Ƴan wasa 10 da za su haska a zagayen kusa da ƙarshe na Gasar Zakarun Turai

- Marubuci, Alex Bysouth
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Senior Journalist
- Lokacin karatu: Minti 4
Yau ne za a shiga zagayen wasan kusa da ƙarshe a Gasar Zakarun Turai, inda daga nan ne ake samun zaƙaƙuran da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or.
A wannan mako PSG za ta fuskanci Bayern yayin da Atletico za ta karɓi baƙuncin Arsenal.
Duka dai ƙungiyoyin huɗu na ƙunshe da zaƙa-ƙuran ƴan wasan da ke haskawa a wannan gasa ta bana.
A wannan muƙala mun zaƙulo wasu ƴan wasa da muka ba su matsayi daga na 1 zuwa na 10, dangane da ƙoƙarinsu a wannan kaka ta bana.
Mun kuma fara ne daga na 10 zuwa, wanda muke ganin ya fi kowa ƙoƙari a cikinsu a bana.
10. Matteo Ruggeri (Atletico Madrid)
Atletico Madrid ta fara wasa 11 cikin 14 da ta buga a gasar bana da Matteo Ruggeri.
Ƙungiyar, wadda Diego Simeone ke jagorantan, na shirin karɓar baƙuncin Arsenal, wadda ta ci su 4-0 a farkon gasar.
Dan wasan Italiyan mai shekara 24 na matuƙar yin ƙoƙari ga ƙungiyarsa a bana.
9. Bukayo Saka (Arsenal)
Ruggeri ya yi matuƙar ƙoƙari wajen hana Lamine Yamal sakat a zagayen kwata fayinal na gasar, don haka yanzu aikin da ke gabansa shi ne tare Bukayo Saka.
Ɗan wasan gefen na Arsenal ya shafe fiye da wata guda yana jinya, lamarin da ya bai buga zagayen kwata fayinal da Sporting ba.
Don haka ake ganin dawowarsa a yanzu za ta zame wa Atletico babbar barazana, musammam ga masu tsaron bayan ƙungiyar.
8. Achraf Hakimi (Paris St-Germain)
A baya-bayan nan tsohon fitaccen ɗan wasan bayan Brazil, Cafu ya bayyana Achraf Hakimi a matsayin wanda a yanzu babu kamar a lamba biyu a duniya.
Kuma kowa zai iya yarda da hakan ganin irin gudunmowar da yake bai wa PSG a yanzu.
Ɗan wasan Bayer Leverkusen, Alejandro Grimaldo ne kawai ɗan wasan baya da ya fi Hakimi taimaka wa a ci ƙwallo a wannan kaka.

7. Joshua Kimmich (Bayern Munich)
Joshua Kimmich na daga cikin ƴan wasan Bayern Munich da suka fi ƙwazo a kakar bana.
Ɗan wasan tsakiyar mai shekara 31 ya kasance ɗaya daga cikin ƴan wasan gaban ƙungiyar da suke yi tsaron bayan ƙungiyoyi barazana.
6. Khvicha Kvaratskhelia (Paris St-Germain)
Ousmane Dembele ya ci ƙwallo takwas tare da taimakawa a ci shida a gasar Turai ta bara lokacin da ya lashe kyautar Ballon d'Or.
Sai dai yayin da za a fara zagayen kusa da ƙarshe, ƙwallo ɗaya ko taimako ɗaya ne kawai ya hana Khvicha Kvaratskhelia cimma wannan nasara, inda tuni ya zura ƙwallo takwas da bayar da taimakawa a ci biyar.

Asalin hoton, Getty Images
5. Michael Olise (Bayern Munich)
Wani ƙarin ɗan wasan gefen da ake tunanin zai haska shi ne Michael Olise, wanda a wasa ƙalilan ne ba ya cin ƙwallo.
Luis Diaz da Serge Gnabry da Lennart Karl duka sun bayar da gudunmowarsu bayan ta Harry Kane.
Amma abu muhimmi shi ne Olise ya zuwa ƙwallo 20 ya taimaka aka ci 29 a duka gasannin da ya buga a bana.
4. David Raya (Arsenal)
David Raya ya wakilci tawagar masu tsaron bayan Arsenal a wanann lissafi, da suka ƙunshi William Saliba da kuma Gabriel Magalhaes.
A wasannin Zakarun Turai 22, ƙungiyar ta fara da duka ƴanwansan uku, kuma a wasa 13 daga cikinsu an gaza zura wa ƙungiyar ƙwallo, yayin da aka zura wa ƙungiyar ƙwallo 11 a ragowar wasannin tara.
Ɗan Sifaniyar mai shekara 30 ya tare kashi 90 cikin 100 na ƙwallayen ƙungiyoyin da ya fuskanta.

Asalin hoton, Getty Images
3. Julian Alvarez (Atletico Madrid)
An jima ba a buga wasa tsakanin Atletico Madrid da Arsenal ba sai a wannan kaka da suka fara haɗuwa a matakin farko na gasar.
Ɗan wasan Argentinan ya zura ƙwallo tara a gasar zuwa yanzu, fiye da kowane ɗan wasan ƙungiyar a kakar bana.
2. Vitinha (Paris St-Germain)
An jima ana ambata sunan Vitinha a wanann muƙala saboda kasancewarsa ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan tsakiyar duniya a yanzu.
Ɗan wasan na Portugal ya taimaka wa Luis Enrique lashe kofin a bara.
Ƙoƙarin da yake a wannan kaka ya sa ake kwatanta shi da tsohon ɗan wasan tsakiyar Barcelona da Sifaniya, Xavi.

Asalin hoton, Opta
1. Harry Kane (Bayern Munich)
Mutum na farko a wannan jeri shi ne Harry Kane. Ruwan ƙwallaye da ɗan wasan ke yi a wannan kaka ya sa ake alaƙanta shi da kyautar Ballon d'Or ta bana.
Zuwa yanzu ɗan wasan Ingilan ya zura ƙwallo 53 cikin wasa 45 da ya buga a duka gasanni a ƙungiyarsa ta Bayern a wannan kaka.
Ɗan wasan da ake yi wa laƙabi da dodon raga a yanzu ya zura ƙwallo a wasanni huɗu a jere a Gasar Zakarun Turai.
Zuwa yanzu ya zura ƙwallo 12 a gasar ta bana, adadi mafi yawa da wani ɗan wasan Ingila ya ci a gasar a kaka ɗaya.

Asalin hoton, Getty Images











