Ma'aikatar kasuwanci ta China ta sanar da cewa, ba za ta yi aiki da takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa kamfanoni biyar da ke son sayen man kasar Iran ba.
China dai ita ce babbar mai sayen man Iran, musamman ta hanyar ƙananan matatun mai masu zaman kansu da aka fi sani da “teapots,” waɗanda ke saye da dogaro da danyen man Iran, wanda ake sayarwa a kan farashi mai rahusa.
Amurka wadda ke ta ƙokarin rage kuɗaden shigar Iran, ta kara sanya takunkumi kan ire-iren wadannan matatun mai.
Sai dai ma'aikatar kasuwancin kasar ta China ta ce ba ta amince da takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba mata ba, don haka kamfanoni da cibiyoyin ba za su yi aiki da buƙatar ba.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce, takunkumin "ya haramtawa da kuma dakatar da kamfanonin kasar gudanar da harkokin cinikayya da sauran ƙasashe, kuma hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa."
Ma'aikatar ta ƙara da cewa: "A ko da yaushe gwamnatin China ta na adawa da takunkumin bai-daya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi ba, ko kuma ba su dace da dokokin ƙasa da ƙasa ba."
Umurnin na Amurka dai ya shafi kamfanonin kasar China guda biyar: uku a lardin Shandong, sai wasu biyu da suka haɗa da matatar mai ta Hengli Petrochemical (Dalian) da kuma Hebei Xinhai Chemical Group.
A jiya ne Washington ta sanya wa wani kamfanin China takunkumi, inda ta ce ya shigo da "miliyoyin ganga" na ɗanyen man Iran tare da samar wa Iran kuɗaɗen shiga na biliyoyin daloli.