Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka kashe kusan mata 600 cikin watanni uku a Afirka ta Kudu
- Marubuci, Khanyisile Ngcobo
- Aiko rahoto daga, Johannesburg
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Kusan mata 600 ne aka kashe a Afirka ta Kudu tsakanin watan Yuli zuwa Satumba na wannan shekarar, a cewar kididdigar laifukan da aka fitar a kasar.
Wannan adadi ya haɗa da mata 13 waɗanda aka gano gawarwakinsu tsirara da raunuka a wuraren jama'a a Johannesburg da kewaye.
Kisan gillar ya haifar da fushin jama'a, kuma 'yan sanda sun fuskanci matsin lamba don gano waɗanda suka aikata laifin, a cikin ƙasar da ke ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da cin zarafi da kisan kai a duniya.
A cikin sabon kisan gillar da aka yi, an harbe mata biyar da wani yaro karami a lardin Free State a farkon wannan makon.
Sabuwar kididdigar laifuka, da aka fitar a ranar Juma'a, ta nuna cewa an kashe mata 581 a kasar tsakanin watan Yuli zuwa Satumba, ciki har da 131 a lardin Gauteng wanda ya hada da Johannesburg.
Wannan kididdiga ta nuna raguwar adadin kisan kai kaɗan.
'Yan sanda sun bayar da rahoton kisan kai 5,590, kasa da 204 idan aka kwatanta da na wannan lokacin a bara. Wannan har yanzu yana zuwa matsakaicin kisa kusan 60 a rana.
Ba a san ko adadin matan da aka kashe karuwa ne ko raguwa ba saboda 'yan sanda sun daina bayar da waɗannan alkaluma kwanan nan saboda rashin daidaito a alƙaluman.
Mukaddashin Ministan 'Yan Sanda Firoz Cachalia ya ce akwai bukatar a yi "ƙarin ƙoƙari don hana cin zarafi" ga mata da yara.
A cewar 'yan sanda a lardin Free State, kudu da Johannesburg, wasu mutane uku da suka rufe fuska sun bude wuta kan wani iyali a garin Botshabelo a daren Laraba.
An yi zargin cewa mutanen uku suna neman mai gidan ne, kuma lokacin da suka fahimci ba ya nan, "sun shiga gidan da ƙarfi suka fara harbin mutanen da ke ciki," in ji 'yan sanda.
An harbi matar mai gidan a ciki kuma an kai ta asibiti. Ba a kama kowa ba.
A ranar Alhamis, shugaban 'yan sanda na lardin Gauteng ya ce an kama mutane takwas dangane da kisan gillar guda 13 wanda ya haifar da koke-koke a kasar a farkon wannan shekarar.
Janar Tommy Mthombeni ya ce uku daga cikin wadanda aka kama ana zarginsu da kisan Elizabeth Moselakgomo, wacce bacewarta ta haifar da nemanta a duk fadin kasar.
Matar mai shekaru 38 ta ɓace ne a lokacin da take motsa jikin da ta saba yi kullum a kusa da gidanta da ke Kempton Park.
An gano gawarta, dauke da rauni sosai a ranar 12 ga Satumba.
Shugaban 'yan sandan ya ce an kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da hannu a mutuwar Jabulile Ntimba mai shekara 33, wadda aka gano gawarta sanye da ƴar ƙaramar riga, aka kuma naɗe ta da mayafi a gefen hanya a Boksburg ranar 17 ga Satumba.
Gawar Ntimba ita ce ta tara cikin gawarwaki da aka gano a yankin Ekurhuleni.
Ya ce an kama wani mutum bisa zargin hannu a ɗaya daga cikin kisan da aka aikata a Kempton Park, yayin da aka kama wani da ake zargi da kisan Ntombifuthi Nxumalo a Tembisa, da ke arewa maso gabashin Johannesburg.
An gano gawar Nxumalo a wata makabarta ranar 26 ga Satumba. An same ta tsirara, tana da munanan raunuka a kai, sannan akwai duwatsu a kusa da gawarta.
A watan Yuli ma, an kama wani mutum dangane da mutuwar Busisiwe Mahlangu, wadda aka gano gawarta a Kempton Park ranar 15 ga Yuli. Ita ce ta farko cikin mutane 13 da aka gano gawawwakinsu a yankin.
A watan Satumba, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi alƙawarin cewa za a yi duk mai yiwuwa domin gano waɗanda ke da hannu a kisan.
A bara, ya ayyana cin zarafin mata a matsayin "bala'i na ƙasa".