Jerin ƴantakarar gwamna na jam'iyyar APC a 2027

Ƴantakarar gwamnan APC
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Yayin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban zaɓen shekarar 2027 a Najeriya, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na ci gaba da fitar da masu neman takarar gwamna a jihohi daban-daban na ƙasar.

Wasu daga cikinsu gwamnoni ne masu neman wa'adin mulki na biyu, yayin da wasu kuma sabbin ƴan siyasa ne da ke neman jagorancin jihohinsu.

A wasu jihohin an kai ruwa rana kafin masu matsaya kan wanda zai tsaya wa jam'iyyar takara, musamman inda ake da ƴan takara masu tasiri da kuma manyan jiga-jigan APC a jihohin.

A wannan muƙala, mun tattaro jerin sunayen masu neman tikitin gwamna na jam'iyyar APC a jihohin Najeriya tare da taƙaitaccen bayani kan tarihinsu da kuma rawar da suka taka a harkokin siyasa da mulki.

Obafemi Hamzat - Legas

Obafemi Hamzat

Asalin hoton, Obafemi Hamzat/X

Kadri Obafemi Hamzat, wanda aka haifa a ranar 19 ga watan Satumbar 1964 ɗan siyasa ne wanda ke riƙe da muƙamin mataimakin gwamnan Jihar Lagos tun shekarar 2019.

Mahaifinsa, marigayi Oba Mufutau Olatunji Hamzat, ya taɓa zama ɗan majalisar dokokin Jihar Lagos da kuma kwamishinan sufuri na jihar (tsakanin 1979 zuwa 1983) kafin ya zama mataimakin shugaba (na yankin Kudu maso Yamma) na jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) a wancan lokacin.

Ya zama shugaban jam'iyyar Action Congress a yankin Lagos ta Yamma, sannan ya zama sarki bisa gadon sarauta daga ɓangaren dangin mahaifiyarsa.

A ranar 21 ga watan Mayun 2026, Obafemi Hamzat ya zama ɗan takarar gwamnan Jihar Lagos a zaɓen shekarar 2027 a ƙarƙashin jam'iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC).

Princess Damilola Sonayon-James ce za ta yi masa takarar mataimakiya.

Uba Sani - Kaduna

Uba Sani

Asalin hoton, Uba Sani group/Facebook

An haifi Uba Sani a ranar 31 ga watan Disambar 1970; injiniya ne kuma ɗan siyasa wanda ke riƙe muƙamin gwamnan Jihar Kaduna tun daga shekarar 2023.

A baya, ya taɓa zama sanatan da ke wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Yana da digiri na biyu (Master of Science) a fannin harkokin kuɗi daga Jami'ar Calabar, da kuma takardar shedar karatu ta gaba da digiri (Post-Graduate Diploma) a fannin gudanar da harkokin kasuwanci daga Jami'ar Abuja.

Comrade Jerry Adams ne zai yi masa takarar mataimaki.

Abba Kabir Yusuf - Kano

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, Kano State Government

Abba Kabir Yusuf ɗan siyasa ne wanda ke riƙe da muƙamin gwamnan Jihar Kano tun watan Mayun 2023. Ya taɓa zama kwamishinan ayyuka, gidaje, da Sufuri a Majalisar zartaswa ta Jihar Kano tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015, a lokacin gwamnatin Rabi'u Musa Kwankwaso.

Ya sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC a shekarar 2026, inda ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda buƙatar samun haɗin kai da kuma kawo ci gaba ga al'umma.

Ya zaɓi mataimakinsa, Murtala Sule Galadima Garo, a matsayin abokin takararsa a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Dikko Umar Radda - Katsina

Dikko Umar Radda

Asalin hoton, Dikko Umar Radda

Dikko Umar Radda masanin tattalin arziki ne kuma ɗan siyasa.

An zaɓe shi a matsayin gwamnan Jihar Katsina a zaɓen gwamnoni na Najeriya na shekarar 2023.

A baya, ya taɓa riƙe muƙamin Darakta-Janar na Hukumar Raya Ƙananan Masana'antu da Masu Matsakaicin Girma ta Najeriya (SMEDAN).

Ya samu digirinsa na biyu a fannin Faɗaɗa aikin gona da ilimin zamantakewar al'ummar karkara daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Mataimakin gwamnan Jihar mai ci Faruk Lawal Jobe ne za yi masa takarar mataimaki.

Kingsley Chinda - Rivers

Kingsley Chinda

Asalin hoton, Rep. Ogundu Kingsley Chinda/FB

An haifi Kingsley Ogundu Chinda a ranar 24 ga watan Maris na shekarar 1966; ɗan siyasa ne kuma ɗaya daga cikin ƴan majalisar dokokin tarayyar Najeriya. A halin yanzu, yana wakiltar mazaɓar Obio/Akpor a Majalisar Wakilai ta Tarayya.

A ranar 21 ga watan Mayun 2026, Chinda ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Rivers a ƙarƙashin jam'iyyar APC, bayan da Siminalayi Fubara, wanda shi ne gwamnan jihar Rivers a lokacin, ya janye daga takarar.

Shugaban Masu Rinjaye na majalisar dokokin jihar Rivers Major Jack shi ne zai yi masa takarar mataimaki.

Sheriff Oborevwori - Delta

Sheriff Oborevwori

Asalin hoton, Sheriff Oborevwori

Sheriff Francis Orohwedor Oborevwori ɗan siyasa ne da ke riƙe da muƙamin gwamnan Jihar Delta tun daga shekarar 2023.

A baya, ya taɓa zama kakakin majalisar dokokin Jihar Delta, inda ya wakilci mazaɓar Okpe ta jihar a ƙarƙashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Abokin takarar Sheriff Oborevwori, wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar Delta na yanzu, shi ne Sir Monday Onyeme.

Peter Mbah - Enugu

Peter Mbah

Asalin hoton, Peter Mbah/Facebook

Peter Ndubuisi Mbah lauya ne mai ƙwarewa a fannin shari'ar harkokin sufurin jiragen ruwa, kuma mai nazarin harkokin kuɗi, wanda ke riƙe muƙamin Gwamnan Jihar Enugu tun shekarar 2023.

Shi ne wanda ya kafa kamfanin Pinnacle Oil and Gas Ltd. kuma yake riƙe da muƙamin babban jami'in gudanarwa (CEO) na kamfanin.

Mbah ɗan asalin garin Owo ne da ke cikin ƙaramar hukumar Nkanu ta gabas a Jihar Enugu, Najeriya.

Shi memba ne mai daraja ta musamman a ƙungiyar Certified Institute of Public Administration and Management (CIPM), haka kuma memba ne na ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA).

Abokin takarar Peter Mbah shi ne Ifeanyi Ossai, wanda ke riƙe da muƙamin mataimakin gwamnan Jihar Enugu.

Jamilu Gwamna - Gombe

Dr. Jamil Isiyaku Gwamna

Asalin hoton, Dr. Jamil Isiyaku Gwamna/FB

Jamilu Isiyaku Gwamna ɗaya ne daga cikin matasan ƴan siyasa a Jihar Gombe. Ya yi fice ne ta hanyar shiga harkokin siyasa.

A tsawon shekaru, ya kasance mai goyon bayan manufofin jam'iyyar APC tare da taka rawa a shirye-shiryen siyasa da na matasa.

Ya kasance tsohon shugaban kamfanin raraba wutar lantarki na KEDCO mai kula da shiyyar Kano.

Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin sabbin jinin siyasar Gombe, musamman saboda kusancinsa da al'umma da kuma yadda yake bayyana ra'ayoyinsa kan batutuwa da dama.

Mustapha Gubio - Borno

Mustapha Gubio

Asalin hoton, Mustapha Gubio/FB

Mustapha Gubio ɗan siyasa ne a jihar Borno wanda ya taɓa riƙe muƙamai daban-daban a gwamnati.

Ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Harkokin Kuɗi na Jihar Borno, inda ya taka rawa wajen tsara da kuma gudanar da harkokin kuɗin jihar.

Haka kuma ya yi aiki a wasu muhimman fannoni na gwamnati da suka shafi tsare-tsare da gudanarwa.

Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin matasan jiga-jigan APC masu tasowa a jihar Borno.

Gubio ya fito daga ƙaramar hukumar Gubio, kuma ya daɗe yana cikin harkokin siyasa da mulki a jihar.

A fagen siyasa, magoya bayansa na kallonsa a matsayin mutum mai ƙwarewa a harkokin kuɗi da gudanar da gwamnati, lamarin da ya sa sunansa ke fitowa cikin waɗanda ake ambata a tattaunawar siyasar Borno.

Mohammed Abubakar - Bauchi

Mohammed Abubakar

Asalin hoton, Mohammed Abubakar/FB

Mohammed Abdullahi Abubakar lauya ne kuma ɗan siyasa a jihar Bauchi.

Ya kasance gwamnan jihar Bauchi daga shekarar 2015 zuwa 2019, bayan ya yi nasara a zaɓen da ya gudana ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Kafin zamansa gwamna, ya yi aiki a fannoni daban-daban na harkokin shari'a da gudanarwa a matakin jiha da tarayya.

Bayan shan kaye a zaɓen 2019 ya ci gaba da kasancewa cikin manyan jiga-jigan siyasar Bauchi.

Mohammed Abubakar na daga cikin fitattun 'yan siyasa a Arewa maso Gabas, kuma yana da tasiri a harkokin APC a jihar Bauchi.

Aliyu Wadada - Nasarawa

Aliyu Wadada

Asalin hoton, Aliyu Wadada/FB

Sanata Aliyu Ahmed Wadada na daga cikin fitattun ƴan siyasa a Jihar Nasarawa.

Wadada ya wakilci mazaɓar Keffi/Kokona/Karu a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga 2011 zuwa 2019.

Bayan haka, a zaɓen 2023 ya lashe kujerar Sanatan Nasarawa ta Yamma inda yake wakiltar mazabar a Majalisar Dattawa.

A tsawon rayuwarsa ta siyasa, ya yi aiki a jam'iyyu daban-daban kafin ya koma APC.

Wadada na dogara ne da gogewarsa a majalisar dokoki da kuma tasirinsa a siyasar Nasarawa wajen neman goyon bayan masu kaɗa ƙuri'a idan ya shiga takarar gwamna.

Caleb Mutfwang - Plateau

Caleb Muftwang

Asalin hoton, Caleb Muftwang

Caleb Mutfwang lauya ne kuma ɗan siyasa, ɗan asalin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Ya taɓa zama shugaban ƙaramar hukumar Mangu na tsawon shekaru biyu, kafin daga baya ya kasance cikin manyan jiga-jigan siyasa a jihar Plateau, yana taka rawa a harkokin jam'iyya da shugabanci.

A shekarar 2023 ya lashe zaɓen gwamnan jihar Plateau, inda ya hau mulki a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, kafin ya sauya sheƙa zuwa APC a farkon shekarar da muke ciki.

Ana kallon Mutfwang a matsayin ɗaya daga cikin fitattun 'yan siyasar Plateau masu tasiri.

Yakubu Danladi Salihu - Kwara

Yakubu Danladi Salihu

Asalin hoton, Yakubu Danladi Salihu/FB

Yakubu Danladi Salihu ɗan siyasa ne daga jihar Kwara kuma mataimakin gwamnan jihar ƙarƙashin gwamnatin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.

Ya fito daga ƙaramar hukumar Ilesha-Baruba da ke yankin Kwara ta Arewa, kuma ya kasance cikin fitattun jiga-jigan APC a jihar.

Kafin hawansa kujerar mataimakin gwamna a shekarar 2019, Yakubu Danladi ya taka rawa a harkokin siyasa da gudanarwa a matakin jiha.

Gogewarsa a harkokin mulki da kuma tasirinsa a siyasar Kwara sun sanya shi cikin fitattun sunayen da ke amo a siyasar jihar.

Sauran ƴantakarar

  • Solomon Adeola - Ogun
  • Sharafadeen Alli - Oyo
  • Eric Opah - Abia
  • Baba Malam Wali - Yobe
  • Hyacinth Alia - Benue
  • Bassey Otu - Cross River
  • Francis Nwifuru - Ebonyi
  • Peter Mbah - Enugu
  • Umar Namadi - Jigawa
  • Ahmed Galadima - Adamawa
  • Umar Bago - Niger
  • Nasir Idris - Kebbi
  • Umo Eno - Akwa Ibom
  • Dauda Lawal - Zamfara
  • Ahmed Aliyu - Sokoto