KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 26/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 26/04/2026

Taƙaitattu

  • An fitar da Trump daga ɗakin taro bayan wani ɗanbindiga ya buɗe wuta
  • Yadda jam'iyyun hamayya sama da goma ke neman yi wa Tinubu taron dangi
  • Abin da muka sani kan mutumin da ake zargi da kai wa Trump hari
  • 'Wanda ake zargi ya ce jami'an Trump ya yi niyyar kai wa hari'
  • Kalli bidiyon yadda aka kuɓutar da Trump a lokacin harin
  • Shugabannin duniya na aike wa saƙonnin jaje ga Trump

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Shugaban jami'an tsaron farin kaya na Amurka ya yaba wa ma'aikatansa

    Daraktan hukumar tsaron farin kaya na Amurka, Sean Curran, ya jinjina wa ma'aikatansa kan ƙoƙarin da suka yi na daƙile harin bindiga a wurin liyafar cin abincin dare.

    "Mun ga irin ƙwazon da ma'aikatanmu suka nuna wajen kare mutane. Ba aiki ne mai sauƙi ba, don haka mun yaba musu da wannan namijin ƙoƙarin da suka yi'', in ji shi.

    Mista Curran ya ƙara da cewa an yi sa'a ɗaya daga cikin jami'an da ak harba yana raye.

    Ya kuma gode wa Shugaba Trump saboda tuntuɓarsa da ya yi kan harin

  2. Sabon faɗa ya ɓarke a yankin Kidal na Mali

    Shugaban Mali

    Asalin hoton, others

    An sake samun sabon faɗa a yankin Kidal da ke arewacin Mali, kwana guda bayan wasu hare-haren haɗin gwiwa da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi suka kai sassan ƙasar ciki har da Bamako, babban birnin ƙasar.

    A ranar Asabar ƙungiyoyin Tuareg da FLA sun yi iƙirarin iko da yankin na Kidal.

    Rundunar Sojin Mali, wadda ta jima tana samun goyon bayan sojojin hayar Rasha , ta ce yanzu haka tana fafatawa da ƙungiyoyin a yankin.

    Kakakin ƙungiyar FLA, Mohamed Ramdane, ya ce sun cimma yarjejeniyar bai wa sojojin hayar Rasha damar janyewa daga yankin.

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniy, Antonio Guterres ya buƙaci ƙasashen duniya su haɗa kai wajen tallafa wa Mali.

    Ƙasar Mali na ƙarƙashin mulkin soji tun shekara 2020.

  3. Araqchi ya gana da sakin Oman a birnin Muscat

    Araqchi da Oman

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi ya gana da sarkin Oman, Haitham bin Tariq a birnin Muscat.

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce jagororin biyu sun tattauna halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Iran da ma yankin baki ɗaya.

    Shafin kafar yaɗa labaran Tabnak ta wallafa cewa ''bayan barin Pakistan an tsara Araqchi zai tafi Rasha ne, domin tattauna yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin.

    To amma sai ma'aikatar harkokin wajen Iran ta sauya tsarin bulaguron nasa, inda ya fara zuwa Oman sannan zai sake komawa Pakistan kafin ya kama hanyar zuwa Rasha.

    Kamfanin dillancin labarai na IRNA na Iran ya ce wasu daga cikin wakilan da Araqchi ya halarci Islamabad da su jiya sun sake komawa Tehran, domin samo umarni kan tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin, kuma za su sake komawa Islamabad, su haɗu da Araqchi domin ci gaba da tattaunawa.

  4. Jami'an FBI sun kai samame gidan mutumin da ake zargi da yin harbi a Washington

    Jami'an tsaro

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an FBI sun kai samamen gidan mutumin da ake zargi da buɗe wuta a taron da Trump ya halarta a Washington.

    Jami'an tsaron sun kai samame gidan mutumin da ke Torrance a birnin California.

    An ga hotunan motocin jami'an tsaro na ficewa daga gidan mutumin bayan bincikarsa.

    Tuni dai jami'an tsaro suka kama mutumin, inda suka ce za su gurfanar da mutumin a gaban kotu.

    Jami'an tsaro

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an tsaro

    Asalin hoton, Reuters

  5. Shugabannin duniya na aike wa saƙonnin jaje ga Trump

    Wata mata

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Shugabannin ƙasashen duniya daban-daban na ci gaba da aikewa da saƙonninsu na jaje kan harin bindiga da aka kai wa Trump a Washington.

    Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce ya yi matuƙar "kaduwa da harin da aka kai ɗakin taron a birnin Washington cikin dare".

    "Dole ne a yi Allah wadai da duk wani hari kan dimokradiyya ko ƴancin faɗin albarkacin baki'', in ji shi.

    Haka ma firministan Kanada, Mark Carney ya ce "ya ji daɗi" da ya samu labarin cewa Trump da mai ɗakinsa da sauran manyan baƙi kowa ya kuɓuta.

    ''Ina jajanta wa waɗanda lamarin ya tayar musu da hankali a wannan taro".

    Shi ma takwaransa na Australia, Anthony Albanese, ya ce ya samu nutsuwa da ya ji waɗanda ke halartar taron sun kuɓuta.

    ''Muna jinjina wa jami'an farin kaya da sauran jami'an tsaro, bisa ƙoƙarin da suka yi,'' in ji shi.

    Kaja Kallas, babbar jami'ar diplomasiyyar Tarayyar Turai, ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Trump da mai ɗakinsa.

    ''Dimokraɗiyya ba ta maraba da tashin hankalin siyasa'', in ji ta.

    Ita ma shugabar riƙo ta ƙasar Venezuela, Delcy Rodríguez ta yi "Allah wadai da yunƙurin harin'', sannan ta aike da saƙon fatan alkairi ga waɗanda suka halarci taron.

    Can a Pakistan Firaministan ƙasar, Shehbaz Sharif, ya ce ya yi matuƙar ''kaɗuwa da labarin harin.

    ''Muna alhini tare da yin addu'a ga Shugaba Trump'', kamar yadda ya bayyana.

    Shi ma firaministan Indiya, Narendra Modi ya ce yana aikewa da saƙon jaje ga Shugaba Trump da mai ɗakinsa da mataimakinsa da sauran mahalarta taron.

    Shugaban Mexico Claudia Sheinbaum ya aike da nasa saƙon jajen.

  6. Kalli bidiyon yadda aka kuɓutar da Trump a lokacin harin

    Shugaba Trump na tsaka da tattaunawa da manyan baƙi lokacin da maharin ya buɗe wuta.

    Nan da nan jami'an tsrao suka yi nasarar kuɓutar da shi tare da fitar da shi daga ɗakin taron.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon yadda aka kuɓutar da Trump
  7. Labarai da dumi-dumi, 'Wanda ake zargi ya ce jami'an Trump ya yi niyyar kai wa hari'

    Kafar yaɗa labarai ta CBS, ƙawar hulɗar BBC a Amurka, ta ce mutumin da ake zargi da kai harin Washington ya faɗa wa hukumomi cewa wasu jami'ai masu alaƙa da Trump ya yi niyyar kai wa hari.

    CBS ta ambato wasu majiyoyi biyu da ba ta ambaci sunansu ba na cewa an ji ƙarar harbin bindiga a ɗakin taron har sau biyar zuwa takwas.

    Tuni dai jami'an tsaro suka samu nasarar kuɓutar da Trump da mai ɗakinsa da sauran manyan baƙi daga wurin da lamarin ya faru.

  8. Hotunan yadda yansanda suka cika birnin Carlifonia domin bincikar gidan maharin

    motoci

    Asalin hoton, Reuters

    jami'an tsrao

    Asalin hoton, Reuters

    jami'an tsaro

    Asalin hoton, Reuters

  9. Abin da muka sani kan mutumin da ake zargi da kai wa Trump hari

    mutumin da ke zargi

    Asalin hoton, DONALD TRUMP

    Jami'an tsaron FBI sun fara fitar da bayanai kan mutumin da ake zargi kai da buɗe wuta a ɗakin taron da Shagaba Trump na Amurka ke halartar taro a birnin Washinton.

    Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce jami'an tsaron sun fitar da bayanai game da mutumin mai shekara 31.

    Ƴansandan sun bayyana sunansa da Cole Tomas Allen, wanda ke zaune a Torrance da ke birnin California a jihar Los Angeles.

    Kafar yaɗa labarai ta CBS, abokiyar hulɗar BBC ta ce Allen na aiki ne a matsayin mai koyarwa a Torrance bayan kammala karatunsa a cibiyar fasaha ta California.

    Ƴansanda sun kuma ce Allen ya sauka a otal ɗin da lamarin ya faru a matsayin baƙo, kuma yana ɗauke da makamai masu yawa, ciki har da bindigogi da wuƙaƙe.

    Tuni dai ƴansanda suka bazama gidansa da ke California domin bincikarsa.

  10. An fitar da Trump daga ɗakin taro bayan wani ɗanbindiga ya buɗe wuta

    ..

    Asalin hoton, ..

    Jami'an tsaron FBI sun samu nararar fitar da shugaban Amurka, Donald Trump daga wani taron cin abincin dare na ƙungiyar masu aiko da rahotonni daga fadar shugaban ƙasar da ake yi kowace shekara a birnin Washintong bayan da wani mutum ya buɗe wuta a wurin taron.

    Da yake jawabi daga fadarsa jim kaɗa bayan faruwar lamarin, Mista Trump ya ce wani mutum ne ɗauke da makamai ya yi yunƙurin kutsawa wurin da taron ke gudana.

    Lamarin ya faru ne lokacin da baƙi suka kammala cin abinci zagaye na farko, inda ka ji ƙarar harbin bindiga, a harabar ɗakin taron da ke Hotel ɗin Hilton a birnin.

    Jami'an tsaron FBI sun yi gaggawar kai wa Trump da mai ɗakinsa ɗauki inda suka yi nasarar fitar da su cikin kariya.

    Bayanai sun ce ɗaya daga cikin harsasan da aka harba ya samu wani jami'in tsaron da ke sanye da rigar kariya, wanda yanzu haka ke asibiti.

    Tuni dai aka kama mutumin da ake zargi da kai harin.

    Wannan ne dai karo na uku da ake yunƙurin kai wa Shugaba Trump harin bindiga a cikin shekaru ƙalilan.

  11. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.