Me ya sa fim ɗin Ƙaddara ya samu karɓuwa?

Kaddara

Asalin hoton, Abdul Amart

Lokacin karatu: Minti 3

Ana ci gaba da tattaunawa a duniyar fina-finan Hausa musamman a kafofin sadarwa a game da fim ɗin 'Ƙaddara'.

Abdul Amart ne ya shirya fim ɗin, sannan fitaccen darakta, Falalu Ɗorayi ya bayar a umarni.

Wani abu da ya ja hankalin mutane a game da fim ɗin shi ne irin rawar da jaruma Nafisa Abdullahi ta taka tare da Adam A. Zango, inda suka fito a matsayin mata da miji.

Fitowa ta farko a zango na farko na fim ɗin, wanda aka fara fitarwa a YouTube a ranar 12 ga Afrilu ya samu masu kallo 821,075 a kimanin kwana 10.

Sai fitowa ta biyu da aka fitar a ranar 19 ga watan Afrilu ya samu masu kallo 603,242 zuwa ranar haɗa wannan rahoton.

Fim ne da aka shirya yadda Adam Zango da ya fito da sunan Haidar ya taka rawar mijin Nafisa, wadda ta fito a matsayin Maimuna a shirin.

Shi Haidar ya fito a matsayin mai tsantsar kishi da zargin matarsa, inda har ya kafa mata sharaɗin haƙura da aiki da mu'amala da wasu, duk da cewa ta ce ba ta iya haƙura da kafofin sadarwa ba.

Daga ƙarshe dai Maimuna ta gaji da haƙuri, inda ta daddage ta zabga wa Haidar mari.

Tsakuren daidai marin ne ya yi ta yawo a kafofin sadarwa, har ya ƙara tallata shirin, ya sa aka ci gaba da tattaunawa a kafofin sadarwa.

Me ak yi na daban a Ƙaddara?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr. Muhsin Ibrahim, malami ne a Jami'ar Cologne da ke Jamus, kuma fitaccen mai sharhi kan harkokin fina-finai, musamman Kannywood, ya bayyana cewa akwai wasu abubuwa guda huɗu da suka taimaka wajen ba fim ɗin tagomashi:

  • Nafisa tsawon shekaru ba a ganta a sabon fim ba, kuma an san ƙwararriya ce mai farin jini. To mutane suna so ga irin rawar da za ta taka. Musamman ta yi takanas daga Amurka zuwa Najeriya domin fitowa a fim ɗin.
  • Alaƙar da ke tsakanin da Adam Zango da Nafisa a baya ta taimaka. An daɗe ba a gan su tare ba, sai mutane suke son ganin rawar da za su taka.
  • Kamfanin Abnur ya kasance kamfani ne da aka san yana shirya fina-finan.
  • Jigon labarin ya zama daban. Fim ɗin ya zo a daidai lokacin da aka daɗe ba a ga irinsa ba.

A nasa ɓangaren, daraktan fim ɗin, Falalu Ɗorayi ya ce yanayin yadda fim ɗin ya fito da abubuwan da suka shafi mata ya taimaka matuƙa wajen ƙara isar da saƙon.

"Fim na samun karɓuwa ne idan ya taɓa abin da ya shafi mutane, musamman mata waɗanda su ne kusan kashi 60 na masu kallon fim. Sannan idan ya taɓa matsalolin auratayya da cin zarafi da soyayya da ƙalubalen su da rashin daidaito da sauransu. Kusan duk Ƙaddara ya taɓo waɗannan abubuwa."

Falalu ya ƙara da cewa fim ɗin ya taɓo abubuwan da suka shafi addini da al'adu.

"Gaskiya mu a fina-finanmu muna ƙoƙarin saka al'adu domin tafiya tare da masaa da masu binciken adabi, da kuma Hausawa da ke ƙasashen saboda su riƙa ganin abubuwan al'adu da ba sa gani a ƙasashen waje."

'Da na gaba ake gane zurfin ruwa'

Babban abin da ya ja hankali shi ne muhawarar da ake yi cewa lallai tsofaffin jarumai sun nuna ƙwarewa a shirin, inda tuni wasu suke fara cewa lallai da tsohuwar zuma ake magani.

A game da wannan, Dr Muhsin ya ce jaruman baya da na yanzu kowa na ƙoƙari, "amma lallai an ce duk wanda ya riga kwanciya, zai riga ka tashi. Don sababbin jaruman su riƙa kallon tsofaffin jarumai suna koyon darasi."

Shi ma Falalu Ɗorayi ya ce dama can kowa ya san Zango da Nafisa jarumai ne ƙwararru, sannan sun fahimci juna sosai wajen taka rawa a fim.

Falalu Ɗorayi ya ƙara da cewa babban abin da ake buƙata a fim shi ne a samu ingantaccen labari da darakta mai kyau, sannan a samu jarumai gwanaye, "wannan haɗakar ce take fitowa da fim sosai."