Maharashtra: Garin da wasu tuzurai ke kashe kansu saboda rashin samun aure a India

- Marubuci, Aashay Yedge
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Marathi
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Bayanan ƴansandan Maharashtra sun nuna cewa maza 383 ne suka kashe kansu a gundumar Jalgaon cikin wata shida, daga ranar 1 ga Janairu zuwa 30 ga Yuni 2026.
Binciken ƴansanda ya gano dalilai da dama da suka haddasa waɗannan kashe-kashen kai, ciki har da shan miyagun ƙwayoyi, damuwa ta tunani, matsalolin iyali da kuma basussuka.
Ƴansandan sun ce a cikin waɗanda suka kashe kansu, 29 rashin samun wadda za su aura ne ya kasance dalilin kashe kansu.
Bayan bayyana waɗannan alƙaluman, an fara muhawara sosai kan matsalar matasan maza a Jalgaon na rashin samun matan aure.
Ya kamata a yi aure a lokacin da ya dace
A Jalgaon, na gana da Vishal Patil, wani farfesa mai shekara 30, wanda ya yi magana kan batun aure ta hanyar da ta yi daidai da irin abubuwan da matasa da dama ke fuskanta.
Ya ce: "Iyayena ma suna son in yi aure. Sai dai ni ina ɗan jinkirta hakan. Ina son mayar da hankali kan aikina kuma in samu damar dogaro da kaina ta fuskar kuɗi. Zan yi aure ne kawai idan na samu macen da za ta fahimce ni kuma ta dace da ni," in ji shi.
Vishal ya ce al'umma ta sanya wani takamaiman shekara da ake ganin ya kamata mutum ya yi aure.
A cewar Vishal: "A cikin al'ummar Indiya, ana sa ran mutum ya yi aure kafin ya kai shekara 24 zuwa 26, ko kuma aƙalla kafin ya kai 28 zuwa 29. Da zarar mutum ya haura shekara 30, mutane kan fara kallonsa da wani irin kallo. Wannan matsin lamba ba wai kawai yana da alaƙa da rashin yin aure ba ne. A hankali, mutum na iya fara jin cewa akwai wani abu da ya rasa ko kuma ya gaza a rayuwa saboda bai yi aure ba."

"Maza sun fi mata yawa"
Bayanan da aka samu daga jihar Maharashtra sun bayyana wani sabon salo wajen fahimtar wannan matsala.
A cewar bayanan, binciken kiwon lafiyar iyali na ƙasa (NFHS-5) na tsakanin 2019 zuwa 2021, ya nuna cewa kusan kashi 11 cikin 100 na matan da shekarunsu ke tsakanin 20 zuwa 49 a Maharashtra ba su yi aure ba, yayin da adadin mazan da ba su yi aure ba ya kai kusan kashi 30 cikin 100.
Wannan na nuna cewa adadin mazan da ba su yi aure ba a jihar ya fi na mata sosai. Amma shin ƙarancin mata ne kaɗai ke haifar da wannan matsala?
Lamarin Kaustubh Potdar daga Jalgaon ya amsa tambayar.
Bayan kammala karatunsa na B. Pharma, ya samu aiki a wani kamfani mai zaman kansa a Nashik. Bayan rasuwar mahaifiyarsa, ƴan'uwansa sai suka fara neman matar da ta dace domin ya aura.
A cewarsu, mata daga wurare da dama sun ƙi amincewa da aurensa saboda ba shi da aikin gwamnati, kuma ba shi da gida.
Ya kashe kansa a watan Fabrairun 2026.

Gina gida na da muhimmanci wajen samun aure
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata tsohuwa da na gana da ita a Jalgaon ta faɗa min cewa ɗanta yanzu yana da shekara 40, kuma shekaru da dama ke nan tana neman masa matar da zai aura.
Bayan rashin nasara, yanzu ita da kanta take gina masa gida. Tana fatan cewa "da zarar an kammala gidan, zai samu mata."
Wannan sauyi ya kuma bayyana a wani bincike da Mayur Kudupalle da Joel Cabalian suka gudanar kan yankunan karkara na Maharashtra. Binciken nasu ya gano cewa mallakar ƙasa da ilimi da manufar rayuwa da shekaru su ne manyan abubuwan da ke tasiri wajen neman aure a yankunan karkara.
Mayur Kudupalle ya ce: "A da, mahaifin yarinya zai duba yawan gonar da wanda zai auri ƴarsa ya mallaka. Yanzu, abin da ya fi muhimmanci fiye da mallakar ƙasa shi ne ko yana da aiki ko babu."
A cewarsa, "Tattalin arzikin karkara ya sauya, amma abubuwan da mutane suke sa ran samu a batun aure ba su sauya ba. A da, mallakar ƙasa alama ce ta samun kwanciyar hankali ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki. Yanzu kuma abubuwa kamar samun kuɗin shiga na yau da kullum, samun aiki, damar zama a birni da kuma mallakar gida sun fi muhimmanci."
Buƙatun aure na sauyawa

A cewar Mayur Kudupalle, a yanzu mallakar ƙasa kaɗai ba ta isa a samu aure ba; iyalan yarinya suna neman ango mai aikin dindindin.
Darshana Pawar, mai horas da mutane kan daidaiton jinsi, ta nuna wani saɓani da ke tattare da wannan tsarin.
Ta ce: "Idan namiji ya ga cewa yana buƙatar yin aure, yana iya kasancewa a shirye ya auri mace daga kowace irin gado. Amma shin ita mace fa?
Ra'ayin mata
Yayin da muke tattaunawa da maza a Jalgaon, ƙorafi guda da aka fi maimaita shi ne cewa "abubuwan da mata suke buƙata sun ƙaru."
Mutane da dama sun yi imanin cewa mata suna son abokin aure wanda yake da aiki, ya mallaki gida a birni kuma yake da wadataccen yanayin kuɗi.
Sai dai tattaunawar da muka yi da mata ta nuna wani yanayi na daban. Mun tattauna da wata budurwa ƴar shekaru 20 zuwa 22 game da abubuwan da ita da kanta take sa ran samu a aure.
Sai dai washegari bayan hirar, iyayenta su nemi kada a yi amfani da wannan tattaunawar.
Haƙiƙa, abubuwan da mata suke sa ran samu sun sauya, amma ba kowa ce ke da damar bayyana waɗannan ra'ayoyin a fili ba.
Darshana Pawar ta ce: "Ba laifi ba ne mace ta buƙaci samun lokacin tattaunawa da mijinta, ta fita tare da shi, kuma su kasance suna ba juna lokaci. Waɗannan ba ƙarin buƙatu ba ne; buri ne na asali ne kuma halastattu. Abin da ya faru kawai shi ne yanzu wayar da kan mutane game da waɗannan abubuwa na ƙaruwa."
Yawancin mazan da muka tattauna da su a Jalgaon sun ɗora alhakin rashin samun aure ne kacokan kan mata.
Binciken Mayur Kudupalle ma ya gano irin waɗannan korafe-korafen daga mazan yankunan karkara game da sauyin abubuwan da mata suke so.
Sai dai bincike ya nuna cewa ba za a iya kallon waɗannan sauye-sauye a matsayin sauyin abubuwan da mata suke sa ran samu kaɗai ba.

Yaya matsayar mazan?
A ƙauyukan Jalgaon, duk lokacin da muka fara batun aure, yanayin maganar mazan kan sauya. Wasu ma gaba ɗaya ba sa son a ɗauke su a hoto suna magana kan wannan batu.
Wani matashi ya ce: "Idan na yi magana game da kaina aka ɗauka, wace ce za ta amince ta aure ni?"
Iyalai da dama yanzu sun daina matsa wa ƴaƴansu maza su yi aure, wataƙila saboda sun yanke ƙauna bayan shekaru da suka kwashe suna ƙoƙari ba tare da nasara ba.
Sai dai har yanzu wasu iyalai suna ci gaba da gina gidaje, sayen filaye ko ƙoƙarin inganta yanayin kuɗinsu domin su samu wadda za ta auri ƴaƴansu maza.
A cewar wasu iyaye, abubuwan da suka shafi damfara da sunan shirya aure ma sun ƙaru.
Wasu maza suna tafiya sassa daban-daban na Maharashtra suna neman abokiyar rayuwa, yayin da wasu iyalai ma suke shirye su biya kuɗi domin samun amarya.
Daga zubar da cikin mata zuwa fafutika

Asalin hoton, RAVEENDRAN/AFP via Getty Images
A cewar Darshana Pawar: "Tasirin yawaitar zubar da cikin ƴaƴa mata a cikin shekarun da suka gabata yanzu yana bayyana a cikin wannan ƙarni na mazan da suka kai shekarun yin aure."
Ta ce: "Mazan da ke tsakanin shekara 30 zuwa 35 da a yanzu suke fuskantar matsalar samun abokiyar rayuwa, an haife su ne a lokacin da ake zubar da da cikin mafi yawan ƴaƴa mata. Sai dai raguwar yawan mata ba ya nufin cewa yanzu mata sun samu cikakken ikon yanke hukunci na ƙarshe kan aure."
A cewar wani bincike da Mayur Kudupalle da Joel Cabalian suka gudanar, ikon mata na yanke shawara ya ƙaru zuwa wani matsayi, amma har yanzu yana aiki ne a cikin tsarin iyaye da tsarin gado da matsin lambar al'umma.











