'Burinmu ƴaƴa mata su yi karatu su zama likitoci da ma'aikatan asibiti'

Yan makaranta
Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da Najeriya ke fama da ƙarin tabarbarewar tsaro da ta zama tarnaƙi ga ilimin ƴaƴa mata, masu ruwa da tsaki na kiran a ƙara himma wajen ganin miliyoyin ƴanmata a Arewacin ƙasar sun kammala aƙalla sakandare.

Da yawan ƴanmata ne ba su iya kammala karatunsu na firamare da sakandare. Baya ga ɗimbin waɗanda ba sa zuwa makarantar ma baki-ɗaya saboda dalilan talauci da al'ada da sauransu.

To sai dai, wata gidauniya bunƙasa ilimin ƴaƴa mata a garin Zaria mai suna Center for Girls' Child Education ta ce ta tashi tsaye wajen taimaka wa mata wajen kawar da ƙalubalen da ke hana su samun ilimin.

Ɗaya daga cikin waɗanda suke cin moriyar wannan shirin, Khadija Sa'id Ismail ta ce burinta shi ne ta ga tana aikin asibiti.

"Na samu kaina ne a wannan karatu na musamman daga lokacin da muka shiga aji biyu na sakandare. Suka zo suka ce za su taimaka mana da horo na musamman saboda mu cika abin da muke buri a rayuwa saboda yawancinmu ba za mu iya ba," in ji ta.

Wannan wata ɗalibar sakandare ce a garin Zaria da ke da dogon buri rayuwarta na ganin ta je jami'a, inda take son karanta fannin gano cututtuka ta hanyar ɗaukar hoto, wato radiogaohy.

Ta ce ilimin ƴaƴa na da muhimmanci, "Ko ba ta taimaka ma wasu ba, za ta taimaka wa ƴaƴanta da waɗanda suke kusa da ita, musamman danginta," in ji Khadija.

Ilimin ƴaƴa mata a Najeriya

Dalubai
Bayanan hoto, "Burinmu ilimin ƴaƴa mata ya zama kyauta kuma ingantacce na shekara 12"

Khadijah Sa'id Ismail, ɗaliba ce da ta fito daga gidan masu ƙaramin ƙarfi a yankin karkara. A arewacin Najeriya, dubban ɗaruruwan ƴaƴa mata ne har yanzu ba sa zuwa makaranta ko kuma ba sa iya kammala karatu duk da ana ta daɗa kwarzanta batun cewa ilimi ne ginshikin rayuwa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai Khadijah Sa'id Ismail ta yi gam-da-ƙatar: "wata gidauniya yanzu ta ɗauki nauyinta, inda ta sanya ta a cikin ɗaliban da take bai wa horo na musamman domin su cika burinsu na rayuwa.

"Sun taimaka wa rayuwarmu, sun ba mu abin da ba kowa ba ne zai iya ba mu shi. Kirana ga gwamnati shi ne ta taimaka ta buɗe irin kalan horon na musamman ga ɗalibai wanda iyayensu ba su da ƙarfin da za su iya kai su ga cika burinsu.

Kamar Khadijah, wata matashiya mai suna Amina Yusuf, ƴar asalin garin na Zaria, ta ce ba ta taɓa tsammanin za ta iya kammala karatun firamare ba, inda ta ce har karkararsu aka je aka fara koya musu karatu a ƙofar fadar mai unguwa.

Amina Yusuf ta ce ta dalilin wannan cibiya, ta Centre for Girls' Education ''da ta zo karkararmu ta ce tana so ta biya mana kuɗin makaranta da littafan karatu da na rubutu sannan za ta riƙa ba mu horo na musamman da ilimin zamantakewa da ake kira Safe Space a cikin karkararmu. Duk lokacin da muka taso daga makaranta bayan mun koma gida mun ci abinci, sai mu zo kofar gidan mai unguwa."

Ta ce, "Na koma na yi NCE na karanci Biology/Chemistry. Bayan na gama na koma na karanci biology education. Alhamdulillahi duka ta dalilin wannan kungiyar ne, yanzu ni graduate ce.

Wani ƙarin arashin shi ne Amina, wadda ta fito daga karkara, ta samu damar zuwa ƙasashe da dama na duniya.

"A lokacin da Malala ta zo Najeriya ina ɗaya daga cikin waɗanda suka tarbe ta. Akwai wani taro da muka je na Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka. Na je Rwanda. Na je Zambia duka a kan a kan harkar da ya shafi ilimin ƴaƴa mata," in ji ta.

Ita ma ɗaliba Sakina Abdulkadir ta bayyana irin gwargwamayar da ta sha domin cika burinta na zuwa makaranta.

"An haife ni a garin Tsibiri da ke ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna. A gidanmu tun muna firamare ake mana aure, amma da taimakon wannan cibiyar, na samu damar ci gaba da karatu, har na kai matakin NCE, kuma zan ɗaura har zuwa digiri."

"An koya mana rubutu da karatu da na ilimin rayuwa wato yadda za mu zauna da ƴan'uwanmu da na gaba da mu da yadda za mu yi magana da yadda za mu yi zamantakewa. Kai, har yanda za mu kula da lafiyarmu. Sannan ana koya mana sana'o'in yadda za mu riƙe kanmu har mu taimaka ma na kusa da damu."

'Abin da ya sa nake taimakon ƴaƴa mata'

Da ɗalibai 64 aka fara assasa Cibiyar Center for Girl's Education
Bayanan hoto, "Da ɗalibai 64 aka fara assasa Cibiyar Center for Girl's Education"

Akwai dai ƙungiyoyi da daidai kun mutane da yawa da suka dukufa kan kokarin rage illolin matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma wanda ba sa iya kammala makaranta a yankin.

Cibiyar tallafa wa karatun ƴaƴa mata ta Centre for Girls' Education na cikin irin waɗannan ƙungiyoyi masu ƙokari.

Habiba Mohammad, ita ce shugabar gidauniyar, ta ce burinsu shi ne su tallafa wa ƴaƴa mata su samu ilimi, su koyi sana'a kuma su zama mutane nagari, inda ta ce a shekarar 2007 ta assasa cibiyar da ɗalibai 64.

"A yanzu muna da tallafi da muke yi wa yara ko shirye-shirye kusan 8. Abin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa yara sun je makaranta, sannan suna ƙoƙarin gama karatun nan kuma su shiga makarantun gaba da sakandare ko kuma su koyi sana'a da zai taimaka musu."

Gidauniyar wadda ke garin Zaria a Jihar Kaduna ta ce burninta shi ne ganin ƴaƴa mata sun samu ilimi domin inganta rayuwarsu da ta danginsu da ta ma sauran al'umma baki ɗaya.

Baya ga tallafa wa ɗalibai, cibiyar na da wasu gogaggun malamai da ke taimakawa wajen ƙara fahimtar darussa na musamman. Misali, kimiyya da lissafi.

Malama Sadiya Nuhu na cikin malaman da ke koyar da ɗaliban, ta ce suna ganewa sosai.

"Wannan koyarwa na musamman na taimaka musu ƙwarai da gaske a rayuwarsu. Ko a makarantu ɗalibanmu ne a gaba. Ina kira ga gwamnatin Najeriya da a ƙara muhimmantar da ilimin ƴaƴa mata, ta yadda za a samu likitoci da ma'aikatan asibita mata domin su riƙa kula da mata."

Cikin dalilan da ke janyo matsalar rashin kammala makaranta a Arewacin Najeriya akwai talauci da auren wuri da taɓarɓarewar tsaro da kuma al'ada.

Shugabar gidauniyar ta Centre for Girls' Education ta ce sun duƙufa wajen wayar da kai game da wadannan matsaloli.

"Ni mace ce kuma na san lalurorin da mu mata ke fuskanta wanda ya shafi abubuwan da yawa. Shi ya sa nake ganin idan mace ta samu karatu ingantacce duk matsalolin da muke samu na ƙasa, za ku ga cewa an samu sauƙinsa. Kamar sake-saken aure da auren wuri da matsalolin haihuwa da mace-macen mata wurin haihuwa da sauransu," in ji ta.

Masana sun nuna cewa idan mace ta samu ilimi, yawan mutuwar mata masu haihuwa na iya raguwa; yara kan samu kulawa mai kyau sannan tattalin arzikin iyali yakan inganta, kamar yadda wani rahoton Bankin Duniya game da muhimmancin ilimin ƴaƴa mata ya nuna.

Yayin da wani rahoton UNICEF kuma ya nuna cewa idan mace ta yi akalla shekara 12 a makaranta, yiwuwar gamuwa da talauci a gidanta na raguwa sosai. Wata ƙididdiga dai ta nuna cewa Najeriya na fama da ƙarancin jami'an lafiya musamman a yankunan karkara. Mai yiwuwa ta hanyar bunƙasa ilimin ƴaƴa mata da karfafa musu gwiwa su karanci fannonin lafiya, kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka na iya warware wannan matsalar, wadda ake ganin a yanzu kamar ta gagari Kundila.