An naɗa Zidane a matsayin kocin Faransa

    • Marubuci, Charlotte Coates
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

An sanar da nadin tsohon mai horas da ƙungiyar Real Madrid Zinedine Zidane a matsayin sabon mai horas da tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa.

Didier Deschamps, kocin tawagar Faransa mafi daɗewa ya kammala aikin da ya kwashe shekara 14 yana yi a tawagar bayan cire Faransa da Spain ta yi a wasan kusa da ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Zidane wanda ya taɓa lashe kofin duniya a matsayin ɗan wasan tawagar Faransa a shekarar 1998, ya kasance ba ya wani aiki tun bayan barin Real Madrid a karo na biyu a matsayin koci a shekarar 2021.

Zidane mai shekara 54 wanda ake kallo a matsayin ɗanwasan Faransa mafi bajinta, zai sanya hannu kan kwantaragin da zai ba shi damar jan ragamar ƙasar a wasannin neman gurbin gasar kofin duniya ta 2030.

Lokacin da ya yi magana kan naɗa shi sabon aikin, Zidane ya ce "wannan babban abin alfahari ne" samun damar jagorantar babbar tawagar Faransa bayan ta kammala Gasar Kofin Duniya a matsayi na huɗu.

"Na sha faɗi cewa: babu abin da za a iya kwatantawa da tawagar ƙasar Faransa. Saboda haka abin murna ne, babban abin alfahari ne a ce mutum ya zama mai horas da tawagar ƙasar Faransa," in ji shi.

"Haka nan kuma babban nauyi ne. Ina so na gode wa shugaban [Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa] Philippe Diallo da tawagarsa, da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Faransa saboda yarda da suka nuna, haka nan ina jinjina wa Didier kan shekara 14 da ya kwashe yana aiki.

A tsawon shekara 14 da Deschamps ya jagoranci Faransa, ya taimaka mata wajen lashe Kofin Duniya karo na biyu a shekarar 2018.

Wasan farko da Zidane zai jagoranta a matsayin mai horas da tawagar Faransa shi ne wanda za a kara tsakanin Faransa da Turkiyya a gasar tawagar ƙasashe ta Nations League a ranar 25 ga watan Satumba.

Zidane mai tarin kofuna

Bayan yin ritaya daga ƙwallon ƙafa, bayan Gasar kofin duniya ta 2016, Zidane bai shiga aikin horaswa ba har sai shekara ta 2014, lokacin da ya karɓi aikin horas da ƙaramar ƙungiyar Real Madrid.

Ya samu ƙarin matsayi zuwa mai horas da babbar ƙungiyar Real Madrid a watan Janairun 2016, kuma ya zuwa ƙarshen kakar wasa ta farko ya jagoranci ƙungiyar zuwa lashe kofin zakarun nahiyar Turai, inda ta yi nasara kan Atletico Madrid a wasan ƙarshe ta hanayr bugun fenariti.

Wannan ne karo na farko a cikin nasarori uku da ƙungiyar ta samu a jere ta lashe kofin na zakarun Turai, inda ta zamo wata ƙungiya ta farko da ta lashe kofin sau uku a jere bayan Bayern Munich wadda ta yi irin haka a shekarar 1976.

Zidane ya kuma lashe kofin La Liga a kakar wasa ta 2016-17, amma sai ya bar ƙungiyar a kaka ta gaba, inda ya ce ana buƙatar sauyi a ƙungiyar.

Sai dai Zidane ya koma ƙungiyar ta Madrid a watan Maris na 2019 yayin da ƙungiyar ke cikin wani hali, inda ya samu nasarar lashe kofi a kakar 2019-20.

Ya jagoranci wani lokaci da Real Madrid ta narka kuɗi sosai wajen sayen ƴanwasa, inda aka sayi ƴanwasa irin su Eden Hazard da Rodrygo.

Amma Zidane ya bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa ta 2020-21 bayan Real ta kammala kakar ba tare da lashe komai ba, kuma tun daga lokacin bai sake karɓar wani aiki ba.

An daɗe ana alaƙanta Zidane da aikin horas da tawagar Faransa, amma karon farko da aka fara alaƙanta shi da aikin sosai shi ne bayan cire Faransa tun a matakin rukuni a gasar kofin duniya ta 2010.

Shekaru 16 bayan haka, yanzu Zidane ya karɓi ragamar ƙungiyar inda zai jagoranci Faransa zuwa gasar kofin nahiyar Turai ta 2028.

Rawar da Zidane ya taka a tarihin ƙwallon ƙafa

Zidane ya fara sana'ar ƙwallo ne a ƙungiyar Cannes ta Faransa a shekarar 1989, daga nan ya tafi Bordeaux, sannan ya koma Juventus a 1996.

Mai buga tsakiya, Zidane ya taimaka wa Juventus lashe kofunan gasar Serie A a jere da kuma kaiwa wasan ƙarshe na zakarun nahiyar Turai, kafin ya tafi Real Madrid a 2001.

Ya koma Madrid ne kan kuɗi fam miliyan 66, a matsayin mafi tsada a tarihi a wancan lokacin, sa'ilin da ƙungiyar ke kan ganiya, inda ya taka leda tare da mashahuran ƴanwasa irin su Ronaldo da Luis Figo da kuma David Beckham.

Ya fara fanshe kuɗin da aka saye shi ne a kakar 2002 sa'ilin da ya ci wata ƙwallo mai ƙayatarwa a wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai, inda Real Madrid ta yi nasara da ci 2-1 a kan Bayer Leverkusen.

A tawagar Faransa kuwa Zidane ya bayar da gudumawarsa sosai ne a gasar kofin duniya ta 1998, lokacin da ya zura ƙwallo biyu da kai a wasan da aka buga a birnin Paris.

Faransa ce ta doke Brazil 3-0 a wasan inda ta lashe kofin a karon farko, sannan kuma Zidane ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallo ta Ballon d'Or a shekarar.

Haka nan Zidane na cikin tawagar Faransa da ta lashe kofin Turai na 2000, amma ta kasa taɓuka abin a zo a gani a gasar kofin duniya ta 2002 da gasar kofin Turai a 2004.

Ya yi ritaya daga buga wa Faransa wasa ne a shekarar 2004, amma an shawo kansa ya buga wa ƙasar wasa sa'ilin wasannin neman gurbin kofin duniya na 2006.

Zidane ya taka rawa a gasar, inda Faransa ta kai matakin kifa ɗaya ƙwale har zuwa wasan ƙarshe da Italiya – wasa na ƙarshe a matsayinsa na ɗanwasan ƙwallon kafa – inda ya ci ƙwallo ta farko ta hanyar bugun fenariti, minti 7 bayan fara wasa.

Sai dai Italiya ta rama cin inda wasan ya kai ga ƙarin lokaci, kuma a lokacin ne aka samu saɓanin da ya kai ga Zidane ya kara wa Marco Materazzi kai, aka ba shi katin kora. Italiya ta yi nasara a wasan lokacin da aka kai matakin bugun fenariti.