Manchester United ta yi wasan Premier 18 a waje ba a doke ta ba

Manchester United ta tashi wasa ba ci a gidan Arsenal a gasar Premier League da suka fafata, a ranar Asabar.

Sakamakon wasan ya sa United ta ci gaba da zama ta biyu a teburin Premier League da maki 11, ita kuwa Arsenal tana ta tara da maki 31.

Rabon da United ta yi rashin nasara a karawar waje a Premier League tun 19 ga Watan Janairu 2020 a fafatawar da Liverpool ta yi nasara da ci 2-0.

A wasan na ranar Asabar, United ta kasa doke Gunners karo na shida kenan da suke fafatawa a tasakaninsu.

Wannan ne karon farko da aka buga canjaras tsakanin Arsenal da Manchester United tun bayan Fabrairun 2014.

United ba ta ci was aba a karo biyar a Premier League da Arsenal karkashin Ole Gunnar Solskjaer - kuma shi ne ya ja ragamar United a wasa da Gunners bai yi nasara ba.

A fafatawar kuwa dan kwallon Brazil Willain ya buga wasa na 250 a Premier League, shi ne dan Brazil da keg aba wajen buga gasar.