Yadda INEC ke neman wanke shugabanta kan zargin goyon bayan APC

Asalin hoton, INEC
Hukumar zaben Najeriya, INEC ta ce wani binciken kwakwaf da kwararru suka gudanar sun tabbatar da zargin da ake yi wa shugabanta Farfesa Joash Amupitan da alhakin wallafa bayanan da suka danganta shi da jam'iyyar APC mai mulki cewa kirkirarsu aka yi.
A wani bayani da hukumar ta fitar ta ce wani kwararre da ta yi hayarsa ya gudanar da bincike tare da gano cewa an rarraba bayanan na bogi ga jama'a domin bata wa shugaban nata suna.
Kimanin mako biyu kenan da suka gabata bayan da aka bankado wani shafin X (Twitter) mai dauke da sunan shugaban hukumar ta INEC, Joash Ojo Amupitan, da ake zargin nasa ne, inda aka ce ya wallafa wasu ra'ayoyi da suke nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu da jam'iyya mai mulki ta APC a 2023.
Duk da yake hukumar zaben ta musanta zargin, da ta ce Amupitan ba shi da shafi a X, wasu da suka ce sun yi binciken kwakwaf ciki har da jaridar Daily Trust da fitaccen marubucin nan Farfesa Farooq Kperogi ya wallafa wani abu da 'yan Najeriya suka kalla a matsayin tonan asiri ga shugaban na INEC.
A shafinsa na X Farfesa Kperogi ya wallafa cewa bayan bin diddigi na shekara da shekaru na wallafe-wallafen da Amupitan ya yi a shafinsa na X ya gano cewa mutumin da aka nada ya jagoranci INEC "ɗan jam'iyyar APC ne" kuma mai goyon bayan Shugaba Tinubu, bayan gano lambar waya da kuma adireshin imel masu alaka da shafin, wadanda suka ce sun yi daidai da na shugaban na INEC.
A yanzu dai hukumar zaben ta bayyana cewa wannan shafin an jirkita shi ne da sunan yin sojan-gona domin ya bata sunan shugabanta.
Ta ce a yanzu ta dauko hayar wasu kwararru da suka gudanar da binciken kwakwaf da ya kai ga gano cewa shafukan X da ma na Facebook da aka alakanta da Amupitan ba nasa ba ne.
Kuma ta sha alwashin gurfanar da masu hannu a wannan lamari a gaban kotu.
Sai dai BBC ta tuntubi Umar Sale Gwani wani kwararre a kan shafukan sada zumunta da kuma binciken kwakwaf a kan yadda ake gane irin wadannan bayanai, inda ya ce:
''Wadannan na'urori da kuma manhajoji da ake amfani da su wajen irin wadannan bincike din sanannun na'urori ne a duniya, wanda kuma babu tantama ko jayayya a kan yadda ake bincike a gano watakila ko an yi amfani da wayar hannu ko an yi da kwamfuta ko kuma wani abu wanda yake da alaka da akawunt na mutum a irin wadannan shafuka a sada zumunta din.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kazalika, dangane da bangarorin da ya dace su gudanar da wannan bincike har ya zama karbabbe kwararren ya ce:
''Wato kamar su jam'iyyu na siyasa da suka mika korafinsu a kan wadannan zarge-zarge, ya kasance su ma sun samo nasu masu ilimin sun yi nasu binciken wanda kuma zai iya hadawa har da samun umarnin kotu don a tantance a kuma samu biyan bukata.
''Yanzu ai hukumar zabe ita ta dauki wadanda suka yi wannan bincike kuma biyansu za ta yi. Saboda haka ba lalle ba ne wannan sakamako da suka bada babu wani abu na akasin haka din.''
A cikin ƴan makonnin nan muhawarar ta kaure a fili da kuma shafukan sada zumunta a Najeriya bisa zargin Amupitan da cewa ya taɓa nuna goyon baya ga jam'iyyar APC mai mulk, zargin da hukumar ta musanta.
Wannan matsi da sabon shugaban na INEC ke fuskanta abu ne da ba a saba gani a baya-bayan nan ba, kasancewar akasarin ƴan Najeriya na yi wa shugabannin hukumar da suka shuɗe kallon masu mutunci da kuma tsayawa a tsakiya ba tare na nuna goyon bayan wata jam'iyya ko dan siyasa ba.
A makon da ya gabata ma jam'iyyar ADC mai hamayya ta mika wa hukumar zaben takardar neman Amupitan ya sauka daga muƙaminsa, bisa zargin cewa ba zai iya gudanar da sahihin zaɓe cikin adalci ba.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC, a watan Oktoban 2025, bayan ƙarewar wa'adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya shugabanci hukumar tsawon shekara 10.











