Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawan ƙasar ta amince da ciyo bashin fiye da dala miliyan 516 daga babban bankin Jamus (Deutsche bank) , domin aikin wani ɓangare na babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Godswil Akpabio, Shugaban ƙasar ya ce an tsara aikin gina kilomita 100 na titin ne domin ya haɗa Arewa maso yammacin ƙasar da kudu maso yammaci, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.
A cewar sa, babbar hanyar za ta taso ne daga Illela a jihar Sokoto, ta bi ta jihohin Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun, ta kare a Badagry da ke Jihar Legas.
A cewar wasiƙar, za a yi amfani da bashin wajen gina sashe na 1, rukuni na 1 da na biyu, mai nisan kilomita 120, cikin bakidaya kilomita 1,000.
Za a biya bashin ne cikin shekaru 9, amma za a iya ƙara lamunin aƙalla shekaru uku.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni Majalisar ministocinsa ta amince da tsarin karɓo bashin, inda ya buƙaci majalisar Dattawan ta sanya bashin cikin tsarin karbo bashi na ƙasar.
Wasiƙar shugaban ƙasar ta bayyana cewa babbar hanyar za ta taimaka wajen bunƙasa kasuwanci, da samar da isashen abinci, da haɗin kan ƙasa.
Sanata Akpabio ya miƙa buƙatar ga kwamitin kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje, kuma ana sa ran zai bayar da rahoto nan da mako guda.