'In ka gudu su harbe ka, in ka tsaya su sace ka': Munin garkuwa da mutane a Najeriya

    • Marubuci, Yemisi Adegoke
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Africa
    • Aiko rahoto daga, Zamfara and Oyo states
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

"Idan ka gudu ka shiga ɗaki, sai su banka wa ɗakin wuta, idan kuma ka fito kana gudu, sai su harbe ka" in ji Fatima yayin da take ba da labarin wani hari da aka kai ƙauyensu a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Ta ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe biyu na dare, inda suka kasu zuwa gida uku domin kewaye ƙauyen: daba ta farko a bakin ƙauyen, wata ta shiga cikin ƙauyen, sannan wata dabar ta koma bayan ƙauyen don tare masu tserewa.

"Sun dinga harbe-harbe ba tare da nuna tausayi ba, suna harbin mutane kan uwa da wabi," in ji matar mai shekara 55 a tattaunawarta da BBC.

Wannan na ɗaya daga cikin hare-hare da dama da suka addabi al'ummar yankin, galibinsu Musulmi, inda mutane ke rayuwa cikin fargabar a yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.

Fatima ta bayyana yadda irin waɗannan hare-hare ke gudana, tana cewa: "Za ka iya ganin babura 100, kuma kowanne na ɗauke da mutum uku."

A cewarta, kimanin mutum 70, ciki har da yara, aka kashe a ƙauyen Bia Buki a watan Yuni.

Ta ce maharan sun kuma riƙa kai farmaki ga mutanen da ke ƙoƙarin tserewa, yayin da wasu yara suka jikkata bayan sun faɗa cikin ramuka.

Daga cikin waɗanda harin ya kashe har da mijinta da kuma shida daga cikin 'yan'uwansa bakwai.

Fatima na ɗaya daga cikin kimanin mutum 800,000 da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rikicin ya raba da muhallansu a arewa maso yammacin Najeriya.

Ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa mutane suka bar gidajensu shi ne tashe-tashen hankula.

Wasu daga cikin hare-haren mayaƙan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ne ke kai su, amma mafi yawansu a wannan yanki ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane ne da ake kira 'bandit', waɗanda galibi ke amfani da babura wajen kai hare-hare cikin gaggawa sannan su tsere kafin jami'an tsaro su iso.

Dubban mutane sun shiga ƙungiyoyin sa-kai da gwamnati ke mara wa baya domin yaƙi da 'yan bindiga.

BBC ta tattauna da ɗaya daga cikinsu, wanda ya ce ƙungiyarsa mai ɗauke da makamai ta kashe ƴan bindiga da dama.

Sai dai duk da haka, ƙungiyoyin na ci gaba da kai hare-hare.

Alamun da ake gani sun nuna cewa tashe-tashen hankula da sace mutane suna ƙara ta'azzara tare da yaɗuwa zuwa wasu yankunan kudancin ƙasar.

Fatima ta ce lokacin da ƴanbindigar suka kai hari gidanta, ta gudu tare da wasu mazauna ƙauyen zuwa dajin da ke kusa domin ɓuya.

"Dajin ne ya zama mafakarmu. Mun gudu tare da yaranmu, idan ba ka ga ɗanka ba, sai ka ɗauki ɗan maƙwabcinka," in ji ta.

Ta ce mutane sun kwana a cikin dajin kafin daga bisani su nufi babban birnin jihar, Gusau, "inda muka samu ɗan natsuwa."

A yanzu Fatima na zaune a wani sansanin ƴan gudun hijira na wucin gadi da ke Gusau tare da ƴaƴanta bakwai masu shekaru tsakanin tara zuwa talatin.

A cikin harabar sansanin, ana ganin mata da dama zaune rukuni-rukuni cikin ƙura, da yawa daga cikinsu sanye da hijabai masu launuka iri-iri.

Fatima na ganin fiye da mutum dubu ɗaya ne ke zaune a sansanin.

Ta ce rayuwa a sansanin tana da matuƙar wahala, domin "babu ma wurin da ya dace da za ka kwanta." Abinci ma ba ya wadatuwa, kuma taimako yana zuwa ne lokaci-lokaci.

Fatima ta ba da labarin sau biyu da wasu "masu taimako" suka kawo musu shinkafa ko dankali.

Ta ce ana tura yara zuwa neman itacen girki domin su sayar, su samu kuɗin sayen abinci, amma ƴanbindiga sun yi garkuwa da yara 22 daga cikinsu.

Yayin da take nuna wani gini da ke kusa, Fatima ta ce: "A can za ka samu mata ɗari ko fiye... wataƙila biyu ko uku ne kawai suka ci karin kumallo."

"Lokacin da muke cikin zaman lafiya muna da arzikinmu, amma yanzu al'amura sun sauya kuma mun zama mabarata."

Idanunta suka cika da hawaye, sannan ta yi kuka na wasu mintuna tana share fuskarta da hannayenta.

Duk da cewa tana da nisan kusan kilomita 25 daga ƙauyenta, barazanar da ta gudu daga gare ta ba ta gushe ba.

Ta ce lokacin da ta fara isa sansanin, sautin harbe-harbe kan hana ta barci da dare.

Yanzu abubuwa sun ɗan lafa, a cewarta, sakamakon sintirin da sojoji da ƙungiyoyin sa-kai masu goyon bayan gwamnati ke yi, amma har yanzu akwai fargaba a yankin.

Galibin ƴanbindigar daga ƙabilar Fulani suke, waɗanda a al'adance sana'arsu ita ce kiwon dabbobi.

Sai dai wasu daga cikinsu sun daina kiwon shanu, sun kuma karkata garkuwa da mutane da kuma karɓar kuɗin fansa, domin suna kallon hakan a matsayin hanya mafi sauri da sauƙin samun kuɗi.

Suna kai hare-hare kan garuruwa da ƙauyuka ko kuma su yi kwanton ɓauna ga matafiya, suna yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, suna kwashe duk abin da suka ga dama, kuma wani lokaci suna kashe waɗanda suka yi ƙoƙarin nuna turjiya.

Haka kuma suna tilasta wa al'ummomi biyan haraji, inda suke barin manoma su shiga gonakinsu ne kawai idan sun biya makudan kuɗaɗe.

A yanzu hare-haren sun fi yawa fiye da kowane lokaci.

A yankunan arewa maso yammacin Najeriya da suka zama maɓoyar 'yan bindiga, adadin hare-haren da ƙungiyar sa ido kan rikice-rikice ta duniya, ACLED, ta rubuta ya ƙaru da kashi 78 cikin 100 a rabin farkon wannan shekara idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Wata cibiyar ba da shawara kan harkokin tsaro ta ƙiyasta cewa masu garkuwa da mutane a Najeriya sun karɓi kimanin naira biliyan 7.8 na kuɗin fansa a cikin shekara guda da ta gabata, yayin da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ya ƙaru sosai.

Cibiyar SBM Intelligence ta ƙiyasta cewa an yi garkuwa da mutum 7,825 tsakanin watan Yulin 2025 zuwa Yunin 2026, wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 66 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Ana ganin ƙaruwa a ayyukan ƴan bindiga na daga cikin manyan abubuwan da suka haddasa wannan yanayi.

Malik Samuel na ƙungiyar Good Governance Africa, wata ƙungiya mai zaman kanta da ke bincike da fafutukar inganta shugabanci, ya ce "A halin yanzu babu wani yanki a arewacin Najeriya da ba ya fuskantar wani nau'i na garkuwa da mutane masu yawa."

Yaƙin da Najeriya ke yi da ƴanbindiga wani ɓangare ne kawai na matsalolin tsaro masu sarkakiya da ƙasar ke fuskanta.

Baya ga ƙungiyoyin ƴanbindiga da ke arewa maso yamma, akwai tayar da ƙayar baya ta masu iƙirarin jihadi a arewa maso gabas da rikice-rikicen masu neman ɓallewa a kudu maso gabas, da kuma rikice-rikice a yankunan tsakiyar ƙasar.

A yankunan tsakiyar ƙasar, manyan ƙorafe-ƙorafen sun shafi samun damar amfani da ƙasa da ruwa don kiwo da noma, yayin da bambance-bambancen ƙabilanci da na addini ma suka ƙara ruruta wasu daga cikin rikice-rikicen.

Yawancin masana sun yarda cewa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun kai hare-haren tashin hankali da suka shafi al'ummomi daban-daban ba tare da la'akari da ƙabila ko addinin mutanen da abin ya shafa ba.

Makarantu na daga cikin wuraren da masu garkuwa da mutane suka fi kai wa hari.

A shekarar 2014 ne aka fara kai munanan hare-hare kan makarantu, inda ƙungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da sama da 'yan makaranta mata 200 daga garin Chibok da ke jihar Borno.

Daga nan kuma ƴanbindiga suka riƙa kai hare-hare kan makarantu, ciki har da makatarntar Furamaren Oyo tare da garkuwa da ɗalibai da malamansu 44 waɗanda suka kwashe fiye da kwana 50 a hannun masu garkuwa kafin kuɓuyar da su.

A halin da ake ciki yanzu, al'ummomi na ci gaba da fama da matsalolin tsaro, kuma a jihar Zamfara dubban mazauna yankuna sun shiga ƙungiyoyin sa-kai masu samun goyon bayan gwamnati domin cike gurbin tsaron da ake ganin babu shi yadda ya kamata.

Sai dai akwai damuwa game da rawar da waɗannan ƙungiyoyi ke takawa.

A shekarar 2020, gwamnatin Zamfara ta haramta wata babbar ƙungiyar sa-kai saboda fargabar cewa kashe-kashen da ake yi ba tare da bin doka ba na ƙara rura wutar tashin hankali, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Mahukunta na cewa sabbin ƙungiyoyin sa-kai sun samu horo mafi inganci, amma Samuel na ƙungiyar Good Governance Africa ya bayyana su a matsayin "bam ɗin da ke jiran lokacin fashewa."

"Idan jama'a suka ɗauki makamai, ta yaya za a iya sarrafa su bayan rikicin ya ƙare? Ta yaya kuma za a iya kwace makaman daga hannunsu?"

Wani daga cikin mambobin ƙungiyar sa-kai ya same mu a wajen hedikwatarsu, wani gini mai bene ɗaya da aka yi da siminti, kuma ya amince ya yi magana da mu bisa sharadin a ɓoye sunansa yayin ziyararmu a watan Yuli.

Yana zaune kan babur ɗinsa, bindigar AK-47 rataye a kafaɗarsa, yayin da ya rufe fuskarsa da shirami.

Ya ce "Muna daga cikin mutanen da gwamna ya ɗauka aiki domin kare al'umma."

Ya bayyana cewa a wasu lokutan suna samun bayanan inda 'yan bindiga suke, kuma:

"Da taimakon Allah muna yaƙar su kuma muna cin galaba a kansu."

Ya ƙara da cewa "Ya kamata 'yan bindiga su fahimci cewa idan suka kai hari wani wuri suka kashe mutane, su ma ana iya kashe su."

Ya kiyasta cewa ya yi artabu da ƴan bindiga aƙalla sau 20, sannan ya ce ana ci gaba da samun kiraye-kiraye daga al'ummomi suna neman taimakon ƙungiyarsu.

Fatima ta yi kiran ƙara ɗaukar matakai, "Waɗannan masu garkuwa da mutane suna ko'ina da ko'ina'', in ji ta.

''Ba ina cewa gwamnati ta gaza ba, amma ko da tana ƙoƙari, tana buƙatar ta ƙara ƙaimi. Matsaloli suna nan, kuma muna ganin idan aka ƙara ƙoƙari tare da ƙarin jami'an tsaro, ƙauyuka za su samu zaman lafiya," a cewarta.

Ta ce tana son komawa gida, amma ba ta da tabbacin hakan zai yiwu, domin ta ji labarin cewa yanzu ƴanbindiga sun ƙauyensu sansani.

A cewarta, shugaban ƴan bindigar yankin ya zama tamkar mai iko a zahiri, har iyalai ke komawa gare shi domin sasanta rikice-rikicen cikin gida.

Fatima ta ce wani ƙauye da ke kusa da nasu "ya zama kufai gaba ɗaya, ko kaza babu a ƙauyen... irin waɗannan ƙauyukan da suka zama kufai ba sa ƙirguwa."

"Ko da ka koma, wahala kaɗai za ka tarar. Babu komai a can, babu abinci. Kana noma, amma idan lokacin girbi ya yi, sai su hana ka girbi ko kuma su yi garkuwa da kai."