Messi ya yi ritaya

Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Kyaftin ɗin Argentina Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa da ƙasa, inda ya bayyana cewa wannan mataki ya sosa masa rai amma ya yi la'akari da cewa "lokaci ya yi".

Ɗan wasan mai shekara 39, wanda ya jagoranci Argentina wajen lashe Kofin Duniya a Qatar a shekarar 2022, ya zura Ƙwallaye 125 a wasanni 207 da ya buga, lamarin da ya sanya shi zama ɗan wasan Argentina da ya fi kowa yawan zura ƙwallaye da kuma yawan buga wa ƙasar wasa a tarihi.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Messi ya ce ya bayar da dukkan ƙarfinsa ga tawagar ƙasar, amma yanzu "ba shi da sauran abin da zai bayar".

Messi ya zamo ɗanwasan Argentina da ya fi ɗaukar hankali a gasar kofin duniya ta 2026.

Messi ya shafe kusan shekara 20 yana jan zaren shi a wasan ƙwallo.

A cikin waɗannan shekarun, ya lashe kyautar gwarzon ɗanwasa ta Ballon d'Or har takwas, ya ci gasar ƙasashen Sifaniya da Faransa, da gasar zakarun Turai da Copa America da kuma kofin duniya a 2022, yayin da ya kafa wani tarihin a fannin cin ƙallaye da yawa.

Masu goyon bayan shi suna kuma nuna ƙwarewar shi wajen iya taka leda a duk inda ya samu kanshi, daga yadda Barcelona ta mamaye Turai zuwa kane-kanen da Argentina ta yi a fagen ƙwallon ƙafa a duniya.

Masoyan Messi su na ganin ƙarkon da ya yi, da basirar shi da gudunmuwar da ya ke bayarwa wajen samun nasarar ƙungiyoyin shi, su ne bambancin shi da sauran ƴanwasa da aka yi a tarihi.

Wane ne Messi a tawagar Argentina?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya zama ƙyaftin a watan Agusta 2011. Daga nan ne tawagar ta fara jerin rashin nasara a wasanninta. Gasar Kofin Duniya ta 2014, Argentina ta sha kashi a hannun Jamus a ƙarin lokaci a wasan ƙarshe a Maracanã. Sannan a Copa America a 2015, Chile ta doke su a bugun daga kai sai mai tsaron raga. Haka kuma Copa America a 2016 ta sake rashin nasara a hannun Chile ta hanyar bugun fanariti.

Wasannin ƙarshe uku cikin shekaru uku, duk sun ƙare da rashin nasara, bayan da tun farko an ɗora buri a kansa. A lokacin wasu ke cewa ya fi mayar da hankali da sa ƙwazo a Barcelona fiye da a wasannin Argentina.

Hakan ya tunzara Messi da ta kai ya yi murabus daga tawagar. Amma daga baya ya dawo ci gaba da wakiltar kasar, bayan da aka rarrashe shi. Sai dai ya riga ya canza salon wasanninsa.

A Copa America a 2019, inda aka fitar da Argentina a hannun Brazil a wasan kusa da na ƙarshe cikin cece-kuce, Messi ya shiga taron manema labarai inda ya soki hukumar ƙwallon ƙafa ta Kudancin Amurka sosai.

Wannan ba shi ne ɗan wasan da yake yin shiru baya magana ga duk hukuncin da za a yanke wa Argentina a lokacin wasanninta. Sai kawai ya yanke shawarar daina barin abin da aka yi wa tawagar idan har na rashin adalci ne.

Copa America a 2021 ta zama lokacin da Argentina ta doke Brazil a wasan ƙarshe a Maracanã, ta kuma kawo ƙarshen shekara 28 ba tare da lashe manyan kofi ba a tarihinta. Jawabin da Messi ya yi kafin wasan ya sa ɗakin manema labarai ya cika da hawaye.

Messi a gasar Kofin Duniya a 2022 ya zama wani sabon ɗan wasa gaba ɗaya—da yadda ya yi jagoranci.

Akwai wani gudu da ya yi har ma ya wuce Josko Gvardiol a wasan kusa da na ƙarshe da Croatia, kai kace kamar tsohon Messi na 2009 ne ya dawo na ɗan lokaci.

Akwai kuma ƙwarewar jagoranci a wasan ƙarshe da Faransa—inda ya bayar da ƙwallo ga Nahuel Molina, sannan ya yi wani gudu da ya taimaka aka ci ƙwallo ta uku, sannan ya ci fanareti a lokacin da komai ke kan hanyar ɗaukar kofin.

"Ƙwallon ƙafa ya canza sosai," in ji shi a wata hira da Zinedine Zidane a 2023. "Hanyar wasa, tsarin dabara. Yanzu wasan ya fi dogaro da dabaru da ƙarfin jiki fiye da a baya. A can bya akwai sarari da yawa."