Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko waɗanne dalilai ne suka haddasa rikici a PRP?
A Najeriya yayin da ake ci gaba tsokaci dangane da wata sabuwar ɓaraka da ta kunno kai a jam'iyyar PRP, shugabanin jam'iyyar sun yi watsi da duk wani ikirari da ke nuna hakan ko rarrabuwar kai ko rikicin cikin gida a cikin jam'iyyar.
Jam'iyyar ta yi gargaɗi game da take-taken wasu waɗanda ta bayyana a matsayin bara gurbi da ke neman yi wa jam'iyyar kutse da rikita mata lissafi.
Shugaban jam'iyyar PRP Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya shida wa BBC cewar babu wata ɓaraka da suke fama da ita, sai dai: ''ɓaraka a siyasa shi ne a sami ɓangarori biyu ko uku da ke ikirarin shugabanci, ko wani ya ce ba a yi masa adalci ba, ko kuma kotu ta ce ba ta yarda da wani shugabanci ba, to mu ba mu fuskanci ko ɗaya daga ciki ba,'' in ji shi.
Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya kuma ce a iya saninsa bayan jam'iyyar ta su ta PRP ta gudanar da babban taronta inda aka zaɓe su suka zama shugabanni, babu wata hatsaniya ko mastaala da suke fuskanta.
''Mun gama babban taronmu lafiya, kuma waɗanda suka yi kuka a lokacin, Allah Ya taimake mu, tsarin jam'iyya ya ce dukkan wanda yake ganin ba a yi masa adalci ba, to yana iya kai ƙara.
''Sun kuma kai ƙarar an kuma sanar da su cewar nan an yi gaskiya nan kuma ba a yi ba, kowa kuma ya dawo aka ci gaba da tafiya. To ka ga ba mu da wata matsala a jam'iyyarmu a iya saninmu,'' in ji Haleem Baba-Ahmed.
Ya ƙara da cewa: ''Wannan yunƙuri ne kawai na haifar da tashin-tashina, ganin yadda tagomashin jam'iyyar ta PRP ke karuwa, kuma take ƙamshin turare Ɗan-goma a wajen masu neman sauyin sheka daga wasu jam'iyyu, saboda irin cuku murɗar da suke fuskanta.''
Har ila yau, shugaban PRP din a Najeriya, ya kuma yi zargin cewar ƙungiyar da ta kunno kai a jam'iyyar tasu, sun san daga inda ta futo, amma ba zai sanar da inda ta futo ba sai nan gaba.
Sai dai ya ce duk lokacin da aka ce zaɓe ya ƙarato, suna samun irin haka, don haka sun saba fuskantar hakan.
"Munsan daga inda ta futo, sai dai mun yi maganinta. Tun sanda suka kunno kai, mun faɗa musu cewar idan a baya sun saba yin irin wannan barazana a ba su kuɗi, to ba mu da shi.
Mun kuma tambaye su ko sun shiga zaɓe ne ba a yi musu adalci ba? Suka ce ba su shi ga ba. Ina katinku na jam'iyya? Suka ce babu, illa kawai ba sa jin daɗin yadda jam'iyyar ke tafiya, daga nan suka tafi" in ji shugaban PRP ɗin.
Sai dai wasu kuma na ganin ɓullar wannan matsala dai, tamkar somi-somin afkawa jam'iyyar ne cikin wani sabon rikicin da ka iya shafar tsarin PRP a zaɓen 2027 da ke ƙaratowa.
To amma Hakeem Baba Ahmed ya yi martanin cewar suna tsaye a kan gaskiya kuma ba su karay dokar zaɓe, ko ta hukumar zaɓe ko ta gwamanti, ko kundin jam'iyyar PRP kuma ba su take wa kowa haƙƙi ba.
"Ina ganin cewar ko don an ga cewar wasu daga cikin ƴan Najeriya da yan jam'iyyar da aka ƙona gidansu na shiga jam'iyyar ita tasa suke zargin ya sa ake musu irin haka ganin cewar suna samun karɓuwa wanda shi ya sa wasu ke musu irin wannan kutse".
Ya ce idonsu a bude yake ba za su amince wasu su shigo su ɓata musu jam'iyya ba, inda ya jaddada kira ga yan jam'iyyar tasu da su sa ido da kyau wajen ganin cewar dukkan wani baragurbi da ya shigo don tayar da zaune tsaye ko raba kawunan jam'iyya don kar ta yi nasara ko tasiri a zaɓen da za a yi na 2027 ba, su yi gaggawar sanarwa da shugabancin jam'iyya don ɗaukar matakan da suka kamata.