Me ya sa mutane ke rububin taɓa dutsen Hajaral-Aswad?

...

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A duk lokacin aikin Hajji Musulmai ke ibadar ɗawafi a ɗakin Ka'aba, akan gan su suna ta turuwa a wuri guda a ƙoƙarin taɓa wani baƙin dutse da ke jikin ɗakin Ka'abar.

Dawafi na nufin zagaye Ka'aba har sau bakwai, kuma a wannan lokaci ne yawancin zuƙatan alhazai ke karkata zuwa kusurwar da ke ɗauke da baƙin dutsen na Hajar al-Aswad.

A nan ne ake ganin tururuwar mutane, wasu na ture wasu cikin turmutsisti duk a yunƙurin taɓa ko sumbatar dutsen, duk da cunkoson jama'a da ke kewaye da shi.

Wannan yanayi kan haifar da tambayoyi ga masu kallo da wasu Alhazai.

Shin wajibi ne musulmi ya taɓa wannan dutse a lkacin ibadar, ko kuwa akwai wata ma'ana ta daban da ke bayan wannan aiki?

Domin samun ƙarin haske kan wannan batu, BBC ta tuntuɓi wani malami a Abuja, Ustadh Aminu Zubairu, wanda ya bayyana cewa mutane suna rububin taɓa Hajar al-Aswad ne saboda matsayinsa a tarihin Musulunci da kuma abin da ake dangantawa da shi na falala da lada.

A cewar malamin ya zo a cikin hadisi, Annabi Muhammad (SAW) ya taɓa wannan dutse, kuma Musulmai suna bin wannan misali ne domin neman lada da ɗaukaka da falala da ake kyautata zaton yana da shi da kuma daga asalin inda ya Dusten ya taho

....

Asalin hoton, Getty Images

Shin wajibi ne sumbata ko taɓa dutsen?

Ustaz Aminu ya ce sumbatar Dutsen ba wajibi bane, abu ne dai da yake da muhimmanci saboda an ga Annabi (SAW) ya yi sanda yayi Umrah da lokacin da ya yi aikin Hajji kuma sahabai dukansu sun sumbaci Dutsen.

"Amma a daidai lokacin da mutum ba zai samu damar sumbatar Dutsen ba, an yi umarnin cewa zai iya yin ishara ko zai iya taɓawa da sanda sannan sai ya sumbata."

"Idan sandan ma ba zai yiwu ba, ya yi ishara kawai ta hanyar nuni daga hannun shi kamar ya taɓa sai ya sumbata, shikenan an wuce wannan matsalar."

Ustadh ɗin ya kuma kawo misalin inda ya ce an samu sayyidina Umar (RA) yana cewa "wannan Dutse ne kawai yanda kake bawan Allah, ba ka iya cutar da ni, ba ka iya amfanar da ni komai, da ba dan cewa naga Annabi Muhammad (SAW) ya sumbace ka ba, nima bazan sumbace ka ba"

"Kinga wannan bayani ne ƙarara na cewa wannan Dutsen, sunbatar shi ba wai wani abu ne na wajibi ba na dole dole sai anyi ba."

Ya ƙara da cewa "Tunda anga Annabi da Kanshi wani lokaci yana sumbatar Dutsen kuma wani lokacin da bai samu sumbatar shi ba saboda cunkoson jama'a, an ga ya yi ishara zuwa ga hannun shi, saboda haka, za a iya yin ishara kawai a wuce wurin."

Yaya matsayin ibadar mutumin da bai taɓa dutsen ba?

....

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ustadh Aminu ya ce idan ma mutum bai samu damar taɓa ko sumbatar Dutsen ba ko kuma yin ishara ga Dutsen ba gaba ɗaya, tunda ba rukuni bane, kuma ba wajibi bane, aikin Hajjin bawa ko Umrah bai ɓaci ba

"Abun da ya tabbata daga Annabi (SAW) shi ne Annabi ya sumbaci Dusten, shine kawai abun da aka sani, bayan ga wannan, idan da akwai wani falala da mutum zai samu ko girmamawa ko ɗaukaka shine na yayi aiki da aikin da Annabi (SAW) ya yi. to wannan falala ce wadda take da matsayi sosai a addinin Musulunci."

"Saboda haka, wannan na nuna cewa Sumbatar ko taɓa Dusten Hajarul Aswad ba wajibi bane, sunnah ce saboda an ga Annabi ya yi ne, shiyasa ake yin shi kuma sunnah ba ta ɓata ibadah, ba ta lalata duk wani ibadah da aka ce an cire sunnah face idan wata babbar sunnah ce wacce take mu'akkada."

Ustadh ɗin ya ƙara da cewa falala da ake ƙoƙarin samu daga wannan Dusten , falala ne na ayi aiki da umarnin Annabi Muhammad (SAW) ko kuma da aikin da Annabi ya yi.

"Amma cewa sai an taɓa shi ko sai an sumbace shi dan ana tunanin wasu har suna gogoriyar su shafa Dutsen sannan su goga a jikinsu ko a fuskarsu dan neman tabarruki, duk wannan ba abu bane da ya inganta.

"Saboda haka, ana fatan Insha Allahu aikin Hajjin wanda bai smau ya taɓa Baƙin Dutsen ba ko sumbace ba ya yi bi izzinin Allah. Allah ne masanin komai." Ustadh ɗin ya ƙara da cewa.

Asali da tarihin Hajar al-Aswad?

.....

Asalin hoton, Getty Images

Aminu ya ce asalin Baƙin Dutse (Al-Hajar al-Aswad) ya kasance daga cikin batutuwan da malamai suka yi bayani a kai bisa abin da ya zo a Hadisai.

"An ruwaito cewa akwai Hadisin da ya tabbata cewa Manzo Allah (SAW) ya ce asalin Dutsen ya zo ne daga Aljannah tun zamanin Sayyidina Ibrahim (AS) da Isma'il (AS) a lokacin da za su gina ɗakin Ka'aba."

Ustadh ɗin ya ƙara da cewa asalin shi, Dutse ne da yake fari ƙal wanda ya fi madara ƙyalli da haske.

"Amma kuma zunubin mutane da abubuwa dai da yake faruwa na ɗanadam shine har ya mayar da Dutsen baƙi, wannan shine asalin Dusten Hajarul Aswad." in ji sa.

Matsayin dutsen a wajen ɗawafi

Ustadh Aminu ya ƙara da cewa matsayin Baƙin Dutse (Al-Hajar al-Aswad) a cikin Hajji da Umrah yana da girma sosai a Musulunci.

"Matsayin wannan Dutse a addinin Musulunci da kuma ibadar Hajji ko Umrah, matsayi ne mai daraja sosai, domin Hadisi ya nuna cewa Annabi (SAW) ya kasance yana sumbatarsa." in ji malamin.