Ba za mu miƙa wuya ba - Iran
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya rubuta a shafin X yana sukar hare-haren da ake kai wa ababen more rayuwa na fararen hula da kuma matsin lambar da ake yi wa rayuwar jama'a.
Ya ce: “Idan Amurkawa masu son yaƙi ne, su fuskanci dakarun sojinmu masu ƙarfin hali. Me ya sa suke kai hari kan ababen more rayuwar fararen hula, abinci da hanyoyin samun abin masarufin jama'a? Idan mutane ne, me ya sa suke hana jama'a ruwa, abinci da magunguna? Ba za a tilasta wa al'ummarmu miƙa wuya ta hanyar ƙarfi da matsin lamba ba. Iran ba za ta miƙa wuya ba.”
Kalaman Mista Pezeshkian sun zo ne yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar tashe-tashen hankula da kuma musayar hare-hare tsakanin Iran da Amurka.
A ranar da ta gabata, yayin taron ƙungiyar BRICS a New Delhi, ya ce matsin tattalin arzikin da ake yi wa Iran ya shiga “wani mataki mafi hatsari sosai” bayan yaƙin da aka yi tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila.
A wannan taron, shugaban na Iran ya yi kira ga ƙasashen BRICS da su samar da wata hanya da za ta hana dakile halastacciyar huldar kasuwanci tsakanin ƙasashe sakamakon matsin lambar siyasa da tattalin arziki.
Ya kuma jaddada muhimmancin faɗaɗa amfani da kuɗaɗen ƙasashen da ke cikin ƙungiyar wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci tsakaninsu.