Ko Ronaldo zai lashe kofin duniya a gasa ta shida da zai buga?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Za a buɗe labulen fara gasar cin kofin duniya daga ranar 11 ga watan Yuni, tsakanin tawaga 48 da a gudanar a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Portugal, wadda ba ta taɓa ɗaukar kofin duniya ba tana daga cikin kasashen da za su fafata a bana, har da fitatcen ɗan wasanta Cristiano Ronaldo zai yi wasannin karo na shida jimilla.

Cristiano Ronaldo ya karya tarihi da dama a fannin ƙwallon ƙafa, harma yanzu bai zama wani sabon abu ba da zarar ya yi bajinta, domin ya zama abu na yau da kullum.

Amma buga gasar Kofin Duniya ta shida yana da shekara 41 a duniya wani abin mamaki ne matuƙa, har ma da ma'aunin da aka saba amfani da shi wajen auna nasarori da ƙwazo da kuma bajintarsa.

Ana sa ran gasar Kofin Duniya ta 2026 za ta ƙara buɗe wani sabon babi a rayuwar Ronaldo, wanda ya fara daga buga gasar kofin duniya a Jamus a shekarar 2006.

Daga nan ya halarci wadda aka gudanar a Afirka ta Kudu da Brazil da Rasha da kuma Qatar da aka yi a 2022, amma har yanzu ba ta kai shi ga lashe kofin da ya daɗe yana nema ba.

Ronaldo wanda a kullum ake hamayya tsakaninsa da Lionel Messi kan wanene kan gaba a taka leda a duniya - Messi ya lashe kofn duniya a 2022, yayin da ƙyaftin ɗin Portugal shima ya samu nasara a kakar nan.

An fara hamayya tsakanin Ronaldo da Messi tun suna buga wa Real Madrid da Barcelona daga nan ta faɗaɗa zuwa ƙyautar Ballon d'Or, yanzu kuma tana gasar cin kofin duniya da kowannensu zai buga karo na shida jimilla.

Messi ya lashe Ballon d'Or sau takwas, yayin da Ronaldo ya ɗauka sau biyar. Duk da shekarunsu, har yanzu suna ci gaba da rubuta sabbin tarihi a shafuka rayuwarsu a fannin taka leda a duniya mai ban mamaki.

Ga Ronaldo, Kofin Duniya shi ne matakin da bai taɓa mallaka gaba ɗaya ba kamar yadda ya yi a sauran gasa.

Mafi kyawun nasararsa a gasar ta zo ne a 2006 lokacin da Portugal ta kai wasan kusa da na ƙarshe kafin ta sha kashi a hannun Faransa. Tun daga lokacin, ya fuskanci aka fitar da kasar a zagayen ƴan 16 sau biyu, ta kuma kai wasan kwata fainal sau ɗaya, sannan aka fitar da ita tun daga matakin rukuni a Brazil 2014.

A gasar ta 2026, Portugal za ta fafata a rukunin da ya haɗa da tawagar Jamhuriyar Congo da Uzbekistan da kuma ta Colombia a rukunin na 11.

A tsawon gasar Kofin Duniya guda biyar da ya buga, Ronaldo ya yi wasa 22 kuma ya ci ƙwallo takwas jimilla. Wannan adadi mai kyau ne ga mafi yawan ƴan ƙwallon da suke buga gasar, amma bai kai matsayin da ake tsammani daga Ronaldo, wanda ya mayar da yin abubuwan mamaki kamar al'ada a matakin ƙungiyoyi.

Kofin Duniya na Qatar 2022 ya yi kama da na karshe da ya halarta a rayuwarsa ta taka leda. Ya halarci gasar ta Qatar ne a lokacin da ake ta magana kan ficewarsa daga Manchester United. Ya ci ƙwallo a gasar, amma tsohon kocin Portugal Fernando Santos ya ajiye shi a benci, bayan shan kashin da suka yi a hannun Koriya ta Kudu da ci 2-1, sannan Portugal ta doke Switzerland a zagayen gaba ba tare da Ronaldo ba a fafatawar.

Sai dai Ronaldo ya sake dawowa cikin tawagar Portugal a kan ganiya ƙarƙashin jagorancin tsohon kocin Belgium, Roberto Martinez, da irin juriyar da ta sa mutane ke ganin kamar a lokaci baya bai yi tasiri ba a Qatar.

Yanzu Portugal na da tarin fitattun ƴan wasa kamar Vitinha da Joao Neves da Bruno Fernandes da kuma Nuno Mendes, amma Ronaldo ne har yanzu babban tauraron tawagar.

Bayan fitar da Portugal a wasan kwata fainal a Euro 2024, Portugal ta dawo da ƙarfi inda ta doke zakarun kofin nahiyar Turai, Sifaniya a wasan ƙarshe a Nations League a bara, kuma yanzu za ta buga gasar kofin duniya da za a gudanar a Arewacin Amurka a kan ganiya tare da Ronaldo a matsayin jagora.

Martinez ya ce alkaluman wasa har yanzu suna nuna muhimmancin Ronaldo a tawagar. A ƙarƙashin jagorancinsa, Ronaldo ya ci ƙwallo 25 cikin wasa 30, adadin da ya fi matsakaicin ƙwallayen da ya ci a ƙarƙashin dukkan kocin ƙasar da suka gabata. Baya ga haka, yana ba da gudummawa ta hanyoyi da ba lallai ne su bayyana a jadawalin masu cin ƙwallaye ba.

"Kwarewarsa wajen motsi da gudu don jawo hankalin abokan hamayya, buɗe sarari da kuma yanke masu tsaron baya abin mamaki ne," in ji Martinez a wata hira da Reuters a watan Mayu.

Ya ƙara da cewa: "Mutumin da ya lashe komai yana sa ƙwazo da ɗaukar kowacce karawa da mahimmaci, duk da bai taɓa lashe kofin duniya ba."

Ga Ronaldo, Kofin Duniya na 2026 na iya zama wasan bankwana daga buga wa Portugal wasanni. Amma kuma, an taɓa faɗin hakan sau da dama a baya, kuma duk da haka ya ci gaba da dawowa yana karya tarihi a fannin taka leda. Shi ya sa har yanzu mutane ba sa gaggawar cewa wannan ne karon ƙarshen labarin Cristiano Ronaldo a babbar gasar tamaula ta duniya.