Abin da taswirorin duniya ke nunawa daidai da inda suka yi kuskure

- Marubuci, Jaroslav Lukiv
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kiran a sauya taswirar duniya da aka fi amfani da ita a yanzu da wata da za ta fi nuna ainihin girman nahiyoyi kamar Afirka.
Ƙudurin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shi, mai taken "Correct the Map" , na da nufin magance kura-kuran da ke cikin taswirar Mercator, wadda ke nuna Nahiyar Afirka da kusan girman tsibirin Greenland, duk da cewa a zahiri Afirka ta fi Greenland girma kusan sau 14.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da amfani da wata sabuwar taswira mai suna Equal Earth projection, wadda aka ce ta fi bayyana ainihin girman yankunan ƙasa a doron duniya.
Sai dai duk da haka, sabuwar taswirar ma na da nata ƙalubalen.
A tsawon shekaru da dama, an yi ƙoƙari iri-iri daga masana domin samar da taswira da za ta iya wakiltar saman duniya mai siffar ƙwallo a kan shimfiɗar takarda mai faɗi ba tare da karkatar da bayanai ba.
Kowane ɗaya daga cikin waɗannan ƙoƙarin na da nasa fa'idoji da kuma matsalolinsa wajen nuna girma da siffa da nisan wurare a duniya yadda ya kamata.
Taswirar Mercator

Asalin hoton, Getty Images
Taswirar Mercator, wadda a yanzu ta zama ɗaya daga cikin taswirorin da aka fi amfani da su a duniya, ɗan ƙasar Flanders mai ƙera taswira, Gerardus Mercator ne ya ƙirƙire ta a shekarar 1569.
Babbar manufar ƙirƙirarta ita ce taimaka wa matuƙan jiragen ruwa na Turai wajen yin kewaya a cikin tekuna, kamar yadda Farfesa James Cheshire masanin taswira a Jami'ar University College London ya bayyana.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya shaida wa BBC cewa: "Ya so a sami damar zana layi madaidaici a taswira wanda zai kasance madaidaici a zahiri idan mutum ya bi alkiblar kamfas. Wannan ne manufar taswirar, kuma ta yi wannan aiki cikin ƙwarewa sosai."
Domin tabbatar da cewa kusurwoyi sun kasance daidai a kan taswira mai shimfiɗa, Mercator ya tilasta faɗaɗa layukan grid yayin da suke matsowa daga mashigin duniya (equator) zuwa ga turakun duniya (poles).
Saboda haka taswirarsa ta nuna ƙasashen da ke kusa da mashigin duniya kamar sun fi ƙanƙanta fiye da yadda suke a zahiri, yayin da ƙasashen da ke kusa da turakun duniya suke bayyana da girma.
Wannan karkatarwar hoto ta samo asali ne daga rashin yiwuwar wakiltar saman duniya mai siffar ƙwallo daidai a kan taswira mai fuskoki biyu.
Sama da shekaru 450 bayan ƙirƙirar ta, har yanzu taswirar Mercator ce tushen yawancin taswirorin da ake gani a ajujuwan karatu da talabijin da kuma intanet, ciki har da Google Maps.
Sai dai masu suka na cewa irin wannan taswira na da tasirin tunani, domin tana sa wasu wurare su bayyana ƙanana fiye da yadda suke a zahiri, wasu kuma su bayyana manya, alhali mutane kan ɗauki abin da ya fi girma a matsayin mafi muhimmanci.
Ga masanin ƙasa daga Kenya, Kioko Muendo, hakan ya taimaka wajen rage yadda ake kallon yalwar albarkatun Afirka, yawan al'ummarta da kuma damar zuba jari da nahiyar ke da su.
Ya shaida wa BBC cewa: "Taswira ba wai hanya ce kawai da matafiya ke amfani da ita ba. Tana taka rawa wajen tsara yadda ake kallon yankuna ta fuskar siyasa da tattalin arziki."
Taswirar Equal Earth

An ƙirƙiri raswirar Equal Earth domin magance matsalar da ke tattare da taswirar Mercator.
Wasu masana ilimin taswira ne suka ƙirƙiro ta a shekarar 2018 domin nuna girma da siffar yankuna cikin daidaito fiye da yadda ake yi a baya.
An gina tunanin taswirar ne bisa tsarin Robinson projection da aka samar a shekarar 1963, wanda ke ba da damar ganin dukkan faɗin doron duniya a lokaci guda.
Sakamakon haka, ƙasashen membobin Tarayyar Afirka sun amince da amfani da taswirar Equal Earth a watan Fabrairu, kafin daga bisani Majalisar Ɗinkin Duniya ma ta amince da ita.
Sai dai kuma taswirar ta yi watsi da wasu siffofi da suka sa taswirar Mercator ta dace sosai wajen zirga-zirgar ruwa da kewayawa ta hanyar amfani da alkibla.
Haka kuma, ba za a iya amfani da taswirar Equal Earth wajen auna ainihin tazara tsakanin wurare daban-daban a duniya ba.
Masanin ilimin taswira, Cheshire, ya ce:
"Za ka iya kiyaye daidaiton girman yankuna, ko kuma daidaiton siffa, ko kuma daidaiton nisa da alkibla, amma ba za a iya kiyaye dukkan waɗannan abubuwa lokaci guda ba cikin cikakken yanayi. Domin idan hakan zai yiwu, to da za ka koma ga siffar duniya ta asali wato ƙwallo."
Taswirar Peters

Fitaccen masanin tarihin nan na Jamus, Arno Peters ne ya tsara taswirar duniya ta Peters a farkon shekarun 1970.
Taswirar mai siffar murabba'i tana amfani da tsarin da ɗan ƙasar Scotland mai ƙera taswira James Gall ya fara bayyanawa tun a shekarar 1855.
Wannan tsarin taswira ya fifita nuna girman ƙasashe daidai, ko da kuwa hakan zai sa siffofinsu su karkace.
Saboda haka yankunan da ke kusa da turakun duniya suna bayyana a matse, yayin da wuraren da ke kusa da mashigin duniya (equator) suke bayyana a shimfiɗe.
Hakan ya magance matsalar yadda taswirar Mercator ke nuna Greenland kamar tana kusa da girman Afirka, inda taswirar Peters ke bai wa mai kallo damar fahimtar ainihin bambancin girman ƙasashe da nahiyoyi, tare da ci gaba da kiyaye layukan longitude da latitude a tsaye.
Sai dai kuma taswirar tana karkatar da siffofin yankunan duniya sosai, wanda ke sa kusan dukkan ƙasashe su bayyana ba daidai da yadda suke a zahiri ba.
Alal misali, Rasha tana bayyana ƙanƙanta fiye da yadda take a gaske.
Bugu da ƙari, layukan da ke kan taswirar Peters ba sa nuna ainihin alkiblar da kamfas ke bayarwa a zahiri, don haka ba ta da amfani wajen zirga-zirgar ruwa ko kewayawa.
Taswirorin da aka juya ko aka sauya matsayinsu

Asalin hoton, Universal Images Group via Getty Images Images
Kamar yadda ake nuna girman wani yanki na ƙasa a taswira kan iya tasiri a yadda ake kallon muhimmancinsa, haka ma matsayin da aka ba shi a taswirar kan iya yin tasiri ga yadda mutane ke ganinsa.
Wasu masana ilimin taswira sun yi ƙoƙarin tsara taswirori ta yadda kudancin duniya zai kasance a sama maimakon arewa, domin ƙalubalantar ra'ayin da ke sa wasu su ɗauki ƙasashen kudancin duniya a matsayin marasa muhimmanci saboda kasancewarsu a ƙasan taswira.
Haka kuma, nahiyar da ake sanyawa a tsakiyar taswira kan bambanta daga wani yanki na duniya zuwa wani.
Abin da ake nunawa a tsakiyar taswira a wata ƙasa na iya bambanta da yadda ake gabatar da ita a wata ƙasa.
Duk da cewa irin waɗannan taswirori na ba da wata sabuwar hanya ta kallon duniya fiye da wadda mutane suka saba gani, masana na cewa ba sa magance matsalar fifikon da ake ba wasu yankuna a taswira.
Maimakon haka, suna sauya wurin da aka karkata hankali ne daga wani yanki zuwa wani.
Taswirorin da aka tsara daga mahangar yankunan (Polar-oriented)

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
Wata hanya da masana ilimin taswira suka bi domin magance matsalar wace nahiya ce za ta kasance a tsakiyar taswira, kuma ta fi ɗaukar hankali, ita ce kada a sanya kowace nahiya a tsakiya kwata-kwata.
Hakan ne aka yi a taswirar da ke cikin tambarin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), inda aka tsara duniyar daga mahangar turken Arewa (North Pole), sannan nahiyoyin duniya suka bazu daga cikinta zuwa kowane gefe.
Ana kiran wannan tsari da "Azimuthal Equidistant Projection", wanda ke nuna yankuna daban-daban na duniya a cikin taswira mai siffar da'ira da aka gina a kan wani matsayi na tsakiya.
A irin wannan taswira, dukkan wurare suna kasancewa a madaidaiciyar alkibla ko shugabanci idan aka auna su daga cibiyar taswirar.
Sai dai domin a iya nuna gaba ɗaya doron duniya mai siffar ƙwallo a cikin da'ira mai shimfiɗa, siffar wurare kan fara karkacewa yayin da ake nisa daga cibiyar taswirar.
Misali, a taswirar Majalisar Ɗinkin Duniya, yankunan da ke kusa da turken Kudu (South Pole) kan bayyana kamar an matse su ko an miƙa su fiye da yadda suke a zahiri.
Hakan na faruwa ne saboda da'irar da ke kewaye da turken Kudu ta fi girma sosai idan aka kwatanta da irin wadda ke kewaye da turken Arewa.
Saboda haka, duk da cewa wannan nau'in taswira na rage yi wa wata nahiya fifiko, har yanzu yana fuskantar ƙalubalen karkatar da siffa da girman wasu yankuna na duniya.










