Abin da hukuncin kotun ƙoli ke nufi ga David Mark da Kabiru Turaki

Lokacin karatu: Minti 3

Kotun ƙoli ta yanke hukunce-hukunce guda uku dangane da shari'o'in da ɓangarorin jam'iyyun hamayya na PDP da ADC suka shigar.

Ɓangaren Tanimu Turaki na jam'iyyar PDP ya shigar ƙarar ne a kotun inda yake neman kotun ta fayyace dangane da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke wanda ya ruguza babban taron da ɓangaren ya yi a birnin Ibadan na jihar Oyo a watan Nuwamban 2025.

Shi ma ɓangaren Abdulrahman Mohammed na PDP ɗin ya shigar da ƙara na a a amince da shugabancinsa da Samuel Anyanwu da Nyesom Wike ke goyon bayansu.

Haka zalika, ɓangaren sanata David Mark na jam'iyyar ADC ya shigar da ƙara ne dangane da cire sunansa daga na'urar hukumar zaɓen Najeriya da Inec ɗin ta yi a watan Maris.

Jam'iyyar hamayyar ta ADC ta fara neman a gaggauta yanke hukunci kan saɓanin da take ciki kan sahihancin shugabancinta, domin fayyace makomar jam'iyyar musamman hamayyar shugabanci tsakanin bangaren Sanata David Mark da kuma bangaren Nafiu Bala Gombe.

Hukunci kan David Mark da ADC

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.

A hukuncin da kotun ta yanke ƙarƙashin mai shari'a Mohammed Lawal Garba, ta ce masu ƙarar su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da ake yi.

Alƙalan sun kuma yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na cewa a tsaya inda ake da cire sunan shugabancin ADC ɓangaren David Mark daga shafin INEC.

Me hukuncin ADC ke nufi?

Yanzu haka dai kotun ƙolin ta ce a koma babbar kotun tarayya domin sauraron ƙarar farko sannan kuma ta yi watsi da hukuncin kotun ƙoli da ta ce a tsaya a inda ake wanda hakan zai ɗage hukuncin da hukumar zaɓe ta Najeriya ta ɗauka na daina kallon David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC.

Tun da farko dai tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa mai kula da yankin arewacin ƙasar, Nafi'u Bala Gombe ne ya shigar da tsagin David Mark ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana zargin su da ƙwace shugabancin jam'iyyar.

Lamarin da ya sa tsagin na David Mark - ya garzaya gaban kotun ɗaukaka ƙara, inda ya buƙaci kotun ta hana babbar kotun tarayya sauraron batun rikicin shugabancin nata.

Ɓangaren na David Mark ya ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi rikicin shugabancin jam'iyya.

Yanzu hakan na nufin cewa komawa ga kotun farko na nufin fara shari'ar tunda fari, kuma abin da hakan ke nufi shi ne turka-turkar shugabancin ADC za ta fara ne daga babbar kotun.

Kotu ta kori ƙarar PDP ɓangaren Tanimu Turaki

Kotun ƙolin ta yanke hukunci dangane da shari'ar jam'iyyar PDP inda kuma ta kori ƙarar da shugabancin PDP tsagin Tanimu Turaki ya shigar.

Kabiru Turaki dai ya shigar da ƙarar ne yana ƙalubalantar matakin rushe taron zaɓen shugabanninsu da aka yi a Ibadan da kotun ƙolin ƙasar ta yi a baya.

Yayin da yake sanar da matsayar alƙalan, mai shari'a Stepehen Adah ya bayyana cewa taron da suka gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025 a Ibadan rashin ɗa'a ne ga hukuncin babbar kotun tarayya da mai shari'a James Omotosho ya yanke inda ya dakatar da su daga gudanar da babban taron jam'iyyar.

Kotun ƙolin ta kuma soki ɓangaren Turaki game da zuwa kotun da ba ta da hurumi, a madadin zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Saboda haka, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar da ta yanke na haramta taron PDPn a jihar Oyo.

Uku daga cikin alƙalai biyar ɗin sun amince da wannan hukuncin, yayin da biyu daga cikinsu suka ce kotun ɗaukaka ƙarar tana da hurumi.

Hukuncin kotu kan PDP ɓangaren Wike

Bugu da ƙari, kotun ƙolin ta kuma yi watsi da buƙatar da shugabancin jam'iyyar PDP ɓangaren Nyesom WIke ya shigar na neman a tabbatar da shugabancin nasu bayan rushe ɓangaren Turaki.

An dai zaɓi Abdulrahman Mohammed da Samuel Anyanwu a matsayin shugaban jam'iyyar PDP da sakatare a watan Maris 2026.

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike shi ne ke goyon bayan shugabancin na Abdulrahman Mohammed.

A watan na Maris ne dai wakilai daga faɗin Najeriya fiye da 2,000 suka zaɓi Abdulrahman da Anyanwu da ƙarin wasu mambobi 19.

To sai dai ƙin amincewar da kotun ƙolin ta yi da buƙatar da ɓangaren ya shigar hakan na nufin a yanzu babu wani tsayayyen shugabanci a jam'iyyar PDP.