Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa

Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da kasuwar 'yan wasanni ta duniya daga nan BBC Hausa daga 24 zuwa 30 ga watan Agusta

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Nottingham Forest na son sayen Delap daga Chelsea

    Kungiyar Nottingham Forest na aiki kan yarjejeniya domin daukar ɗan wasan gaba na Chelsea, Liam Delap.

    Chelsea ta bayyana cewa a shirye take ta sayar da ɗan wasan mai shekaru 23 kan kuɗin fam miliyan 50, kuma a halin yanzu yana atisaye ne daban da tawagar farko ta ƙungiyar.

    Har yanzu ba a tabbatar ko tattaunawar da ake yi ta shafi saye na dindindin ko kuma aron ɗan wasan ba, amma an san cewa Nottingham Forest da Chelsea suna da kyakkyawar alaƙar aiki tsakaninsu.

    Ba a fito da Delap ba cikin tawagar Chelsea da ta buga wasan Premier League da Fulham a ranar Litinin, sannan a makon da ya gabata ya rasa rigarsa mai lamba 9 inda aka bai wa takwaransa na gaba Joao Pedro.

    Yiwuwar barinsa Stamford Bridge na zuwa ne bayan fiye da shekara guda kacal da komawarsa Chelsea daga Ipswich Town kan kuɗin fam miliyan 30.

    Sai dai kakar wasan da ta gabata ba ta yi masa daɗi ba, domin ya kammala ta ne da ƙwallo ɗaya kacal a Premier, sakamakon raunukan kafaɗa da kuma tsokar baya cinyarsa da suka hana shi buga wasanni akai-akai.

  2. 'Yan wasan da suka zo Man Utd

    Ga sabbin 'yan wasan da Manchester United ta dauko a wannan bazarar:

    • Kit Margetson (Swansea City zuwa Manchester United) – Ba a bayyana kuɗin cinikin ba
    • Andrey Santos (Chelsea zuwa Manchester United) – £48m
    • Karl Darlow (Leeds United zuwa Manchester United) – Kyauta
    • Youri Tielemans (Aston Villa zuwa Manchester United) – £35m
    • Cristian Orozco (Fortaleza CEIF zuwa Manchester United) – Ba a bayyana kuɗin cinikin ba
    • Tynan Thompson (Tottenham Hotspur zuwa Manchester United) – Har zuwa £8m

    Idan aka haɗa kuɗaɗen da aka bayyana a hukumance, Manchester United ta kashe aƙalla fam miliyan 91 wajen sayen sabbin 'yan wasa a wannan bazarar, ba tare da ƙididdige kuɗin Kit Margetson da Cristian Orozco ba.

    Haka kuma, idan aka kammala cinikin Carlos Baleba daga Brighton kan kuɗin da zai kai £70m, jimillar kuɗin da United za ta kashe a kasuwar bana za ta haura fam miliyan 160.

    Zuwan Andrey Santos, Youri Tielemans, da kuma yiwuwar zuwan Carlos Baleba na nuna cewa Manchester United ta mayar da hankali sosai wajen ƙarfafa tsakiyar fili domin ƙara inganta ƙungiyar kafin sabuwar kakar wasa ta fara nisa.

  3. Ko Baleba zai iya jurewa matsin lambar United?

    Ga wasu daga cikin ra'ayoyin ku kan yunƙurin Manchester United na ɗauko ɗan wasan tsakiyar Brighton, Carlos Baleba, bayan sun yi ƙoƙarin sayensa tun bara:

    Dave: "Wannan dai kamar yanke shawara ne a mintinan ƙarshe! Na san an dade ana magana a kai kusan shekara guda, amma a cikin wannan shekarar bai yi wani abin a zo a gani ba. A ganina zaɓi ne mara kyau. Myles Lewis-Skelly ya fi Baleba a kusan dukkan fannoni, ko na ƙwallo ko na kuɗi. Kuma mafi muhimmanci, yana cikin ƙoshin lafiya. Baleba bai kai Andrey Santos ba, amma kuma ya fi shi tsada."

    Howard: "Ina farin ciki da wannan. Muna buƙatar ƙarfin tsakiya kuma zai iya samar mana da hakan. Haka kuma yana son zuwa Manchester United, wanda abu ne mai kyau. Bai kamata mu mayar da hankali sosai kan rashin kyakkyawan kakar wasansa ta bara ba, domin hankalinsa ya rabu ne sakamakon batun canjin kulob. Ina ganin zai yi mana amfani sosai. Mu yi fatan yarjejeniyar ta tabbata, domin muna buƙatar ƙwararren ɗan wasan tsaron tsakiya irinsa."

    Thomas: "Akwai 'yan wasa masu hazaka sosai da suka gaza a Manchester United, sannan akwai wasu da ba a yi musu wani tsammani ba amma suka yi fice. Abin da muke buƙata shi ne 'yan wasa masu ƙwarin hali da tunanin zakara. Idan yana da wannan, to yana da cikakken goyon bayana."

    Mark: "Babban abin da ke damuna game da Baleba shi ne ko zai iya jure matsin lambar da ke Manchester United. Wasansa ya ragu sosai a kakar da ta gabata. Idan hakan ya faru ne saboda canjin da bai tabbata ba, to abin zai sa a yi tambaya kan ƙarfin halinsa. Idan kuma ba haka ba ne, to dole a tambayi dalilin da ya sa hakan ya faru da kuma ko zai iya dawo wa irin wannan bajintar."

    Coops: "Na yi matuƙar mamakin wannan labari. Wani matsakaicin ɗan wasan tsakiya ne kuma, alhali muna matuƙar buƙatar sake gina tsaronmu. Maxence Lacroix, Ezri Konsa da Jan Paul van Hecke duk sun koma ƙungiyoyin hamayyarmu. Wata kasuwar saye da sayarwa mara kyau ce, duk da alkawuran da aka yi mana, kamar yadda aka saba!"

  4. Wane ne Bouaddi?

    Ayyoub Bouaddi ya burge mutane da dama a gasar Kofin Duniya ta bana, inda ya fara wasa a wasanni biyar cikin shida da Morocco ta buga har ta kai zagayen kwata fainal. Tun da farko, ya fara jan hankali sosai a duniya bayan rawar da ya taka wajen taimakawa Lille ta doke Real Madrid a gasar Champions League a shekarar 2024.

    Bouaddi na taka rawa a matsayin ɗan wasan tsakiya mai jan ragamar wasa daga baya, wato wanda ke tsara kai hare-hare da rarraba ƙwallaye daga zurfin fili. Salon wasansa zai dace sosai da Elliot Anderson, wanda kuma ke iya taka rawa a matsayin ɗan wasan tsakiya mai kai-komo, baya ga matsayin lamba shida da yake bugawa Ingila.

    Bouaddi ya fara buga wa babbar ƙungiyar Lille wasa ne a watan Oktoban 2023, kwanaki uku kacal bayan cika shekaru 16 da haihuwa. Tun daga lokacin ya buga wasanni 88 ga Lille, sannan ya taimaka wa ƙungiyar ta kammala kakar wasan Ligue 1 da ta wuce a matsayi na uku.

    Haka kuma, ya karya tarihin da fitaccen tsohon ɗan wasan Lille, Eden Hazard, ya kafa, bayan ya kai wasanni 50 a gasar lig ta Faransa yana da shekaru 18 kacal.

  5. Man Utd ta amince ta biya £70m kan Baleba na Brighton

    Manchester United ta cimma yarjejeniya da Brighton kan cinikin ɗan wasan tsakiya Carlos Baleba a kuɗin da zai iya kaiwa fam miliyan 70.

    Kungiyoyin biyu sun samu nasarar cimma matsaya a tattaunawarsu a daren Juma'a, lamarin da ya bai wa ɗan wasan mai shekaru 22 damar zuwa domin gwajin lafiya tare da Manchester United a wannan karshen mako.

    United ta mayar da hankalinta kan ɗan wasan na ƙasar Kamaru ne a wannan makon bayan ta yanke shawarar ƙara ƙarfafa tsakiyarta, biyo bayan zuwan Andrey Santos daga Chelsea da kuma Youri Tielemans daga Aston Villa.

    Manchester United za ta biya fam miliyan 65 da farko, sannan akwai yiwuwar ƙarin fam miliyan 5 idan wasu sharuɗɗa sun cika. Haka kuma, Brighton ta saka sharadin samun wani kaso daga kuɗin da za a sayar da Baleba a nan gaba.

    Baleba, wanda ya koma Brighton daga Lille a shekarar 2023, yana jinya a halin yanzu sakamakon raunin idon sawu da ya samu yayin wasannin shirye-shiryen fara kakar wasa da ƙungiyar ta yi a ƙasar Austria.

    Idan aka kammala cinikin, jimillar kuɗin da Manchester United ta kashe wajen sayen 'yan wasa a wannan bazarar za ta kai fam miliyan 153.

    Sai dai kuma, wannan ciniki na nufin United ta samu rangwame mai yawa idan aka kwatanta da kuɗin da Brighton ke nema yayin da ake gab da rufe kasuwar musayar 'yan wasa ta shekarar 2025.

  6. Waɗanda suka bar Man City

    Ga 'yan wasan da Manchester City ta sayar ko kuma suka bar ƙungiyar zuwa yanzu a wannan bazarar:

    • Tijjani Reijnders (Manchester City zuwa Al-Qadsiah) – £52m
    • Rodri (Manchester City zuwa Barcelona) – kusan £65m
    • James Trafford (Manchester City zuwa Leeds United) – ba a bayyana kuɗin cinikin ba
    • John Stones (Manchester City zuwa Inter Milan) – kyauta
    • Manuel Akanji (Manchester City zuwa Inter Milan) – £13m
    • Nathan Aké (Manchester City zuwa Fenerbahce) – £7m
    • Bernardo Silva (Manchester City zuwa Real Madrid) – kyauta
    • Savinho (Manchester City zuwa Tottenham Hotspur) – £75m

    Wadannan sauye-sauye na nuna babban canji a tawagar Manchester City, inda fitattun 'yan wasa irin su Rodri, Bernardo Silva, John Stones da Savinho suka bar kungiyar.

    Sai dai mafi daukar hankali shi ne cinikin Savinho zuwa Tottenham kan fam miliyan 75, da kuma komawar Rodri Barcelona a kan kudin da ake hasashen ya kai kusan fam miliyan 65.

    Idan aka hada kudaden da aka bayyana a hukumance, Manchester City ta samu akalla fam miliyan 212 daga sayar da 'yan wasa a wannan bazarar, ba tare da lissafa kudin James Trafford da sauran yiwuwar kari da ke cikin wasu yarjejeniyoyi ba.

  7. Man City ta amince ta biya £81.4 kan Bouaddi

    Manchester City sun cimma yarjejeniya ta farko mai darajar Yuro miliyan 100 (£85.6m) domin daukar matashin ɗan wasan tsakiya na Lille, Ayyoub Bouaddi mai shekaru 18.

    BBC Sport ta ruwaito a farkon wannan makon cewa kungiyoyin biyu na tattaunawa a mataki na karshe kan cinikin ɗan wasan ƙasar Morocco zuwa City.

    Yanzu an cimma matsaya kan yarjejeniyar da za ta kai Bouaddi zuwa kungiyar da Enzo Maresca ke jagoranta, inda Lille ta amince da karɓar £81.4m a matsayin kuɗin farko, tare da ƙarin £4.2m na kari idan wasu sharuɗɗa sun cika.

    Bayan da City ta sayar da 'yan wasan tsakiya Rodri zuwa Barcelona kan £65m da kuma Tijjani Reijnders zuwa kungiyar Al-Qadsiah ta Saudiyya kan £52m, kungiyar ta mayar da hankali wajen ƙarfafa tsakiyar fili.

    Har yanzu City na sha'awar ɗan wasan Chelsea Enzo Fernandez, amma har yanzu ba a san ko za a iya cimma yarjejeniya ba.

    Tuni kuma kungiyar ta kara ɗan wasan Ingila Elliot Anderson daga Nottingham Forest kan £116m.

  8. Sabbin 'yan wasan City

    Ga sababbin 'yan wasan da Manchester City ta dauko a kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara:

    • Elliot Anderson: Daga Nottingham Forest zuwa Manchester City kan kuɗi kusan fam miliyan 116.
    • Mathys Detourbet: Daga Troyes zuwa Manchester City kan fam miliyan 21.4.
    • Jeremy Monga: Daga Leicester City zuwa Manchester City kan fam miliyan 10.
    • Geronimo Rulli: Daga Marseille zuwa Manchester City kan kuɗin da ba a bayyana ba.
    • Pierce Charles: Daga Sheffield Wednesday zuwa Manchester City kan kuɗin da ba a bayyana ba.
  9. Ramsay ya koma St Mirren daga Liverpool

    Dan wasan baya na gefen dama na Liverpool, Calvin Ramsay, ya koma ƙungiyar St Mirren ta Scotland a matsayin aro na tsawon kakar wasa guda.

    Dan wasan mai shekaru 23, wanda ya taba buga wa tawagar ƙasar Scotland wasa sau ɗaya, ya koma Liverpool ne daga Aberdeen a shekarar 2022 da kwantiragin shekaru biyar.

    Ramsay ya buga wasanni hudu kacal a matakin manyan 'yan wasa tare da Liverpool, amma har yanzu bai taba taka leda a gasar Premier League ba.

    Ficewarsa daga Anfield ya ba Liverpool damar samun gurbi domin daukar wani dan wasa da ba ya cikin rukunin 'homegrown' (wanda aka horar a gida).

    Dokokin gasar sun tanadi cewa kungiyoyi za su iya yi wa aƙalla 'yan wasa 17 rajista waɗanda ba sa cikin rukunin 'homegrown'.

    Ana ɗaukar dan wasa a matsayin 'homegrown' idan, ba tare da la’akari da ƙasarsa ko shekarunsa ba, ya kasance yana da alaƙa da wata ƙungiya a Ingila ko Wales na tsawon cikakkun kakanni uku ko watanni 36 kafin ya cika shekara 21 da haihuwa.

    A farkon wannan watan, zuwan Ronald Araujo Liverpool ya sa adadin 'yan wasan da ba 'homegrown' ba ya kai 17, wanda shi ne iyakar adadin da aka amince da shi.

  10. Aston Villa ta fara tattaunawa da Crystal Palace kan Mateta

    Aston Villa ta fara tuntuɓar Crystal Palace domin yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaba Jean-Philippe Mateta.

    Villa na nazarin zaɓuɓɓukanta wajen ƙarfafa harin ƙungiyar, musamman yayin da Al Hilal ta Saudiyya ke ƙoƙarin ɗaukar fitaccen ɗan gabanta Ollie Watkins.

    Haka kuma, Villa ta tuntubi AC Milan kan yiwuwar sayen ɗan wasan gefe Rafael Leao, kamar yadda Sky Sport Italia ta fara ruwaito wa.

    Mateta, wanda saura shekara guda kacal a kwantiraginsa da Crystal Palace, ya daɗe yana cikin jerin 'yan wasan da Villa ke sha'awarsu tun daga kasuwar musayar 'yan wasa ta lokacin hunturun da ya gabata.

    Baya ga Mateta, Aston Villa na kuma bibiyar ɗan wasan gaban Chelsea, Nicolas Jackson. Ana sa ran Jackson zai bar Chelsea kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa, sai dai kuma yana jan hankalin Napoli da wasu ƙungiyoyi da dama.

    Wannan na nuna cewa Aston Villa na shirye-shiryen neman sabon ɗan gaba, musamman idan Ollie Watkins ya amince da tayin komawa Al Hilal.

  11. Tottenhma ta shiga kasuwar saye da sayerwa da karfinta

    Ga jerin 'yan wasan da Tottenham ta dauko zuwa yanzu a wannan kasuwar musayar 'yan wasa:

    • Savinho (Manchester City zuwa Tottenham) – £75m
    • Sandro Tonali (Newcastle United zuwa Tottenham) – £100m
    • Mateus Fernandes (West Ham United zuwa Tottenham) – £85m
    • Jan Paul van Hecke (Brighton zuwa Tottenham) – £52m
    • Marcos Senesi (Bournemouth zuwa Tottenham) – Kyauta
    • Andrew Robertson (Liverpool zuwa Tottenham) – Kyauta
    • Martin Dubravka (Burnley zuwa Tottenham) – Kyauta

    Wannan na nuna cewa Tottenham ta kashe kuɗi masu yawa a wannan bazarar, inda ta zuba aƙalla fam miliyan 312 kan manyan saye uku da huɗu, ba tare da ƙididdige kuɗaɗen kari da sauran tanade-tanaden da ke cikin kwantiragi ba.

    Zuwa yanzu, sayen Sandro Tonali kan £100m shi ne mafi tsada, sai Mateus Fernandes (£85m) da kuma Savinho (£75m). Haka kuma, ƙungiyar ta ƙara ƙarfafa tsaro da gogewa ta hanyar ɗaukar Marcos Senesi, Andrew Robertson da Martin Dubravka ba tare da biyan kuɗin saye ba.

    Idan har Tottenham ta kammala sayen Omar Marmoush daga Manchester City, kuɗin da ta kashe a wannan bazarar zai ƙara tashi sosai, lamarin da ke nuna aniyarta ta gina ƙungiya mai ƙarfin lashe manyan kofuna a kakar wasa mai zuwa.

  12. Ina batun Marmoush da Tottenham?

    Savinho ya bayyana Roberto De Zerbi a matsayin ɗaya daga cikin "fitattun masu horarwa a duniya" bayan ɗan wasan gaba ya kammala komawarsa daga Manchester City zuwa Tottenham Hotspur.

    Da yake magana da shafin yanar gizon Tottenham bayan sanya hannu a kungiyar da ta lashe Europa League ta 2025, tauraron na Brazil ya ce:

    "An ɗauki lokaci kafin komai ya kammala amma ina matuƙar farin cikin kasancewa a nan.

    Wannan babbar dama ce a wata ƙungiya mai girma tare da ɗaya daga cikin mafi kyawun masu horarwa a duniya.

    Da zarar na yi magana da kocin, nan take na san cewa dole ne in zo. Ya gaya mini cewa yana son taimaka mini wajen kaiwa mataki mafi girma, kuma na yi imanin za mu iya cimma hakan tare, a matsayin ƙungiya."

  13. Ethiopia na neman ɗaukar nauyin AFCON 2028

    Habasha ta miƙa buƙatarta a hukumance domin karɓar baƙuncin gasar Kofin Nahiyar Afirka AFCON ta shekarar 2028, wanda zai zama karo na farko da ƙasar za ta shirya gasar cikin fiye da rabin ƙarni.

    Hukumar Kwallon Kafar Habasha ta tabbatar da gabatar da takarar a wani saƙo da ta wallafa a shafin X a daren Litinin.

    A karo na ƙarshe da Habasha ta karɓi bakuncin gasar shi ne a shekarar 1976.

    Habasha ita ce ƙasa ta biyu mafi yawan jama'a a Afirka, inda ake hasashen tana da mutane kusan miliyan 130.

    Bugu da ƙari, babban birninta Addis Ababa ne hedkwatar Tarayyar Afirka (AU). Haka kuma, Addis Ababa ne babban birnin ƙasa mafi tsayi da ke kan tudu a Afirka, tana da tsayin mita 2,300 daga matakin teku.

    Sai dai takarar na fuskantar ƙalubale da dama, ciki har da tashe-tashen hankula da har yanzu suke gudana a jihohin Amhara da Oromia, waɗanda su ne jihohi mafiya yawan jama'a a ƙasar.

    Har ila yau, akwai fargabar sake barkewar yakin basasa tsakanin gwamnatin tarayya da yankin Tigray da ke arewacin ƙasar.

    Tawagar ƙwallon ƙafar Habasha tana matsayi na 143 cikin ƙasashe 211 a jadawalin FIFA.

    Haka kuma, karo na ƙarshe da ta buga gasar AFCON shi ne a shekarar 2022, inda aka fitar da ita tun daga matakin rukuni.

  14. Man City da Tottenham na rige-rigen ɗaukar Cody Gakpo

    Manchester City ta shiga cikin jerin kungiyoyin da ke neman daukar ɗan wasan gaba na Liverpool da ƙasar Netherlands, Cody Gakpo mai shekaru 27, yayin da Tottenham Hotspur ma ke ci gaba da kokarin kulla yarjejeniya da shi.

  15. Manchester City ta amince da sayen Allan Elias daga Palmeiras

    Manchester City ta cimma yarjejeniya da Palmeiras kan ɗaukar ɗan wasan gefe na Brazil Allan Elias a wani ciniki da zai iya kaiwa har fam miliyan 34.2.

    An shirya Allan Elias mai shekaru 22 ya maye gurbin ɗan uwansa ɗan ƙasar Brazil Savinho, wanda ake sa ran zai koma Tottenham Hotspur.

    City za ta biya kuɗin farko na fam miliyan 32, sannan a ƙara wasu fam miliyan 2.2 a matsayin ƙarin kuɗaɗen da suka danganci wasu sharudda. Ana kuma sa ran ɗan wasan zai yi gwajin lafiya cikin kwanaki masu zuwa.

    A gefe guda kuma, City na ci gaba da tattaunawa kan sayar da ɗan wasan gaba na Masar Omar Marmoush zuwa Tottenham.

    Majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun ce akwai "kyakkyawar dama" yarjejeniyar za ta kammala kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar 1 ga Satumba.

    Har yanzu dai tattaunawa na ci gaba tsakanin kulob ɗin biyu, duk da cewa akwai wasu bayanai da sharudda da ba a kammala daidaitawa a kansu ba.

    Haka kuma, ɗan wasan tsakiya Nico Gonzalez na iya barin filin wasa na Etihad kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa, inda Newcastle United ke nuna sha'awa wajen ɗaukar ɗan wasan na Spain.

  16. Me ake ciki ne kan cinikin Watkins

    Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya, wadda ta bayar da tayin kusan fam miliyan 40, har yanzu ba ta kai farashin da Aston Villa ke nema domin sayar da Ollie Watkins ba.

    Yayin da ranar rufe kasuwar musayar 'yan wasa ta kusa a ranar Talata mai zuwa, Villa na da niyyar tsayawa tsayin daka kan dan wasan da ya fi kowa zura mata ƙwallaye a tarihin Premier League.

    Har yanzu ana ganin akwai tazara mai yawa kafin a cimma yarjejeniya, duk da cewa kocin Aston Villa, Unai Emery, ya bayyana a makon da ya gabata cewa mai yiwuwa Watkins ya bar kungiyar.

    Al-Hilal, wadda ta dauki Crysencio Summerville daga West Ham a watan Yuli, na iya bukatar ta sallami ko kuma ta fitar da daya daga cikin 'yan wasanta na ketare domin samun gurbin rajistar Watkins. Ko da yake ta tura Darwin Nunez aro zuwa Diriyah a makon da ya gabata, har yanzu akwai wasu batutuwa da dole a warware kafin yarjejeniyar ta kammala.

    Watkins yana atisaye shi kadai bayan ya dawo daga karin hutun da ya samu sakamakon buga Gasar Kofin Duniya, kuma rahotanni sun nuna cewa ya riga ya bayyana wa shugabannin Aston Villa ra'ayinsa na son barin ƙungiyar.

    Duk da cewa Watkins ko wakilansa ba su yi wata magana a bainar jama'a ba, an fahimci cewa dan wasan a shirye yake ya saurari tayin komawa Saudiyya.

  17. Akwai buƙatar a riƙa jin tsoron Manchester United - Rooney

    Babban kocin Manchester United, Michael Carrick, ya yi wasu muhimman bayanai guda biyu yayin taron manema labarai bayan rashin nasarar da ƙungiyarsa ta yi da ci 2-0 a hannun sabuwar ƙungiyar da ta hawo Gasar Premier, Hull City, a wasan farko na kakar bana.

    Ya ce "Mun yi abubuwa masu kyau da yawa a yau. Na san mutane za su manta da hakan saboda sakamakon wasan, amma a gare mu ba za mu manta da su ba."

    Bayan wasu tambayoyi kaɗan, Carrick ya sake cewa "Don kawai mun yi rashin nasara a yau ba yana nufin sai an warware ko a sake nazarin komai da ya shafi ƙungiyar ba."

    Sai dai galibin masu sharhi da masu bibiyar wasan suna ganin Manchester United ta rasa zafin fafatawa da kuzarin matsawa abokan hamayya.

    Ko da ma tsohon ɗan wasan United kuma babban abokin Carrick, Wayne Rooney, ya bayyana hakan a shirin Match of the Day.

    Rooney ya ce: "Idan Manchester United na son ɗorawa kan abin da ta cimma a kakar da ta gabata, dole ne ta zama ƙungiyar da sauran ƙungiyoyi ke jin tsoronta."

    Ya ƙara da cewa: "Ya kamata a samu ƙarin kuzari wajen matsa wa abokan hamayya lamba. Sun yi wasa cikin sanyin jiki da yawa."

    Sai dai Carrick bai amince da wannan ra'ayi ba. Ya ce "Don kawai an doke ku ba yana nufin kun yi wasa cikin sanyin jiki ba."

    "Wasa ɗaya ne kawai. Irin waɗannan sakamako na iya faruwa a ƙwallon ƙafa. Dukanmu mun san hakan. Ba abin farin ciki ba ne idan ya faru, amma yana faruwa."

    Wannan martani dai ya dace da halin Carrick, wanda aka fi sani da natsuwa da kwanciyar hankali. Duk da haka, ya amince cewa yadda ya fito a bainar jama'a bayan wasan ya bambanta da yadda yake ji a zuciyarsa bayan shan kaye.

    Carrick ya shafe kusan shekaru 20 yana da alaƙa da Manchester United, a matsayin ɗan wasa, koci, babban koci da kuma magoyi baya.

  18. Ana daf da cimma matsaya tsakanin Arsenal da Al Hilal kan Martinelli

    Arsenal na ci gaba da tattaunawa da kulob din Al-Hilal na Saudiyya kan sayar da Gabriel Martinelli kan kuɗi fam miliyan 50.

    Dan wasan na Brazil mai shekaru 25 na da 'yancin barin Arsenal a wannan bazara, bayan da kociyan kungiyar Mikel Arteta ya bayyana cewa ɗan wasan gaban ba ya cikin tsare-tsarensa na gaba.

    Tattaunawar tsakanin kungiyoyin biyu ta ƙara ƙarfi a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kuma yanzu yarjejeniya ta kusa kammaluwa.

    Idan aka cimma matsaya ta ƙarshe, Martinelli ne zai yanke hukunci kan ko yana son komawa taka leda a gasar Saudi Pro League, bayan da a baya ya ƙi tayin komawa Galatasaray ta Turkiyya.

    Rahotanni sun ce albashin da Al-Hilal ke tayin baiwa Martinelli ya fi fam 180,000 a mako da yake karɓa a Arsenal.

    Martinelli ya koma Arsenal daga kulob din Ituano na Brazil a shekarar 2019, kuma saura watanni 12 kacal a kwantiraginsa na Emirates.

    A kakar wasan da ta gabata, ya buga wasanni 53 a dukkan gasa, inda ya ci ƙwallaye 11 yayin da Arsenal ta lashe kambun Premier.

    Sai dai ba a saka shi cikin tawagar Arsenal ba a wasan farko na gasar da Coventry ranar Juma'a, wanda Gunners ta yi nasara da ci 3-0.

    Tsohon dan wasan gaba na Arsenal, Ian Wright, ya soki matakin da Arteta ya dauka na cire Martinelli daga tawagar, tare da yadda kulob din ke mu'amala da shi.

  19. Tottenham ta kammala sayen Savinho daga Man City

    Tottenham ta kammala ɗaukar ɗan wasan gefe na Brazil, Savinho, daga Manchester City kan kuɗi fam miliyan 75.

    Matashin mai shekara 22 ya sanya hannu kan kwantiragi na dogon lokaci da Spurs, yayin da ƙungiyar Roberto de Zerbi za ta iya biyan ƙarin fam miliyan 10 (£10m) idan wasu sharuɗɗan cikin sun cika.

    Komawar Savinho zuwa arewacin Landan ta daɗe tana kan hanyar kammalu wa, domin Spurs ta yi ƙoƙarin sayensa tun bazarar bara amma ba ta yi nasara ba.

    A lokacin, Savinho ya zaɓi ci gaba da zama a filin wasa na Etihad, amma bai samu buga wasa sosai ba a ƙarƙashin Pep Guardiola a kakar da ta gabata, inda ya fara wasa sau bakwai kacal a gasar Premier League.

    Da yake magana bayan kammala canjin, Savinho ya ce: "An ɗauki lokaci mai tsawo kafin a kammala komai, amma ina farin cikin kasancewa a nan."

    "Wannan babbar dama ce a wani babban kulob da ke da ɗaya daga cikin mafi kyawun masu horarwa a duniya."

    "Da zarar na yi magana da kocin, na san dole ne in zo. Ya gaya min cewa yana son taimaka mini in kai mataki mafi girma, kuma na yi imanin za mu iya cimma hakan tare a matsayin ƙungiya."

    Savinho ya koma Manchester City daga kulob ɗin Troyes na Faransa a shekara ta 2024 kan kuɗi fam miliyan 30.8.

    A tsawon zamansa da City, ya buga wasanni 84 a dukkan gasa, inda ya ci ƙwallaye bakwai tare da bayar da taimakon ƙwallaye 16.

  20. Chelsea ta doke Fulham 2-3 har gida

    Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Chelsea ta samu nasarar doke abokiyar burminta Fulham har gida da ci 2-3 a wasan hammayar Landan.

    Tun a daƙiƙa ta 31 da sa wasam kan a kai minti ɗaya João Pedro dan wasan gaban Chelsea ya zura kwallo ta farko.

    31 - Da aka auna a daƙiƙa 31 kacal, João Pedro ya zura ƙwallo mafi sauri da aka taɓa ci a ranar farko ta kakar Premier League.

    Wannan na nufin babu wani ɗan wasa da ya taɓa zura ƙwallo cikin sauri haka a wasan farko na kakar Premier League tun bayan kafa gasar.

    Ƙwallon da João Pedro ya ci cikin daƙiƙa 31 ya kafa sabon tarihi a matsayin ƙwallo mafi sauri da aka ci a ranar buɗe kakar Premier League.

    A mintina na 23 J. King ya dawo da Fulham cikin wasan, wani abu da ya bata karsashi da kwarin gwiwa.

    Sai dai gabanin a juya hutun rabin lokaci ɗan wasan da Chelsea ta saya daga Aston Villa mafi tsada Morgan Rogers ya zira kwallo ta biyu a wasan, ta farko da ya ci a sabuwar ƙungiyarsa a wasan farko.

    Wannan zai rage matsin lamba kan ɗan wasan da aka saya fam miliyan 117 mafi tsada a wannan kakar baki ɗaya.

    Bayan da matsi ya ƙaru ga Chelsea sai a mintina na 49 Cole Palmer ya ƙara kwallo ta uku wadda da ita ce kuma Chelsea ta tsira a wasan.

    Cin kwallon bai kashewa Fulham gwiwa ba, ta ci gaba da matsawa na ganin ta farke kwallayenta, inda dan wasan da ta ɗauko daga Real Madrid Gonzalo García ya ci tasa shi ma a wasansa na farko a mintina na 54.

    A haka aka ƙare wasan Chelsea na gaba 2-3.

    Sai abin birgewar shi ne yadda matasan 'yan kwallon Fulham suka buga wasansu ba tare da jin fargaba ko tsoro ba, kuma ba su tare a baya ba domin nuna kariya.