Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Talata 05/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Hare-haren Isra'ila a Lebanon sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 110 cikin kwanaki 5

    Ma'aikatar lafiya ta ƙasar Lebanon ta ce hare-haren da Isra'ila ta kai sun yi sanadiyar mutuwar mutane dari da goma tun daga ranar Alhamis, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma sama da makonni biyu da suka gabata.

    Ranar litinin na daya daga cikin ranaku mafi muni a ‘yan kwanakin nan, inda sojojin Isra’ila suka kashe mutane goma sha bakwai da suka hada da kananan yara biyu.

    Wakilin BBC ya ce A kudancin Lebanon, wannan tsagaita wuta a suna ne kawai, Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama a kowace rana.

    Isra'ila dai ta dage kan cewa kungiyar Hezbullah ta ke kai wa hari.

    Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya ruwaito cewa, sojojin kasar Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan wasu wurare sama da ashirin a kudancin kasar ta Lebanon a jiya litinin

  2. An sami fashewar wani abu a wata masana'anta da ke tsakiyar China

    Aƙalla mutane 26 ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a wata masana'anta da ke lardin Hunan tsakiyar kasar China.

    Jami’an ceto sun kwashe duk mutanen da ke da nisan kilomita uku daga wurin, bayan fashewar, wanda kuma ya jikkata sama da mutum sittin.

    Shugaba Xi Jinping ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin da kuma yin ƙokari matuƙa wajen gano mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba.

    Wakiliyar BBC ta ce sama da ma'aikatan bayar da agajin gaggawa guda ɗari hudu da tamanin ne suke gudanar da aikin gano waɗanda suka maƙale a cikin ginin.

  3. Iran ta gargaɗi Amurka kan sake komawa yaƙi

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce abubuwan da suka faru a Mashigar Hormuz na nuni da cewa matakan soji ba za su iya warware abin da ya kira "rikicin siyasa" ba, yayin da ake fargabar sake ɓarkewar yaƙi tsakanin kasarsa da Amurka.

    Araghchi ya kuma gargaɗi Amurka kan ta yi taka tsan-tsan, kuma kar ta bari masu mummunan fata su sake jefa ta cikin yaƙi.

    Shugaba Trump ya yi wa yunƙurin Amurka na taimaka wa jiragen ruwan kasuwanci wucewa ta Mashigar Hormuz laƙabi da "Project Freedom", amma Mista Araghchi ya ce a zahiri ba haka lamarin ya ke ba.

    Iran da Amurka sun yi musayar wuta a mashigar ruwan a jiya Litinin, inda daga baya Trump ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta shafe Iran daga doron ƙasa idan har ta kai hari kan jiragen ruwan ƙasarta.

  4. Assalamu Alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar Talata.

    A yau ma, za mu kawo muku labaran irin wainar da ake toyawa a sassan duniya, kama daga yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran, da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.