Ƴan Afirka bakwai da za su taka rawar gani a Gasar Kofin Duniya 2026

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 8

A karon farko a tarihi kasa 10 ce daga Afirka za ta shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 da za a buga tsakanin tawaga 48, inda ake sa ran fitattun ƴan wasa da za su fatan ɗaga kofin.

Morocco ta kafa tarihi a Qatar a 2022, shekara hudu baya da ta zama ta farko daga Afirka da ta kai zagayen daf da karshe.

Cape Verde za ta fara halartar gasar a karon farko a tarihi, yayin da Jamhuriyar Congo za ta sake buga wasannin tun bayan 1974.

BBC ta zaƙulo muku ƴan wasa bakwai daga Afirka da za a saka ido a kansu a lokacin gasar da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli.

Antoine Semenyo (Ghana)

Dan wasan da aka haifa a birnin London bai samu damar lashe kofin Premier League tare da Manchester City ba, amma rawar da ya ta ka ce ta kai ga cin Chelsea a FA Cup da City ta ɗauki kofin a watan da ya gabata.

Mai shekara 26 zai shiga gasar Kofin Duniya ne bayan rawar da ya taka a fannin zura ƙwallaye, inda ya ci 17 a gasar Premier League da ta wuce. Bakwai daga cikin su bayan komawarsa Manchester City a watan Janairu, sauran a Bournemouth ya ci.

Ana sa ran Semenyo zai ɗauki ragamar jan tawagar Ghana, musamman ganin cewa wani fitaccen ɗan wasan ƙasar a Premier League, Mohammed Kudus na Tottenham, ba zai buga gasar ba saboda jinya da yake fama.

Tsohon ɗan wasan Bournemouth din ya buga wa Ghana gasar kofin duniya a Qatar a 2022, kenan karo na biyu zai yi wasannnin, koda yake a farko bai taka rawar gani ba, inda ya rika shiga yana canjin ƴan wasa yayin da Black Stars ta fice tun daga matakin rukuni.

Bayan Ghana ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025 (AFCON), Semenyo zai yi fatan zura ƙwallonsa ta farko a wata babbar gasa a duniya, yayin da Ghana za ta kara da Ingila da Croatia da Panama a wasannin cikin rukuni a gasar ta kofin duniya ta 2026.

Yan Diomande (Ivory Coast)

Tawagar Ivory Coast, wadda za ta sake buga gasar kofin duniya tun bayan 2014, tana alfahari da ɗaya daga cikin fitattun matasan ƴan wasanta da ke taka leda a gasar Bundesliga ta Jamus.

Ɗan ƙwallon mai shekara 19 ya lashe ƙyauta mafi ƙyawun matashin gasar Bundesliga, bayan da ya zura kwallo 12 tare da bayar da takwas aka zura a raga, abin da ya taimaka wa RB Leipzig ta kare a matsayi na uku tare da samun gurbin shiga gasar UEFA Champions League na baɗi.

Wannan bajinta tasa manyan ƙungiyoyi irin su Liverpool da Chelsea ke nuna sha'awar sayensa kan kuɗi masu yawa.

Diomande, wanda ya fara buga tawagarsa wasa huɗu cikin biyar a Afcon 2025, shi ne wanda ya fi yin kokarin wuce abokan hamayya da ƙwallo (dribbles) tare da bajintar iya kwace a Bundesliga a kakar 2025/26.

Kwarewarsa a yanayin mutum da mutum tana sa ya zama babban barazana ga kowace ƙungiya ko tawaga, musamman a bangaren kai hare-hare.

Saboda haka, abokan karawarsu a rukunin da ya haɗa da Jamus, sun san irin haɗarin da yake a garesu. Ivory Coast kuma za ta kara da Ecuador da kuma Curacao, wadda ke shiga gasar Kofin Duniya a karon farko a tarihinta.

Ronwen Williams (Afirka ta Kudu)

Afirka ta Kudu ta dawo buga gasar Kofin Duniya a karon farko tun bayan da ta karɓi bakuncin wasannin a shekarar 2010, inda babban burinta shi ne ta tsallake matakin rukuni—abin da ƙasar "Bafana Bafana" ba ta taɓa cimmawa ba a tarihinta kenan.

Tawagar ta sha fuskantar yin ban kwana da gasar tun da wuri, ciki har da gasar 1998 da 2002, sannan kuma ta zama ƙasa ta farko mai masaukin baki da ta kasa wuce matakin farko a cikin rukuni a gasar.

Tawagar tana da ƴan wasa daga ƙungiyar Mamelodi Sundowns, wacce ke taka rawar gani a ƙwallon ƙafa a Afirka, ita ce ginshiƙin tawagar. Akwai mai tsaron gida kuma kyaftin, Ronwen Williams, wanda ya yi fice saboda bajintar sa wajen tare bugun fenariti, bayan da ya hana kwallaye huɗu a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da suka yi da Cape Verde a zagayen kwata-fainal a Afcon 2023.

Williams, mai shekara 34, ya ce yana "daraja mukaminsa na ƙyaftin Sosai", kuma yanzu yana da ƙwarewa mai yawa a manyan wasanni, musamman bayan da ya lashe kofin CAF Champions League tare da Sundowns kwanan nan.

Afirka ta Kudu za ta buɗe wasanta a gasar da mai masaukin baki Mexico a ranar 11 ga watan Yuni, kafin ta kara da Jamhuriyar Czech da kuma Koriya ta Kudu a sauran wasannin cikin rukuni.

Roberto 'Pico' Lopes

Ɗan wasan mai tsaron baya baya ya zama ginshiƙe a ci gaban da ƙaramar ƙasar Cape Verde ta samu a ƴan shekarun nan, inda ta kai zagaye ƴan takwas a Afcon 2023, sannan ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 a rukunin da Kamaru ke ciki - wannan abin ya bai wa mutane mamaki da masu bibiyar tamaula a duniya.

Dan wasan Shamrock Rovers, Roberto Lopes, shi ne aka fara tunkara domin ya buga wa "Blue Sharks" tamaula ta hanyar dandalin sadarwar kasuwanci na LinkedIn, kuma a farko ya yi watsi da sakon saboda an rubuta shi da harshen Portuguese.

Lopes mai shekara 33, wanda aka haifa a Dublin, ya fara bugawa Cape Verde ƙwallo a 2019. Tun daga lokacin ya buga wa kasar dukkan wasannin da ta yi a neman tikitin shiga gasar ta kofin duniya ta bana, yayin da tsibirin da ke cikin Tekun Atlantika ya samu damar shiga gasar Kofin Duniya a karon farko a tarihinsa.

Cape Verde za ta fuskanci ƙalubale mai tsanani a rukunin da za ta kara da tsoffin zakarun duniya, Sifaniya da Uruguay da kuma Saudi Arabia. Kwarewa da jagorancin Lopes da ya yi a bayan nan, ana ganin zai taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin ƙasar na yin fice a wannan babban mataki.

Brahim Diaz (Morocco)

Ɗan wasan Real Madrid ya kasance gwarzo a Morocco a gasar AFCON 2025, inda ya zura ƙwall0 biyar, yayin da kasar mai masaukin baki ta kai wasan karshe, amma yanzu yana da wani kuskuren da zai gyara a wannan gasar.

A wani lamari da ba zai manta ba, yayin da wasan karshe ke tafiya babu ci da Senegal, kuma an kusan tashi suka samu fenariti, sai ɗan wasan mai shekara 26 ya fuskanci matsala lokacin da ya yi bugun fenariti ta hanyar Panenka, amma mai tsaron ragar Senegal, Edouard Mendy ya tare kwallon cikin ruwan sanyi.

An ci karo da koma baya a karawar ta hamayya, inda Senegal ta fice daga fili kafin a buga fenaritin daga baya suka dawo aka ci gaba da wasa, har kuma Senegal ta ci 1-0 ta samu lashe kofin a karo na biyu.

Daga baya, hukumar ƙwallon kafar Afirka (CAF) ta hanyar kwamitin ɗaukaka kara ta sake bai wa Morocco kofin, sai dai Senegal itama ta ɗaukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara ta Wasanni (CAS).

Duk da haka, Diaz, wanda ya taba buga wa Sifaniya tamaula ta ƴan kasa da shekara 21 kafin daga baya ya fara wakiltar Morocco a 2024,bayan gasar Kofin Duniya ta Qatar, ana sa ran zai yi amfani da wannan dama wajen neman fansa da gyara kuskurensa.

Morocco za ta fara buga gasar Kofin Duniya da Brazil, wacce ta lashe kofin sau biyar, sannan ta fuskanci Scotland ta kammala da da Haiti a wasan cikin rukuni na uku.

Ismaila Sarr (Senegal)

Ɗan wasan mai shekara 28 yana kan ganiya, wanda ya zura ƙwallo 21 a wannan kakar, inda shi ne mafi yawa da ya taɓa ci a rayuwarsa ta ƙwallon kafa tare da Crystal Palace.

Daga cikin waɗannan ƙwallaye, tara sun zo ne a gasar Uefa Conference League, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ƙungiyar da ta lashe kofinsu na farko a tarihin Turai.

Sarr na shirin shiga gasar Kofin Duniya a karo na uku a jere, bayan da Senegal ta fice daga gasar 2018 a Rasha a matakin rukuni, sannan kuma ta sha kashi a hannun Ingila da ci 3-0 a zagaye 16 a gasar da ta biyo baya shekara hudu da suka gabata, wato 2022 a Qatar.

Tawagar Teranga Lions, wacce a yanzu ake kallonta a matsayin zakarun Afirka, za ta fafata tawagar Faransa mai kofin duniya biyu da kuma Norway mai Erling Haaland da kuma Iraq.

A tarihi, Senegal ta yi fice sosai a gasar Kofin Duniya, bayan da ta doke zakarun duniya Faransa da ci 1-0 a shekarar 2002 a karon farko da ta shiga gasar, kuma Sarr na fatan maimaita irin wannan bajinta ta hanyar ƙwazon da ya sa a ƙungiyarsa a bana ya ruɓanya wanda zai buga wa kasarsa a gasar tamaula ta duniya.

Omar Marmoush (Masar)

Ɗan wasan mai shekarA 27 bai kai ƙololuwar da aka yi tsammani ba tun bayan komawarsa Manchester City daga Eintracht Frankfurt a watan Janairun bara kan kuɗi kimanin dala miliyan 79.5 (£59m). Duk da haka, Marmoush ya taimaka wa ƙungiyar da Pep Guardiola ya ja ragama wajen lashe Kofin League Cup da FA Cup a wannan kakar.

A kakar 2025-26, ɗan wasan ya fara da buga wasa takwas a Premier League, amma duk da haka yana daga cikin manyan ƴan ƙwallon da kocin tawagar Masar ke dogaro da su a cikin jerin ƴan wasan kasar.

Marmoush ya zura kwallaye biyu a gasar AFCON 2025 da suka kare a mataki na huɗu, kuma yanzu yana fatan taka rawar gani a karon farko da zai halarci babbar gasar tamaula ta duniya.

Ko da yake Masar ce kasa ta farko daga Afirka da ta fara shiga gasar Kofin Duniya, amma har yanzu mai rike da kofin nahiyar Afirka bakwai AfCON, ba ta taɓa cin wasa ba a gasar cin kofin duniya—inda ta sha kashi a zagaye ƴan 16 a 1934, sannan ta fice daga matakin rukuni a 1990 da 2018.

Da yake kyaftin Mohamed Salah ya murmure daga rauni bayan kakar wasa da ba ta yi masa armashi ba a Liverpool a bana, koci, Hossam Hassan na sa ran Marmoush zai taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar tawagar Masar.