Zai ɗauki Iran shekara 20 kafin ta sake gina kanta - Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump ya faɗa a wata hira da kafar yaɗa labaran Newsmax cewa cewa ''ƙasarsa ta yi nasara a yaƙin da take yi da Iran'' amma ya ce yana son nasarar ta kasance da ''gagarumin rinjaye''.
A cewar kafar yaɗa labaran CBS, ƙawar hulɗar BBC a Amurka, Mista Trump ya yi iƙirarin cewa An lalata rundunonin sojin sama da na ruwan Iran da kuma tsarin shugabancin ƙasar, iƙirarin da jami'an gwamnatinsa ke yi tun bayan fara yaƙin.
To amma jami'an Amurka da dama masu kusanci da hukumar leƙen asirin ƙasar sun shaida wa CBS cewa har yanzu Iran da na ƙarfin soji fiye da yadda White House ko ma'aikatar Pentagon ta sanar.
A cewar wasu jami'ai uku, kusan rabin makaman linzamin Iran da na'urorin harba su sunan nan cikin shirin a lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara a farkon watan Afrilu.
''Mun lalata musu komai, kuma ko da mun bar yaƙin yanzu, zai ɗauke su shekara 20 kafin su sake gina kansu, idan ma za su iya'', in ji Shugaba Trump.
Ya ƙara da cewa ''kuma hakan ma bai wadatar ba, za mu tabbatar ba su samu makamin nukiliya ba''.