yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta bazu zuwa yankunan kiwon lafiya 47 a faɗin larduna biyar na Adja da ke lardin Ituri.

    Alƙaluman da aka fitar ranar 19 ga Yuli sun nuna cewa an tabbatar da mutum 2,423 sun kamu da cutar, yayin da mutum 967 suka mutu, abin da ya sa adadin mace-macen ya kai kashi 39.9 cikin 100.

    A cikin sa'o'i 24 da suka gabata kaɗai, an samu sabbin mutum 79 da suka kamu da cutar da kuma mutuwar mutum 37, inda mafi yawan su suka fito daga lardin Ituri.

    Yankunan Bunia, Nizi, Rwampara da Adja ne suka fi samun sabbin waɗanda suka kamu da cutar.

    Hukumomi sun ce ana bin diddigin kashi 81.1 cikin 100 na waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar, sai dai har yanzu akwai giɓi musamman a lardin Haut‑Uélé.

    An ayyana ɓullar cutar ne a ranar 15 ga Mayu, kuma ƙwayar cutar da ake kira da Bundibugyo ebolavirus ce ke haddasa ta.

    Hukumomin lafiya sun ce matsalar tsaro, yawan zirga-zirgar jama'a da kasuwancin kan iyaka da Uganda da Sudan ta Kudu na ƙara wahalar daƙile yaɗuwar cutar.

    Sun kuma yi gargaɗin cewa wajibi ne a ƙara sa ido da matakan kariya domin daƙile annobar.

  6. Iran ta ce hare-harenta a Jordan sun kashe sojojin Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta ce hare-haren da ta kai kan wani sansanin da sojojin Amurka ke amfani da shi a yankin Rukban na Jordan sun yi sanadiyyar mutuwar wasu sojojin Amurka.

    A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce harin na daga cikin ci gaba da ayyukan soja da take gudanarwa, inda ta ce ta kai hari kan wuraren da ake jibge sojojin Amurka a yankin.

    Sai dai ba ta bayyana adadin waɗanda ta ce harin ya kashe ba.

    Ya zuwa yanzu, gwamnatin Amurka ba ta mayar da martani kan sabon iƙirarin Iran ɗin ba amma kuma ma'aikatar tsaron ƙasar Pentagon ta tabbatar da mutuwar sojojin Amurka uku a hare-haren iran da kuma jikkatar kusan sojojin 100.

    Sabon iƙirarin Iran na zuwa ne yayin da rikici ke ci gaba da ƙamari tsakanin Iran da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ɓangarorin biyu ke zargin juna da kai hare-hare kan muradunsu na soja da na tsaro.

  7. Iran ta yi kira ga duniya kada su amince da duk wani hari kan cibiyoyin nukiliya

    ...

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Iran ta yi kira ga ƙasashen duniya da kada su amince da duk wani hari kan cibiyoyin nukiliya da ake amfani da su domin zaman lafiya, tana mai cewa kare irin waɗannan wurare alhakin ƙasashen duniya ne baki ɗaya.

    A wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Iran a Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya fitar, ya ce Amurka ta harba makamai masu linzami kan wurin da ake gina tashar samar da wutar lantarki ta nukiliya ta Karun (Darkhovin) a safiyar ranar 18 ga Yuli.

    Sanarwar ta bayyana tashar a matsayin "alama ta martaba da kuma dogaro da kai a fannin kimiyya na al'ummar Iran."

    Ta ƙara da cewa duk da Iran na da niyyar ɗaukar duk matakan da suka dace domin kare muradunta na ƙasa da haƙƙoƙinta na ikon mallaka, hana kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliya da ke ƙarƙashin kulawar IAEA da ake amfani da su cikin lumana, nauyi ne da ya rataya a wuyan ƙasashen duniya gaba ɗaya.

    Sai dai Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM ta sanar cewa ta kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Iran, ciki har da cibiyoyin makamai masu linzami, jirage marasa matuƙa da kuma kayayyakin rundunar sojin ruwa ta dakarun IRGC, amma ba ta ambaci tashar Darkhovin ba.

    A nata ɓangaren, Hukumar IAEA ta ce tana binciken rahotannin da ke cewa an kai hari kan tashar nukiliyar Darkhovin da ake ci gaba da ginawa, sai dai har yanzu ba ta fitar da wani rahoto mai zaman kansa da ya tabbatar da abin da ya faru.

  8. Hare-haren Iran sun jikkata sojojinmu kusan 100 cikin makonni biyu - Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar Tsaron Amurka, Pentagon, ta ce kusan sojojin Amurka 100 ne suka jikkata sakamakon hare-haren da Iran ta kai cikin makonni biyu da suka gabata, lamarin da ya nuna yadda rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu ke kara tsananta.

    Pentagon din ta bayyana cewa galibin sojojin sun samu raunuka ne yayin hare-haren da Iran ta kai kan wuraren da sojojin Amurka ke aiki a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Sai dai ma’aikatar ba ta yi ƙarin bayani kan irin raunukan da sojojin suka samu ba.

    Rundunar sojin AMurka ta Pentagon dai a baya da ta sojojin Amurka uku sun mutu sakamakon hare-haren Iran.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundubar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) suka sanar da kai hare-hare kan wasu wurare a Bahrain, Kuwait da Jordan wanda wasu suka kai ga mutuwar sojojin Amurka uku.

  9. Mun kai wa cibiyar bayanan kamfanin Amazon na Amurka hari - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) sun sanar da kai hare-hare kan Kuwait da Jordan, inda suka ce sun kai wa cibiyar bayanan kamfanin Amazon na Amurka da ke Bahrain hari.

    A gefe guda kuma, sojojin Amurka sun ce sun kammala zagaye na goma na hare-haren da suke kai wa Iran, tare da jaddada cewa zirga-zirgar jiragen ruwa za ta ci gaba da gudana a mashigar ruwan Hormuz.

    Haka nan, Hukumar Kula da Harkokin Teku ta Birtaniya ta bayyana cewa wani jirgin dakon mai ya samu rauni sakamakon harin wani makami a mashigar Hormuz.

    Hukumar ta ce ma’aikatan jirgin sun tsira da ransa.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Talata.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.